Nasir S Gwangwazo" />

DAGA TEBIRIN EDITA: Jacob Zuma: Darasi Daga Afrika Ta Kudu

Daga Nasir S. Gwangwazo

Da a ce jam’iyyun Nijeriya za su kasance masu karfi irin yadda na wasu kasashe su ke, hakika da wasu matsalolin siyasa da cigaba da su ka addabi Nijeriya ba su afku ba.

A ranar Larabar 14 ga Fabrairu, 2018 ne jam’iyyar ANC mai mulkin kasar Afrika ta Kudu ta tilasta wa shugaban kasar, Jacob Zuma, yin ritayar dole. Zuma ya sanar da ritayar tasa ne a wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar, inda a cewarsa ya sauka ne saboda rarrabuwar da kai da a ka samu a cikin jam’iyyar tasu.

To, amma a zahiri fa an san cewa, tilas ce ta sanya ya sauka, saboda tuni ANC ta bai wa ’yan jam’iyyarta umarnin tsige shi a an kai washegari Alhamis, inda ta nemi ’yan majalisar dokoki da ta ke da rinjaye a ciki da su gaggata aiwatar da umarninta na tsige shi, don kare mutuncin jam’iyyar daga idanun masu kada kuri’a, saboda zargin aikata cin hanci da rashawa da a ke yiwa shugaban kasar.

A fili hakan ya nuna cewa, jam’iyya a kasar ta Afrika ta Kudu ta na zaman kanta ne. Don haka shugaban kasa bai isa ya juya ta yadda ya ga dama ba, kamar yadda mu ke gani a gida Nijeriya. Idan za a iya tunawa, tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela, duk da irin farin jinin da ya ke da shi, saboda gwagwarmayar da yi wajen kwato ’yancin bakar fatar kasar, amma hakan bai sa ya zama wuka da nama ga jam’iyyar ba, domin a lokacin da matarsa, Winny Mandela, ta nemi ta keta haddi da iyakokin jam’iyya, sai da ANC ta ja kunne Mandela kuma ta ba shi zabi tsakanin ita jam’iyyar da matar tasa. Kuma dole Mandela ya fifita ANC a kan matar, don ya tsira daga juya ma sa baya.

Haka nan, a lokacin da a ka zargi tsohon shugaban kasar, Thabo Mbeki, da keta iyakokin kasa da na jam’iyyar, shi ma ANC ta juya baya a gare shi, inda ta ki zaben shi a matsayin shugaban jam’iyyar kuma ta mara wa Zuma baya ya kayar da dan takararsa bayan shi Mbeki ya kammala zangon mulkinsa, wanda hakan ke tabbatar da cewa, shugaban kasa ba shi da ta cewa a ANC matukar ya saba da akidunta komai isarsa kuwa a kasar.

Hakan ne ya faru a kan Zuma kwanan, inda kiri-kiri matsin lamba daga ANC ya tilasta ma sa yin ritayar dole duk da cewa wa’adin mulkinsa bai kare ba. Da ma dai tun a ’yan watannin baya su ka sauke shi daga mukamin shugabancin jam’iyyar su ka zabi mataimakinsa, Cyril Ramaphosa, wanda a yanzu ya gaje shi a matsayin shugaban kasa.

Wannan babbar ishara ce ga jam’iyyun siyasa a Nijeriya, wadanda a kullum zababbun shugabanninsu ba su jin kunyar ayyana shugaban kasa a matsayin jagoran jam’iyya cikin sigar da ke nuna cewa, ya ma fi su iko a ciki jam’iyyun.

Babban abin takaici shi ne, yadda za ka idan muhimman al’amuran kasa su ka su ka taso, irin wadannan jam’iyyu na Nijeriya su na jira ne ma su ga inda shugaban kasa ya dosa kafin su dauki alkibla, maimakon ya zamana ita jam’iyyar ce ta ke da manufar da duk wani danta zai dauka.

A lokacin da tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya nemi yin tazarce karo na uku, jam’iyyarsa ta PDP ta mara ma sa baya, duk da cewa, hakan abu ne na zubar da mutunci a idanun mafi yawan ’yan Nijeriya. Maimakon ta taka ma sa burki, duk da cewa ita ta ke da rinjaye a majalisa, a’a, sai ya zamana ta na cikin ’yan gaba-gaban tallen hajar tasa, duk da cewa shi ne ya fi kamata ya yi tallen tata hajar.

Baya ga haka kuma, a lokacin da tsohon shugaban Nijeriya, Umaru Musa Yar’Adua, ya kwanta jiya, maimakon PDP ta tilasta bin dokar kasar ta hanyar mara wa mataimakinsa baya, don ya amshi ikon tafiyar da kasar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, a’a, sai jam’iyyar ta cigaba da biye wa na jikin Yar’Adua din, duk da cewa a lokacin hakan zubar da mutuncin jam’iyya ne.

Bugu da kari, a lokacin da tsaron kasa ya durkushe a hannun gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, maimakon jam’iyyarsa ta PDP ta juya ma sa baya a lokacin babban zaben kasa na 2015, ta tsayar da wani daban, don ta sami damar sake lashe zabe, a’a, sai ta ki yin hakan ta cigaba da biye ma sa har su ka fadi tare a zaben na 2015.

Irin wannan isharar da alama har yanzu jam’iyyun Nijeriya ba su dauke ta ba, domin har kawo yanzu da saura shekara daya kacal a sake yin babban zaben kasar, jam’iyyar APC mai mulkin kasar kullum kare kurakuren gwamnatin shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ta ke yi, duk da cewa, alamu na nuni da cewa, kullum farin jinin gwamnatinsa raguwa ya ke yi a gurin ’yan kasa, wanda hakan ya na iya shafar sakamakon zaben 2019 da ke tafe a badi.

A nanya wajaba shugabannin jam’iyyun Nijeriya su zama masu hange da yiwa jam’iyyunsu gata wajen kare manufofinta ba manufofin shugabannin kasa ba, wanda hakan ne kadai zai iya taimakonta wajen kare farin jininta da kuma karfin fada a jinta a wajen ’yan kasa, musamman a lokutan manyan zabuka.

 

Exit mobile version