Sulaiman Bala Idris 07036666850
A wasu lokutan, babu wurin da nake shiga na ji daɗi, na more wa rayuwa ta, cikin nishaɗi da annashuwa fiye da kafafen sadarwa na internet. Duk da wuri ne da ke da ban haushi da cin rai. Musamman ma kafar Facebook. Duk me bibiyan al’ummarmu ta Nijeriya, zai fahimci abin da nake nufi.
A Arewacin Nijeriya, a duk mako akan samu wani maudu’i na musamman. Wanda za a tada jijiyar wuya yadda ya kamata. A tada hankulan juna, a samu saɓani tsakanin makusanta, da abokan hulɗa.
An daɗe ana samun saɓani irin wannan, aminai sun yi rabuwar baram-baram sakamakon irin wannan cacar baki da saɓanin babu gaira ba dalili. Har ma ya zama yanzu, akwai ɓangarori biyu a tsakanin al’ummar Arewa, musamman a Facebook. Duk yayin da wani maudu’i ya samu, ‘yan wancan ɓangaren zasu ja daga, a fara fafatawa a tsakani. Sai sauran membobi kowa ya bi bayan ƙungiyarsa.
Ƙarshen makon da ya gabata, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake bayar da wani aikin ga al’ummanmu na Arewa a kafafen wadarwa. Bayan da a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, Fadar Shugaban Ƙasa ta ayyana sunan Aisha Ahmad, ‘yar shekaru 40 da haihuwa a matsayin Mataimakiyar Shugaban Babban Bankin Nijeriya. wannan ayyanawa ta biyo bayan tantancewar majalisar dattawa ne.
Aishah Ahmad, ta ɗauki lokaci mai tsawo tana gudanar da harkar banki, majiya mai tushe ta bayyana cewa ta share shekaru 20 a cikin wannan harkar.
An haifi Aisha a ranar 26 ga watan Oktoban 1977; Aishah wacce ‘yar asalin jihar Neja ce, kafin a bata wannan sabon muƙami, ta kasance babbar daraktan sashe a bankin ‘Diamond’.
Babu ruwan masu gardamar soshiyal Midiya da ƙwarewa ko kaifin basirar Aisha, gaggawar kallon tsiraicin da ta bayyana a da yawan hotunanta ake yi. Da gaske hotunanta da aka sake bayan an ayyana sunanta da muƙaminta, hotuna ne da ba zasu samu matsuguni a ƙwaƙwalen al’umman Arewa maso yamma, da arewa maso gabashin Nijeriya ba.
Lokacin da na ga an ɗau muhawara, lamurra sun yi ɗumi dangane da hotunan Misis Aisha, na yi ta bibiyan masu cacar bakin, domin na iya fahimtar haƙiƙanin abubuwan da kowanne ɓangare ke nufi.
A ƙashin gaskiya, hotunan da aka sake ɗin, sun saɓawa tunanin al’adar asalin al’ummar ƙasar Hausa, wannan idan za mu fara fashin baƙi a ɓangaren al’ada kenan. Sai dai, ita Misis Aisha ‘yar asalin Jihar Neja ce, kuma daga adalcin da zan iya yi wa ‘yan asalin jihar Neja waɗanda na ga sun haƙiƙance wurin ba ta kariya, sun ce a al’adarsu wannan shiga da ta yi babu alamin saɓa ƙa’ida ta al’adarsu a ciki.
Ko ba komi, Aishar CBN ta ƙara suna, waɗanda ma basu santa ba sun santa. Sannan jama’a da yawa sun sa hotunanta a wayoyinsu da kwamfutocinsu. Abu ɗaya ya yi saura wanda ‘yan Nijeriya za su jira daga Aishar CBN, shin za ta ba mara ɗa kunya a ayyukanta, ko za ta ƙara zama maudu’in tattaunawa a kafafen sadarwa nan ba da jima wa. Kallo ya koma sama!