Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

bySulaiman
4 months ago
Astana

Kwanan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake haduwa da takwarorinsa na kasashen Kazakhstan da Kyrgyzstan da Tajikistan da Turkmenistan da kuma Uzbekistan a birnin Astana, inda suka halarci taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu, don bude sabon babin hadin gwiwar kasashensu. 

Haduwarsu a wannan karo ta biyo bayan wacce suka yi a yayin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na farko da aka gudanar a birnin Xi’an na kasar Sin shekaru biyu da suka wuce. A wannan karo kuma, kasashen sun fitar da sanarwar Astana game da taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu, tare da rattaba hannu a kan yarjejeniyar kyakkyawar makwabtaka da abota da kuma hadin gwiwa na dindindin, baya ga shirye-shiryen hadin gwiwa har 110 da suka cimma.

  • IGP Ya Sake Bayar Da Umarnin Cafko Masa Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Bata Wa Ganduje 
  • Ba Za Mu Yarda A Yi Mana Ƙarfa-ƙarfa Ba – Ayatollah Ya Gargaɗi Amurka

Sai dai ma’anar taron ba ta tsaya ga wadannan nasarorin da aka cimma ba, abun da ya fi muhimmanci shi ne taron ya shaida inda za mu dosa musamman a yayin da duniyarmu ke fama da rashin tabbas da tashe-tashen hankula.

A yayin da shugaba Xi Jinping ke halartar taron, ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana hadin gwiwar Sin da kasashen tsakiyar Asiya a matsayin “ruhin Sin da kasashen tsakiyar Asiya”, da ke “martaba juna da amincewa da juna da cin moriyar juna da kuma taimakon juna, da zamanantar da kowa ta tabbatar da ci gaba mai inganci.”

A bisa ruhin ne, Sin da kasashen nan biyar ke ta fadada hadin gwiwarsu, tare da karfafa hadin kansu don rungumar kyakkyawar makomarsu ta bai-daya. Idan mun duba, tun bayan taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na farko da aka gudanar a shekaru biyu da suka wuce, adadin cinikin da ke tsakanin Sin da kasashen nan biyar ya karu da kaso 35%, baya ga yadda suka inganta hadin gwiwarsu ta fannonin zuba jari da hakar ma’adinai ba tare da gurbata muhalli ba, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Baya ga haka, a hukumance ne aka fara aikin gina layin dogon da ya ratsa kasashen Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, kuma Sin da kasashen sun gina cibiyoyin al’adu a kasashen juna, kana Sin da Kazakhstan da kuma Uzbekistan sun cire wa al’ummomin juna bizar shiga kasashensu.

A shekaru biyu da suka wuce, shugaban kasar Sin da takwarorinsa na kasashen nan biyar sun dasa wasu bishiyoyin ruman guda shida a birnin Xi’an, wadanda yanzu haka cike suke da furanni tare da alamanta hadin gwiwar kasashen mai cike da kyawawan nasarori, wadanda kuma suka shaida cewa, “hannu daya ba ya daukar jinka”, hada karfi da karfe ne zai kai ga inda aka dosa, kuma ba wanda ke iya cin nasara daga faduwar wasu, kuma za a iya tabbatar da nasara ga juna ne kurum idan aka zama tsintsiya madaurinki guda.

Yanzu haka, duniyarmu na fama da rikice-rikice da kariyar ciniki da ra’ayi na kashin kai da kuma siyasar nuna fin karfi. Amma bai kamata a mai da hannun agogon baya ba, kuma ba za a yarda da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummomin duniya ba, kana ‘yan Adam bai kamata su koma irin rayuwar da masu karfi ke cin zalin masu karamin karfi kamar yadda aka yi a baya ba.

Daga birnin Xi’an zuwa Astana, Sin da kasashen tsakiyar Asiya sun samar da ruhin da ya amsa tambayar da zamaninmu ya aza mana, wato “me ya faru a duniyarmu, kuma me ya kamata mu yi”, wanda kuma ya karfafa mana niyyar kiyaye adalci da cin moriyar juna da samun nasara tare, don kiyaye zaman lafiyar duniya da tabbatar da ci gaban kasa da kasa baki daya. (Lubabatu Lei)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kai Farmaki Masana’antar Kera Bindiga, Sun Yi Kame A Taraba

An Kashe 'Yan Ta'adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu - Hedikwatar Tsaro 

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version