Yusuf Shuaibu" />

Daga Yanzu Farashin Buhun Shinkafa Zai Koma Naira 15,000 – Manoma

A korarin karfafa wa gwamnatin tarayya na hana fasakaurin shinkafa a kasar nan, kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya ta ce, daga yanzu buhun shinkafa ba zai wuce naira 15,000 ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamin a garin Abuja, shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya (RIPAN), Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sayar da buhun shinkafa sama da farashin kungiya.

Ya kara da cewa, shinkafar gida da ake yi a Nijeriya ba ta wuce tsakanin naira 13,300 zuwa 14,000, yayin da ita kuma ta gwamnati ta kai 15,000. Kungiyar ta bayyana cewa, ta rubuta wa gwamnatin tarayya wasika wajen karya farashin shinkafa, domin ta karfafa wa gwamnati wajen hana fasakaurin shinkafa a kasar nan. Shuwagabannin kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, Nijeriya tana asarar dala miliyan 400 wajen fasakaurin shinkafa daga kasar Jamhuriyar Benin.

Alhaji Mohammed Abubakar Maifata tare da matemakinsa Mista Paul Eluhaiwe sun bayyana cewa, sun kammala tuntubar mutanensu da ke bakin iyakar kasar nan. Shugaban kungiyar RIPAN ya ci gaba da cewa, akwai tan 500,000 na shinkafa da ake kan hanyar shigo da su kasar nan daga Thailand kafin bikin kirsimeti.

A cewar shugaban kungiyar, ba shakka wannan zai sa masu fasakaurin shinkafa su yi asarar dala miliyan 4000. A bangaransa, rufe iyakar da ke tsakanin Nijeriya da kasar Benin zai taimaka wajen dakile fasakaurin shinkafa tare habbaka shinkafar gida.

Ya kara da cewa, kungiyar tana goyan bayan gwamnatin tarayya wajen kulle iyakar kasar nan. Kungiyar ta babbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za ta saka wa ‘ya’yan kungiyar haraji domin ta cike gurbin farashin shinkafa a kasuwa, sakamakon rufe iyakar kasar nan. Ta kara da cewa, kasar nan tana bukatar tan miliyan hudu na shinkafa a duk sheka, amma mambobin kungiyar za su shigo da shinkafa wanda ya kai tan miliyan biyar.

Mohammed Abubarkar ya ce, “tun daga watan Junairu har zuwa yau, ba a shigo da shinkafar da ta kai miliyan daya ba daga kasar Jumhuriyan Benin da Thailand da kuma India zuwa Nijeriya ta haramtacciyar hanya.

Ya kara da cewa, mafi yawancin shinkafar da ake shigowa da ita daga kasar Benin, ‘yan kasar Benin ba sa amfani da wannan shinkafa shi ya sa ake kawota Nijeriya. Lokacin da aka rufe iyakar kasar nan, ‘ya’yan kungiyar RIPAN sun bayyana cewa, “daga yau saun dauki damarar noman shinkafa yadda ya kamata.”

Mohammed Abubarkar ya ce, kungiyarsa sun kwashe sama da shekara biyu suna neman a rufe iyakar kasar nan, saboda su sauko da farashin shinkafa. A cikin bayanin da ya gabatar ranar Laraba a garin Abuja, mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina, ya bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa, zai dauki mataki a kan masu safarar shinkafa lokacin da ya hadu da shugaban kasar Benin a kasar Japan. Shugaban kasar ya kara da cewa, ayyukan masu fasakaurin shinkafa yana kawo barazana ga tsarin da gwamnatinsa take yi wajen bunkasa harkokin noma.

A cewar shugaba Buhari, “a yanzu mutane suna komawa karkara domin su ci gaba da noma gonakinsu, kasar tana samun kudadan shiga, maimakon amfani da shinkafar kasar waje. Ba za mu taba barin yarda a ci gaban da fasakaurin kayayyakin ba,” in ji shi. Shugaban Nijeriya ya ce, mukasudin rufe iyakar kasar nan shi ne, ‘yan Nijeriya su bunkasa kayayyakin gida.

Tun da farko dai, shugaban kasar Benin Talon ya bayyana cewa, ya yi kira ga shugaban Nijeriya sakamakon alfanun da mutanen kasar suka samu game da rufe iyakar kasar.

Exit mobile version