Hukumar kula da gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta nakasassu ta duniya ta dage wasan linkaya da wasan daga abu mai nauyi wanda aka shirya yi a kasar Medico sakamakon girgizar kasar da kayi a kasar.
Tun farko dai an shirya za’a fara gasar a ranar talatin ga wannan watan sai dai tsarin ya gamu da cikas bayan da aka samu annobar girgizar kasa a kasar ta medico abinda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da rushewar gine-gine.
Shugaban hukumar, Andrew Person ya bayyana cewa sakamakon wannan masifa dole yanzu zasu hada kai da hukumar kasar domin ceto mutane sannan kuma dole a ajiye maganar gasar sai nan gaba saboda nuna damuwa ga mutanen kasar da gwamnati.
Yakara da cewa abinda yake gaban hukumarsa shine ya tabbatar da bganin wakilan hukumar wadanda tuni suke kasar ta Medico don fara shirye-shiryen gasar sun bar kasar cikin koshin lafiya.