Dahiru Bauchi Ya Nemi Shugabanni Su Inganta Rayuwar Mutane Da Alheri

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci shugabanni a Nijeriya da su rika inganta rayuwar jama’a ta hanyar tuna irin alkawurran da suka yi na ingata rayuwar jama’a ta hanyar samar da alheri da kawar da sharri a lokacin da suke yakin neman guri’un masu zabe.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan nasiha ce a gidan sa wannan Talatar a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai don godewa mutanen da suka halarci tarurrukan maulidin da suka gudana a Abuja da Kaduna a karshen makon da ya wuce. Inda cikin jawabansa ya godewa shugabannin da suka halarci taron da kuma dukkan talakawa da almajirai da suka amsa kira, domin nuna soyayyar su ga fiyayyen halitta manzo (SAW) wajen halartar tarukan da suke kara karfin guiwa ga al’ummar musulmi wajen yin riko da addinin Allah tare kuma da bin shari’a kamar yadda manzon tsira ya zo da sako don isar wa dukkan musulmin duniya.

Don haka Sheikh Dahiru Bauchi ya yaba wa dukkan mutanen Nijeriya da na kasashen waje da suka zo taron don daukaka kalmar Allah musamman ganin dukkan mutanen da aka tara kowa shi ne ya kawo kansa ba wanda aka ba wani abu sai ko shi ya dauki nauyin kan sa don zuwa wannan taro da a ka jima ana gudanar da shi don kara kusanto da mutane zuwa ga son Manzo (SAW) da bin umarnin Allah madaukakin Sarki tare da ambaton Allah, don neman yardarsa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da jan hankalin shugabannin kasa su ji tausayi su sani shi mulki wani abu ne da ake zabar mutum don ya kawo alheri ya ture sharri don haka mutane ke zabar mutanen da suka fito suka nemi a zabe su don su kawo alheri ga mutanen kasa. Saboda haka suke fitowa don zabar mutum a duk lokacin da ya fito siyasa ya nemi a zabe shi don ya kawo alheri ya ture sharri, shi yasa a kullum talaka ke ganin duk wanda ya furta zai yi alheri suke ganin ba makawa zai aikata alherin. Don haka ya roki shugabanni su sani mutane sun zabe su ne domin su samar musu da alheri su kawar musu da sharri, tare kuma da kawar musu wahala da samar musu jin dadi a rayuwar su ta hanyar cika alkawarin da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma shi alkawari abin tambaya ne ranar lahira.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ja hankalin shugabannin kan su fahimci cewa alkawari suka yi don inganta rayuwar mutanen Nijeriya ba don su samar da wahala ga mutane ba. Don haka ne a lokacin da dan siyasa ya fito baya tallata kan sa da zai samar da wahala ga mutane sai ko ya tallata kan sa da zai samar wa mutane jin dadi da alheri don haka ya kamata su cika wannan alkawari su san cewa mutane na cikin wahala kuma suna neman tallafin gwamnati don rayuwar su ta inganta. Saboda haka ya roki shugabannin kan su lura da irin mawuyacin halin da talakawan Nijeriya ke ciki wajen sassauta manufofin da suke dauka kan tattalin arziki a kasa don mutane su fita daga cikin wahalar da suke fama da ita a wannan lokaci.

 

Exit mobile version