Daidaita Farashin Man Fetur Zai Hana Hauhawar Kayayyaki, Inji Masani

Abinci

A daidai lokacin da ake ta kara samun hauhawar farashin kayayyaki wanda ya zarce na kashi 12.82 wanda aka samu a baya kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta fatar da rahotonta. An dai kara samu hauhawar farashin kayayyakin fiya da na shekarun baya. Duk wata ana samun karuwar hauhawar farashin kayayyaki na kashi 1.25 har zuwa watan yau. An dai samu canjin na tsawon wata 12 har zuwa karshen shekarar da ta gabata.

A wata bayan wata, ana samun hauhawar farashin kayayyaki wanda ya kai na kashi 1.27 a burane. inda aka samu kashi 1.23 a shekarar 2020, yayin da a yankunan karkara kuma aka samu hauhawar farashin kayayyaki wanda ya kai na kashi 1.23. A cikin watanni 12 a kowacce shekara ana samun karin hauhawar farashi a burane wanda ya kai na kashi 12.66. Wannan dai ya karu da kashi 12.50 idan aka kwatanta shi da rahoton watannin baya, yayin da a yankunan karkara a cikin watan Yuli aka samu na kashi 11.49, idan aka kwatanta shi da na watan Yuni na kashi 11.36.

Bisa ga rahoton da aka wallafa a ranar Litinin, wani shahararren masanin tattalin arziki da kuma farfesa a kan harkokin kudade da ke karantarwa a jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Uche Uwalaka, ya bayyana cewa, karuwar hauhawar farashin kayayyakin da ake samu a cikin kasar nan yana raunata ayyuakn tattalin arziki.

Ya ce, “an dai taba fuskantar irin wannan matsala a cikin harkokin kasuwaci wanda ya haddasa karuwar rashin ayyukan yi a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

“Dalilin da ya sa ake kara samun hauhawar farashin kudade dai sun hada da karin harajin kayayyaki da karuwar farashin mai da rufe iyakokin kasar na da cutar Korona da kuma matsalar tsaro wanda ya mamaye wasu yankuna a Nijeriya. Wadannan abubuwa su suka ruruta wutar hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a yanzu.”

Ya bayyana cewa, hanya mafi dacewa da za a shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki dai shi ne, gabatar da tsare-tsare a cikin sha’anin kudade da daidaita farashin mai wanda zai iya magance kashi 15 daga cikin matsalar. Ya kara da cewa ya kamara gwamnati ta kawo wani tsari da zai dai-daita farashin mai ba tare da samun matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu ba.

Exit mobile version