Wata kungiyar da ke fafatukar hana wariya ,Kick It Out, ta bukaci kungiyar Manchester United da ta hana magoya bayanta yi wa Romelu Lukaku rera wake-waken wariya.
Kungiyar ta ce wakar, wadda a cikinta ake kalamai kan girman mazakutar Dan wasan gaban kasar Belgium din, nuna wariya ce.
“Babu yadda za a lamunci nuna wariya, koda kuwa hakan ana nufin nuna goyon baya ne ga dan wasa,” in ji kungiyar Kick It Out.
Manchester United ta ce za ta tattauna da kungiyar game da al’amarin. Kick it Out game da lamarin.