Dakarun Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dakarun Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya

byCMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Mataimakin sakatare janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya yabawa dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin bisa nasarorin da suka samu a ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalisar.

Jean-Pierre Lacroix ya ce, dakarun suna taka muhimmiyar rawa tare da bayar da gudunmawa gaya wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

  • Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Al’Ummun Asiya

Jami’in wanda ya zanta da wakilin kafar CMG yayin babban taron zauren MDD na 77 dake gudana a birnin New York, ya jaddada cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na Sin sun gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankuna kamar na Gabas ta Tsakiya da Afrika, kana sun nuna sanin ya kamata irin na babbar kasa yayin da suke aikin.

A cewar wata takardar bayani mai taken “shekarun 30 da shigar sojojin kasar Sin cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD” da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a shekarar 2020, sojojin kasar na nuna goyon baya mai karfi ga shirin wanzar da zaman lafiya na MDD na ko-ta-kwana.

Yanzu haka, kasar Sin ta kammala wata rundunar shirin ko-ta-kwana dake kunshe da sojoji 8,000 da rukunoni 28 na kwararru a bangarori 10. Game da hakan, Jean-Pierre Lacroix ya ce kasar Sin ta bayar da gudunmawa ga zaman lafiyar duniya a aikace, kuma MDD za ta ci gaba da hada hannu da ita a harkoki masu ruwa da tsaki.

Yanzu haka, adadin dakarun kasar Sin shi ne mafi yawa cikin mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD. Haka kuma, kasar ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya kusan 30, inda ta tura sama da dakaru 50,000. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Wakilin Kasar Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Daina Tsoma Bakin Soja Ba Bisa Ka’ida Ba A Syria

Wakilin Kasar Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Daina Tsoma Bakin Soja Ba Bisa Ka'ida Ba A Syria

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version