Daga Sulaiman Ibrahim,
Jami’an Hukumar Shige da fice ta Kasa NIS da ke sintiri a kan teku a yankin Kuros Ribas sun kubutar da wani jariri dan makonni uku da haihuwa wanda ake zargin fataucinsa aka yi.
Ezugwu ya ce, jami’an sintiri na kan teku ne suka cafke wacce ake zargin bayan rashin iya bayar da cikakken bayani game da hakikanin mallakar jaririn.
“Kwanakin baya, jami’anmu da ke sintiri akan teku na kasa da kasa sun tare wata mata mai suna Maureen Awokara, wacce ta yi ikirarin cewa ita ‘yar asalin jihar Imo ce tare da wani dan jaririn makonni-uku.
“A lokacin da aka kamata, ta zo da wasu labarai na bogi Wanda Sam ba kamshin gaskiya cikinsu. Da farko, ta ce yaron na ‘yar uwarta ne, amma duk da haka mun gudanar da bincike na farko kuma duk layin salular da ta ba mu don tuntubar ‘yar uwarta Chioma Iweh wacce ta ce jaririnta ne, layin baya tafiya.
Za a mika jaririn da wacce ake zargi da fataucin ga hukumar NAPTIP don ci gaba da bincike. Binciken farko ya bamu cikakken dalili na gaskata cewa jaririn satoshi akayi.
“Wacce ake zargin ta yi ikirarin cewa za ta je Kamaru, Gabon, dama dai duk inda zataje. Hukumar na zargin satan yara, wannan yasa hukumar tasa ido a duk hanyoyin da masu fataucin ka iya bi don fataucin yaran musamman hanyoyin iyakokin filin jirgin sama. Hakan ya tilastawa masu fataucin neman wasu hanyoyin, kamar amfani da kananan kwale-kwale ta hanyar ruwa don fita da yaran.
CIS Ezugwu ya ci gaba da bayanin cewa kokarin da rundunar ta yi don tuntubar wasu ‘yan uwanta don sanin ko ‘yan uwan sun amince da ita akan daukar jaririn, abin ya ci tura saboda wacce ake zargin ba ta son ba da bayanai masu amfani a kan lamarin. .
Shugaban ya bukaci iyaye da su kula da yaransu koyaushe cikin soyayya da kulawa kuma su guji duk wani nau’i na sallama ‘ya’yansu saboda kudi.