Dakarun soji na rundunar ‘yantar da al’ummmar kasar Sin ko PLA reshen kudanci, sun gudanar da jerin sintiri a yankin tekun kudancin kasar Sin. A cewar kakakin rundunar Tian Junli, sojojin sun gudanar da ayyukan sintirin ne a jiya Laraba kamar yadda suka saba yi lokaci bayan lokaci.
Tian Junli, ya ce kasar Philippines ta yi hadin gwiwa da wasu kasashe na wajen yankin, wajen tsara abun da suka kira sintirin hadin kai, wanda hakan ya illata yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin.
Tian, ya jaddada cewa sojojin rundunar PLA reshen kudanci, suna cikin matukar shirin kare ikon mulkin kai na yankunan Sin, da ma hakkokin teku na kasar. Ya ce “Duk wani yunkuri na tayar da husuma a yankin tekun kudancin kasar Sin, da haifar da yanayin zaman dar dar ba zai yi nasara ba”. (Mai fassara: Saminu Alhassan)