An dakatar da tsohuwar ‘yar gudun mita 1,500 Asli Cakir Alptekin daga wasan na gudu har abada, bayan da aka sameta da laifin shan abubuwa masu kara kuzari.
An samu ‘yar wasan mai shekara 32 da laifi a shekarar 2015, inda aka karbe lambar yabon da ta ci a gasar Olympic da gasar Turai a 2012.
A kuma shekarar ce hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta Turkiya ta dagatar da ita shekara takwas bayan nanma an kamata da laifin kwayoyi masu kara kuzari.
Tun farko an yanke wa Cakir Alptekin hukuncin dakatar da ita shekara biyu a 2004, bayan da aka same ta da laifi a gasar matasa ta duniya.
’Yar wasan dai tayi fice wajen wasannin guje-guje da tsalle inda ta lashe manyan kyaututtuka a wasanni daban-daban.