An Dakatar Da Samir Nasri Watanni 6 Daga Buga Wasa

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Samir Nasri na fuskantar haramcin buga kwallo tsawon wata shida da aka same shi da laifin yin karin ruwan da ya keta dokokin hukumar a wani asibitin Los Angeles a shekarar 2016, a cewar lauyansa.

An yi wa Nasri, mai shekara 30, dan kasar faransa karin ruwan ne a lokacin da yake hutu, sai dai hakan ya saba dokar hukumar hana shan abubuwan kara kuzari, lamarin da ya sa hukumar da ke kaasar Sipaniya ta bincike shi.

Lauyan Nasri ya shaida wa  manema labarai cewa Uefa ce da kanta za ta yi masa wannan haramcin na hanashi buga wasanni.

Wani kamfani mai zaman kansa na likitoci mai suna Drip Doctors ya yi wa Nasri, wanda ba shi da kungiya da yake buga wa kwallo tun bayan barinsa Antalyaspor na kasar Turkiya a watan Janairu, karin ruwan a otal dinsa da yake zaune.

A wancan lokacin, Manchester City ta bai wa Sebilla aron dan wasan kuma hoton da ya dauka da daya daga cikin shugabannin kamfanin Jamila Sozahdah ya jawo ce-ce-ku-ce.

Exit mobile version