Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta dakatar da shugaban kungiyar Jubentus Andrea Agnelli daga aiki tsawon shekara guda, sakamakon samunsa da laifin saida tikitin shiga kallon wasannin kungiyar ba bisa ka’ida ba, ga wasu kungiyoyin magoya bayan kungiyar ta Jubentus da basu cancanta ba.
Sakamakon laifin, Agnelli zai kuma biya tarar euro 20,000, yayinda ita kuma kungiyar ta Jubentus zata biya tarar euro 300,000, sai kuma wasu manyan jami’anta uku da suma aka dakatar saboda hannunsu cikin saida tikitin.
Da fari dai mai gabatar da kara Giuseppe Pecoraro, ya bukaci a haramtawa shugaban kingiyar ta Jubentus Agnelli, shiga al’amuran wasannin ne tsawon shekaru 2 da rabi, ya kuma biya tarar euro dubu hamsin, a maimakon euro dubu ashirin da hukumar kwallon kafar ta ce ya biya a yanzu.
Sai dai fa Pecoraro ya ce yana tunanin komawa wata kotun ta daban banda ta hukumar wasannin, domin kara tsaurar hukuncin kan kungiyar ta Jubentus da mai horar da ita.