Muhd Shafiu Sale" />

Dakta Daniel Shagah Ya Zama Sabon Sarkin Yankan Masarautar Numan

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da nadin Dakta Daniel Shagah Ismaila a matsayin sabon Sarkin Numan (Hama Bachama) na 28 biyo bayan rasuwar sarkin na Numan, Marigayi Honest Irmiya Stephen, a watan da ta gabata.

A cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan, Humwhashi Wonosikuo, ya aike wa manema labarai, ya kuma taya sabon sarkin murna, sannan ya yaba da yadda zaben sabon sarkin ya gudana ba tare da cece-kuce ba.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “bisa la’akari da kwarewar da sabon sarkin ke da ita kan sha’anin miyagun kwayoyi, babu wata tantama zai iya jagorantar jama’a a abinda ya dace, musamman ganin yadda zabensa ya gudana cikin ruwan sanyi.

“Na yarda da cewa, shi zai cika muradin tsohon sarki, Honest Stephen, wanda ya tsayar da mulkinsa bisa kokarin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya,” in ji sanarwar.

Haka kuma gwamnan ya bukaci sabon sarkin da ya sa alummarsa da jihar a gaba, ya kuma yi amfani da kwarewarsa a lokacin da jihar ke fuskantar kalubale mai girma da kuma cigaba.

Sanarwar ta kuma roki jama’ar masarautar da su kula da muhimmancin gina zaman lafiya da kuma al’adun da su ka gada.

Exit mobile version