Zubairu T M Lawal" />

Dakta Joseph Kigbu Ya Bukaci Likitoci Su Taimakawa Nijeriya

Shugaban Tawagar Gidauniyar Kwararrun Likitocin Afirika (Doctors on the move Africa).
Hon. Joseph Haruna Kigbu, ya yi kira ga ‘yan’uwansa Likitoci da su rika aiki tsakani da Allah domin taimakawa al’umman Nijeriya. Hon. Joseph Haruna Kigbu, ya yi wannan jawabin ne a wajen taron karawa juna sani ga Ma’aikatan kiwon lafiya, a Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauci.
Taron da aka bude shi na kwanaki biyar, wanda ya fara daga ranar Talata mai taken sanin makaman aiki. Makasudin taron an shirya shi ne domin koyan sanin makaman aikin kiwon lafiya.
Likitan Talakawa, ya yi kira ga duk wani Likitan da yake son ci gaba a bakin aikinsa, sai ya tausayawa al’umma musamman marasa lafiya.
Ya ce; sau da yawa mutane sukan bude Asibiti da zimman wai za su taimaki al’umma, amma sai ka ga ya zama wajen gallaza ma al’umma.
Ya ce; duk Likita an sanshi da nau’i na tausayi. Dole ne Likita ya tausayawa marasa lafiya a dukkan halin da ka tarar da shi. Ya kara da cewa, Likita an sanshi da ba da hankali wajen kula da marasa lafiya, amma bai dace a ce Likitoci suna watsewa a Asibiti su bar marasa lafiya cikin wani hali na damuwa ba.
Hakkin Likita ne a sameshi a bakin aiki na tsawon awa 24, Hon. Kigbu ya ce; ya wajaba a garemu mu Likitoci mu taimakawa al’umman kasan nan.
Ya kara da cewa, halin da al’umma ke ciki na rashin lafiya da cututtuka kala-kala amma abin takaici wasu Likitocin ko da maganin zazzabin cizon sauro ba su iya taimakawa al’umma da shi, a matsayin kyauta.
Hon. Joseph Haruna Kigbu ya ce; ya shafe shekaru goma sha biyar yana gudanar da aikin kiwon lafiya kyauta a matsayinsa na kashin kansa.
Ya ce; ya samu daukaka ne ta hanyar taimakawa al’umma, yau ga shi ko ta ina ana jin sunan Doctor’s on the move Africa, ba komai ba ne illa mu sanya tausayi mu rika taimakawa al’umman kasa.
Kowa ya ga halin da Asibitoci suke ciki, wani lokacin gara mara lafiya ya je Asibitin kudi, to idan Asibitin kudi shi ma ya gagara ina Talakawa za su je su nemi lafiya.?
Hon. Joseph Haruna Kigbu, ya yi kira ga kananan Likitoci masu tasowa da su yi amfani da damarsu wajen taimakawa al’umman kasa da ilimin da Allah Ya ba su na bangaren jinya, su zama masu tausayawa.
Ya kara da cewa; yanzu tawagar kwararrun Likitocin Afirika wanda ake kira (Doctors on the move Africa) tana janyo Likitoci daga bangare daban-daban tana amfani da su domin su kara samun basira da iya gudanar da ayyukan jinya.

Exit mobile version