Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

Maryam Ibrahim Shettima

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Tun farkon kafuwar duniya har zuwa yau, a cikin kowane karni, a cikin kowace al’umma, a kowane zamani, allah ya na fito da wasu mata ‘yan gwagwarmaya da su ke taimakon al’umma, Allah ya bayyanar da Hajiya Maryam Shetty a cikin wannan zamani namu da muke ciki.

A fannin gwagwarmayar siyasa da ba da gudunmawa ga masu mulki, Hajiya Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Sarauniya Raziya Shamsuddeen Iltutmish, wacce ta rasu shakaru 780 da suka gabata. jarumar mace ce wacce ta gaji mahaifinta a Birnin Delhi lokacin India da Pakistan na hade, ta taimaki shugabancin mahaifinta a sarari da boye dukkan yakokin da mahaifinta ya fita tare take da shi a cikin rundunar mayaka.

Ta fuskar taimakon al’umma kuwa, Shetty ta na kamanceceniya da Sarauniya Diana, matar da saboda dumbin ayyukan alkhairanta ga al’umma ake kiranta da suna people’s princess”, (sarauniyar al’umma), kamar yadda ake kiran Hajiya Maryam Shetty da suna (sarauniyar arewa) a wannan zamani namu.

-A bangaren nemowa mata ‘yanci kuwa, Dakta Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Emmeline Pankhurst, ‘yar gwagwarmaya wacce ta yi fafutukar kare ‘yanci da nemo hakkokin mata a Kasar Birtaniya wacce ta yi rayuwa a shekarun (1858 zuwa 1928).

A wannan rana na ga dacewar na yi rubutu akan nagartattun mata ‘yan kishin kasa wadanda su ke ba da gudunmawa cikin al’umma kamar Hajiya Maryam Shetty da kuma irin tasirin da su ke da shi a cikin siyasa da harkokin mulki. Kafin na kai ga yin bayani akan wacece Hajiya Maryam Shetty da irin kwazonta, zan dan yi shimfidar bayani akan mata da irin jajircewarsu ga cigaban al’umma tun kafin wannan zamani da mu ke ciki.

Idan mu ka fara yin duba da tarihin musulunci, za mu ga cewa Mafi yawan shahararrun malaman da su ka tattara hadisan manzon Allah (S.A.W) a farko-farko mata ne su ka karantar da su. Misali: Ibn Hajar ya dauki darasi a wurin mata kimanin 53. Shi ma As-Sakhawi ya yi karatu a wurin mata kimanin 68. Imam Suyuti shi ma ya yi karatu a wurin mata kimanin 33.

Akwai dumbin manyan mata masu daraja wadanda tarihin musulunci ba zai manta da gudunmawarsu ba. Misali: Ashifa Bint Abdullahi ta kasance mace ta farko da Khalifa Umar Ibn Al-Khattab ya nada a matsayin jami’a mai sa ido kan harkokin kasuwanci. Amra Bint Abdurrahma ita ma daya ce daga cikin manyan Malamai masana hadisi da sauran ilimummuka da kuma ba da fatawa kan lamuran addinin musulunci a cikin karni na takwas.

A zamanin Khalifa Umar Ibn Abdul’aziz ana kallonta a matsayin babbar maruwaiciyar hadisai masu alaka da Nana A’isha matar Manzon Allah (SAW). Daga cikin dalibanta, akwai: Abubakar Ibn Hazim sanannen mai shari’a a birnin Madina wanda Khalifa Umar Ibn Abdul’aziz ya umarce shi da ya tattara dukkan hadisan da ta ruwaito wuri guda.

Ita ma Aisha bint Muhammad Ibn Abdul Hadi ta kasance malama wacce ta karantar da dumbin shahararru malamai a birnin Damascus. Daga cikin malaman da ta koyar sun hada da Ibn Hajar Al-Askalani babban malami a zamaninta. Sai kuma Fatima Al-Batayahiyya babbar mace ce a karni na takwas wacce ta karantar da dalibanta ilimin hadisi a sallacin manzon Allah (S.A.W).

A karni na tara akwai Fatima Al-Fihriyya a Fez na kasar Moroko wacce ta assasa Masallacin Al-Karawwiyya a shekara ta 859. Masallacin Karawwiyya wanda ya sanu a tsakanin Larabawa su ke kuma amfani da shi, a Europe ya zama dadaddiyar jami’a ta farko a duniya wacce ta ke cigaba da amfani har zuwa yau. Dalibai su kan tashi daga sassa daban-daban na duniya su je neman ilimin addinin musulunci da na Harsuna da kuma na kimiyya. Fatima Cordoba mai dakunan karatu ce (Librarian) a karni na goma wacce ta samar da dakunan karatu na jama’a guda 70 masu littattafai 400,000.

Bayan su sai kuma wasu matan wadanda su ka hada da: Abidah Al-Madaniyya, Abdah Bint Bishir, Umma Umar Ath-Thakafiyya, Zainab jikar Ali Ibn Abdullahi Ibn Abbas, Nafisa Bint Al-Hassan Ibn Ziyad, Khadijah Ummu Muhammad, Abdah Bint Abdurrahman, tare da sauransu wadanda su ka gabatar da darusan koyar da hadisan manzon Allah (SAW). Tunda farko Abida ta kasance baiwar Muhammad Ibn Yazid. Ta koyi ilimin sanin hadisai sama da guda 10,000.

Zainab Bint Sulayman ‘yar Sarki ce, Mahaifinta dan uwan As-Saffah ma’assasin masarautar Abbassid,  sannan kuma gwamnan Basrah, Omen da Bahrain a zamanin Khalifancin Al-Mansur. Zainab ta kasance mace wacce ta samu kykkyawan horo da sanin sanin Ilimin hadisi. Sannan kuma ta na daga cikin manyan mata malamai sanannu wadanda su ka koyar da manyan mashahuran malamai maza.

A karni na goma sha biyu akwai Shuhadah Bint Ahmad Al-Ibri wacce ta yi karatu a Baghdad tare da shahararrun malaman hadisi. Sannan ta kasance babbar malama masaniyar hukunce-hukuncen shari’a wacce ake yi mata lakabi da “Alfaharin mata”.

Zainab Bint Kamal ta koyar da hadisai sama da guda 400 a wasu daga cikin manyan shahararrun makarantun gaba da sakandire a birnin Damascus. Kuma ta samu kauna daga dalibanta. Akwai Fatima Bint Muhammad Al-Samarkandi, masaniyar ilimin hukunce-hukuncen shari’a wacce ta ba wa sananne mijinta shawarwari akan yadda ake yin fatawa.

A baya-bayan nan kuma, a cikin karni na 19, tarihi ya ba mu labarin tashi da nasarar Nana Asma’u a Nijeriya; mawakiya, malama, sannan kuma mashawarciya ga mahaifinta.

Wasu daga cikin manyan mata wadanda su ka ba wa al’umma gudunmawa ta fuskar likitanci a tarihin musulunci. Tun farkon zuwan Addinin Musulunci, mata sun samu damar sanin ilimin likitanci da kuma yi wa marasa lafiya maza da mata magani musamman ma a wurin yaki.

A zamanin Manzon Allah SAW an samu mace likita mai suna Rufayda Bint Sa’ad Al-Aslamiyya. A lokacin yakin Badar ranar 13 Ga Watan Mach, 624 CE ita ce ta yi wa musulmai mayaka magani kan raunukan da su ka samu. Rufaida ta samu mafi yawan iliminta na likitanci a wurin mahaifinta Sa’ad Al-Aslami wanda masanin kiwon lafiya ne.

Sai kuma Al-Shifa Bint Al-Kuraishiyya Al-Adawiyah, ta kasance daya daga cikin wayayyun mata a wancan lokacin wacce ta ke da ilimin magunguna. Sunanta na asali Layla, amma ta samu lakabin suna “Shifa” (Waraka).

Bayan ita sai kuma Nusayba Bint Ka’ab Al-Mazneya wacce ta gudanar da aikinta na Likitanci a lokacin yakin Uhud. Da kuma Ummu Sinan Al-Islami wacce ita ma ta nemi izinin Manzon Allah SAW ta je wurin yaki ta gudanar da aikin yin magani ga wadanda aka ji wa raunuka da kuma ba da ruwan sha ga mayaka.

Sai Ummu Warka Bint Harith wacce ta ba da gudunmawa wajen hada alkur’ani wuri guda, ita ma ta yi aikin likitanci a lokacin yakin Badar.

Dadi da kari, akwai Nusayba Bint Al-Harith wacce aka fi sani da Ummu Al-Athia, ita ma likita ce har kaciya ta ke yi sannan kuma ta ba da gudunmawa wajen ba da agajin gaggawa ga mayaka a filin daga da kuma tallafa musu da ruwan sha.

Bayan fannin ilimin lafiya, sauran fannonin ilimi ma ba a bar mata a baya ba. Sutayta Al-Mahamili gogaggiyar masaniyar ilimin lissafi ce da adabin Larabci da hadisi da sanin hukunce-hukuncen shari’a.

Sutayta ta taso a gida na ilimi a birnin Baghadad ta rayuwa a tsakiyar karni na 10. Ta samu yabo daga manyan malaman tarihi kamar su: Ibn al-Jawzi, Ibn al-Khatib Baghdadi da kuma Ibn Kathir.

Ayesha ‘ya ce ga Prince Ahmed na Andulus wacce ta rayuwa a karni na 11 gwana ce a fannin Ilimin Rhyme da Oratory. Sannan Labirare dinta ya kasance daya daga cikin kayatattun labirare cikakku a masarautar Andulus.

A fannin fasaha da zane mai kyau akwai Thana, baiwa a gidan Ibn Kayyum. Sai kuma Rasa a kasar Indiya wacce ta wallafa littafi kan magunguna da kulawa da mata. Sai kuma Mariyah Al-Kibtiyya ‘yar kasar Masar wacce ita ma ta yi wallafa a karni na bakwai. Wata kwararriyar a fannin ilimin kimiyya ita ce Al-Ijiliyyah Bint Al-Ijili Al-Asturlabi wacce ta bi sahun aikin mahaifinta na kimiyya a birnin Aleppo a Arewacin Siriya a karni na 10. Kadan kenan daga cikin manyan mata masana da aka taBa yi a tarihin Duniya.

Hatta Manzon Allah (S.A.W) ya samu nasarar yada addinin musulunci da gudunmawar mata iyalinsa. Matarsa Nana Khadija gawurtacciyar ‘yar kasuwa ce wacce Allah Ya azurta da tarin dukiya. Nana Khadija ta taimakawa manzon Allah (S.A.W) da gudunmawar kudin gudanar da da’awa da gudunmawar shawarwari da gudunmawar kykkyawar dabi’a tare da karfafa masa gwiwa kan aikinsa na isar da sakon Allah (Manzanci).

Daga cikin mata wadanda su ka yi sarauta kuwa, tarihi ba zai manta da :Arwa Al-Sulayhi a Yemeni ba, wacce ta shafe tsawon shekaru 71 akan karagar mulki a (karni na 11) ana yi mata lakabi da “Noble Lady”.

Sai Sultana Shajarat Al-Durr wacce ta karBi jagoranci kasar Egypt bayan rasuwar mijinta a (karni na 13).

Da kuma Dhayfa Khatun wacce ta ke mata ce ga dan gidan Salah Al-Din Al-Ayyubi. Ta zama Sarauniyar birnin Aleppo na tsawon shekaru 6 bayan rasuwar danta Sarki Abdul’Aziz.

Sarauniya Dhayfa ta fuskanci yakoki daga rukunonin mayakan addini wadanda su ka hada da: Khuarzmein, Mongols da kuma Seljuks. Dadi da kari a tsarin gudanarwarta ta al’umma da siyasa, ta dauki nauyin Ilimi a Aleppo inda ta gina makarantu guda biyu.

Sai kuma Sitt Al-Mulk ‘yar Sarkin Fatimid daga kasar Egypt kwararriyar mai gudanar da harkokin mulki bisa tafarkin addinin musulunci.

Sai kuma Razia Sultana mace ta tarko da ta taBa zama akan karagar sarautar India a birnin Delhi har tsawon shekaru 4 a cikin (karni na 13).

Firishta wani marubucin tarihi ne a karni na 18 ya bayyana Sarauniya Raziya da cewa “mace ce mai kan maza da zuciya irin ta maza wacce ta fi ‘ya’ya 20”.

Bayan wadannan sai kuma Hurrem Sultan (1500CE) wacce ake kira da suna Rodelana, asali baiwa ce wacce aka bautar a (Crimean Turks Raids) a kasar Ukraine a zamanin Yazuz Sultan Salim sannan aka gabatar da ita a fadar Ottoman ga sarki Suleyman wanda daga baya kuma ya aure ta.

Sarauniya Hurrem Sultan ta assasa manyan makarantu da dama wadanda su ka hada da masallatai da gidajen wanka na maza da na mata da makarantu guda biyu da asibitin mata a birnin Istanbul sai kuma wasu makarantun guda hudu a birnin Makkah da kuma masallaci a Jerusalem.

Sai kuma Amina A Nijeriya wacce ta yi sarautar birnin Zazzau a (karni na 16) a lokacin ta na ‘yar shekaru (16).

Sarauniya Amina ta zaBi ta koyi dabarun yaki da kuma jagorantar rundunar mayaka a kasar Zazzau. A tsawon mulkinta na shekaru 34 ta fadada kasarta ta zama babbar kasa mai girma da fadin gaske.

Sarauniya Amina ta ba da umarni an gina katangun kariya a duk sansanin sojoji. Daga baya garuruwan da ke wurin katangun sun samu cigaba da bunkasa kuma har yau wasu daga cikinsu su na nan su na cigaba da kasancewa ana kuma kiransu da Katangun Amina.

Tarihin gwagwarmayar rayuwar Emmeline Pankhurst, ‘yar gwagwarmaya wacce ta yi fafutukar kare ‘yanci da kuma hakkokin mata a kasar Birtaniya wacce ta rayuwa a tsakanin shekarun (1858 zuwa 1928).

An haifi Emmeline Goulden Pankhurst a birnin Manchester na kasar Ingila a ranar 14 ko 15 ga watan Yuli, 1858. Bayan da ta taso, Emmeline ta yi karatunta a kasar Faransa. Mahaifanta gaba daya ‘yan siyasa ne, kuma mutane ne masu ra’ayi da gwagwarmayar nemowa mata ‘yanci da damar yin zaBe a kasar Ingila. Tun ta na ‘yar shekaru (14) da haihuwa a duniya mahaifiyarta ta taBa zuwa taron tattauna nemawa mata ‘yancin yin zaBe da ita.

A shekarar 1903, Emmeline ta kafa wata kungiyar siyasa ta mata zalla mai suna (Women’s Social and Political Union), kan nemowa mata ‘yanci da damar kada kuri’a a zaBe, wanda kuma a sanadiyyar wannan gwagwarmaya tata an sha kama ta a lokuta daban-daban ana tsare ta a gidan kurkuku. Sannan kuma a sanadiyyar wannan gwagwarmaya tata, majalissar Birtaniya ta samar da takaitacciyar dokar ba wa mata damar kada kuri’a a shekarar (1918)

Emmeline ta fada harkokin siyasa bayan da mijinta ya nemi zama dan majalissa wanda bai kai ga yin nasara ba, a wannan lokaci ta yi wa mijinta yakin neman zaBe inda ta kasance ta na hada gangamin taron siyasa a gidanta.

A shekarar 1905 ‘yar Emmeline mai suna Christabel da kuma wata memba a kungiyar WSPU mai suna Annie Kenny sun shirya wani taro na musamman domin duban jam’iyyar Liberal ko za ta goyi bayan ba wa mata damar yin zaBe. Amma bayan arangama da su ka yi da jami’an tsaro na ‘yan sanda sai aka kame mata masu yawa daga cikin ‘yan fafutukar. Wannan kamu ne kuma ya karawa Emmeline karfin gwiwar cigaba da karawa kungiyarta karfi domin cigaba da gwagwarmayar nemawa mata ‘yancin yin zaBe.

A shekarar 1910 an dakile samar zartar da dokar ba wa mata ‘yancin yin zaBe, inda kuma mata da dama su ka shiga yajin cin abinci a cikin gidan kaso ciki har da Emmeline sannan kuma a shekarar 1913 aka ba da damar fitar da fursunoni masu fama da rashin lafiya tare da dawo da su bayan sun warke daga bisani kuma aka sake su bayan yajin cin abinci. Inda a shekarar 1914 Emmeline ta ziyarci kasar Amurka domin gabatar da jawabi.

A lokacin yakin duniya na daya Emmeline ta karfafi gwiwar mata wajen shiga yakin, kamar yadda ta ke cewa “mun zo wannan wuri ba wai don mun kasance masu karya doka ba, sai domin mu kasance masu tsara doka”.

Wannan gudunmawa da mata su ka bayar a yakin duniya na daya, shi ne ya ja hankalin gwamnatin Birtaniya ta zartar musu da takaitacciyar dokar da ta ba su damar yin zaBe ga mata ‘yan shekaru 30 kawai inda daga bisani kuma aka sake basu cikakkiyar dama da kuma damar tsayawa takara a zaBe su a matsayin ‘yan majalissun dokoki na Birtaniya.

Princess Diana wacce ta rayu a tsakanin shekarun (1961–1997), matar da ta yi kaurin suna ta kuma shahara a kasar Birtaniya da Duniya gaba daya kan ayyukan jin kai da taimakon yara kanana da al’umma gaba daya.

An haifi Diana a yankin Sandringham na kasar Ingila a ranar 1 ga watan Yuli, 1961. Ta fara karatunta a makarantar Riddlesworth Hall, daga nan ta wuce zuwa makarantar West Health. Princess Diana ta kasance ma’abociyar son kade-kade da raye-raye, ta samu lakabin Lady Diana Spencer bayan da mahaifinta ya gadar mata da lakabin a shekarar 1975.

Princess Diana ta kasance mai matukar kaunar yara, wanda hakan ne ma ya sanya bayan da ta kammala karatu a makarantar Alpin Bidemanette a kasar Siwizland, ta wuce zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya ta fara aiki da yara, sannu a hankali ta zamto mai hidima da taimakon yara a masarautar Ingila.

Princess Diana ta rasu da sanyin safiyar ranar 31 ga watan Ogas na shekarar 1997 a asibitin birnin Faris na kasar Faransa a sanadiyyar hadarin mota biyo bayan jikkatar da ta samu a ya yin hatsarin. Ta rasu ta na da kimanin shekaru 36 da haihuwa a Duniya.

Mutuwar Princess Diana ya yi matukar jijjiga al’umma a duk duniya, saboda dumbin ayyukan da ta ke yi na taimako da jin kan mutane.

A cikin jawabin jimamin rasuwar da ta gabatar a gidan talabijin, sarauniyar Ingila, Kueen Elizabeth ta II ta bayyana alhininta da cewa “babu wani mutum da ya san Diana da zai iya mantawa da ita. Miliyoyin al’ummar da ba su taba ganinta a zahiri ba, amma su na jin labarinta ba za su taBa mantawa da ita ba. Rayuwarta abar koyi ce ga sauran al’umma”. Inji Sarauniyar Ingila.

Bayan rasuwar Diana, an yi mata lakabi da “People’s Princess”, wato ma’ana (Sarauniyar Al’umma), saboda dumbin ayyukan alkhairin da ta yi na taimakon al’umma wanda kuma ya game duniya gaba daya a lokacin rayuwarta.

A wani rahoton bincike da aka fitar, tsakanin Maza da Mata su waye su ka fi cancanta su shugabanci Al’umma a tsarin shugabancin Siyasa ?

Idan mu ka yi nazarin wadanda mata da dumbin gudunmawar da su ka bayar ga al’umma za mu fahimci cewa ba shakka mata sun cancanci samun kowacce irin kujerar siyasa. Kuma ko da a sakamakon wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna cewar kashi shida (6%) na mutane (2,250) da aka ji ra’ayinsu sun bayyana cewa mata sun fi cancantar su zama shugabannin siyasa fiye da maza.

Sannan mutum daya cikin mutane biyar, kashi (21%) sun bayyana cewa maza sun fi mata cancantar zama shugabannin siyasa. A ra’ayi na bai daya kuma, kaso sittin da tara (69%) sun bayyana cewa babu bambancin kwaliti ta fuskar cancantar shugabancin siyasa a tsakanin maza da mata, gaba daya kwalatinsu daya ne maza ba su fi mata ba, mata ma ba su fi maza ba. Ba shakka mata sun yi an ga irin kokarinsu kuma an tabbatar da za su iya, kamar yadda mu ke ganin kokarin Hajiya Maryam Shetty a wannan zamani a Nijeriya.

Hajiya Maryam Shettima wacce aka fi sani da (Maryam Shetty) jajirtaccjyar ‘yar siyasa ce, maca ce mai kamar maza, shahararriyar ‘yar gwagwarmaya wacce ta yi fice akan temakon al’umma da kokarin sanya kwarin gwiwa da kishin kasa a cikin zukatan ‘yan Nijeriya.

A fannin ilimi kuwa, (Maryam Shetty) ta yi fafutukar neman ilimi tun daga tushe a fannoni daban-daban na ilimi inda ta kai ga samun nasarar kammala karatun digirin-digirgir a (Jami’ar East London) a kasar Ingila. Ta samu kwarewa ta kololuwa a fannin kula da lafiyar mutanen da su ka samu raunuka (Physiotherapy). Ta yi aiki da tawagar kwararru masu kula da lafiyar ‘yan wasa na tawagar ‘yan wasa Olamfic na kasar Ingila tare da gogagge, kana babba wanda ya taBa rike kambun kwarewa na duniya Jamaica’s Usain Bolt.

Hajiya Maryam ta kuma samu takardar shaida zama jami’a mai wayar da kan al’umma dangane da zaman lafiya da kaucewa tarzoma bisa turbar Dakta Martin Luther King Jr daga Jami’ar Emory ta kasar Amurka. Ta kuma samu nasarar lashe gasa da takardar shaida akan tsare-tsaren ayyukan gwamnati a karni na 21  daga jami’ar Birginia. Kuma kwararriya ce masaniya akan harkar yanar gizo da na’ura mai kwakwalwa.

Hajiya Maryam ta na kuma da gogewar aiki da asibitoci da cibiyoyin samar da cigaba na duniya shirin lafiya na gidauniyar UKAID da kuma asibitin fadar shugaban kasa da tsarin kula da lafiyar yara.

Hajiya Shetty ta kuma gudanar da ayyuka da dama na jinkai da temakon al’umma da cigaban kasa. Ta jagoranci aikin sabunta makarantu a Jihar Kano a karkashin manhajar tallafi ta (#GibingBack initiatibe).

A saboda himma da kwazonta na kishin kasa, Hajiya Shatty ta samu damar wakiltar Nijeriya a zauren majalissar dinkin duniya a karkashin kwamitin daidaito da adalci gami da yaki da cin hanci da rashawa. Sannan kuma a siyasance an saka ta a kwamitocin yakin neman zaBe na shugaban kasa a shekarar 2019. Dadi da kari, memba ce a kungiyar matasan jam’iyyar APC na kasa.

Hajiya Maryam Shetty, yanzu haka ta na da kungiyar da ta samar da kanta mai suna mun yi imani (#Webliebe) domin kokarin ganin ta sanyawa ‘yan kasa kishin kasarsu da fatan samar da shugabanci nagari da ‘yan kasa nagari da dabbaka zaman lafiya da hadin kai da temakon al’umma musamman matasa da raunana tare da sanyawa mutane kwarin gwiwa su ji cewar za su iya zama nagartattu manyan mutane a wannan kasa ta fannoni daban-daban. A saboda wannan himma tata ta kishin kasa da cigaban al’umma mutane da dama su ke kiranta da suna “Sarauniyar Arewa” (North’s Princess).

Exit mobile version