Connect with us

LABARAI

Dakta Shu’aibu Hassan Ya Bayar Da Shawarwari Kan Ayyana Ranar Hausa Ta Duniya

Published

on

Dakta Shu’aibu HassanMalami ne a Sashin Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka Na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yi tskaci dangane da ayyana ranara Hausa ta duniya,wanda ya ce,
duk da cewar wannan ba ayyanawace ta hukuma ba. To amma duk da haka wannan ba za a ce sun yi azarbabi ba, wani hobbasa ne da suka yi, yanzu sarkin Hausa na Turai yana da sarauta a birnin Paris, a Jamus duk ya karade kasashen Turai, a Jamus akwai kaza din Hausa, gari kaza akwai kaza din Hausa to yanzu ne aka fara insha ‘Allahu nan gaba shi ne zai nuna mana yaushe ne, to amma shawarar ita ce wadanda suka yi wannan ayyanawar ya kamata su tallala ayyanawar da ranar ga jami’o’i, idan suka kai ga nan ya samu karbuwa, su jami’o’i din za su rika la’akari da wadannan ranakun.
sannan dalibai masu nazari, a kowace jami’a ka je, nan jami’ar Ahmadu Bello muna da kungiyar habaka Hausa, in ka je jami’ar Bayero suna da irin wannan kungiyar in ka je jami’ar Usman Dan Fodio suna da irin wannan kungiyar, in ka je jami’ar jihar Kaduna suna da irin wannan kungiyar in ka je jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adua Katsina suna da irin wannan da ire-iren wadannan jami’o’in da sauransu.
To su daliban idan aka tallata masu sula sa wannan abun cikin tsarin kungiyoyinsu na habaka wannan harshen, to duk in ranar ta zagayo za su yi kokarin shigo da wani abu, za su shigo da ‘yan jarida a shirin da suka yi kuma za su shigo da malamansu, saboda haka a shirin da suka yi kuma za su shigo da malamansu za su rika shigowa ciki, to a hankali-hankali sai ka ga cewa abu ya karbu, duk Arewa jahohi sun farka idan ranar ta zagayo, jami’o’in da suke nazarin wannan harshe a kasashen turai sai ka ji kamar wasa ne abin ya fara. Amma a yanzu din wannan ayyanawa kp dabbakawa tana jira, jaririya ce, gaskiya ba a san ta ba.
Gaskiya shawarar da zan ba wadanda suka yi kokarin dabbaka wannan rana da ware ta cewa ranar Hausa to ya kyau tukunna da farko su yi dogon bayani a jarida sannan me ya sa suka ware wannan ranar? Wani abu ne muhimmi da ya shafi harshen Hausa da suka dabbaka wannan ranar? To irin wadannan abubuwan shine za ka ga a hankali a hankali ya samu karbuwa ga su masu nazarin harshen, ya samu karbuwa ga daliban harshen, da sauransu wanda za ka ga to a hankali a hankali an cim ma nasara.
To Allah shi gafarta malam, daga cikin bayananka ka yi bayanin cewa ya kamata su tallata ta zuwa ga jami’o’i, wace hanya za su bi wajen tallan wannan rana ga malaman jamu’o’i ko kuma daliban jami’o’i?
Masha Allah ziyara, na farko in har ba mutum daya bane, mutane ne da dama suka hadu suka ga ya kamata su yi wannan abun, sai su dau nauyin da alhakin ziyara, in a Kano suke nan jami’ar Bayero, za su je jami’a. Su je wannan sashen da kuma cibiyar nazarin harsuna da kuma adabin Afirka Centre for Nigerian Languages duk irin wadannan guraren a rubuce dama za su kai, idan sun kai a rubuce sai su bayyana cewa za mu biyo baya da ziyara mu tattauna da shugaban sashe da manyan malaman da ke wannan sashe, farfesoshi akwai su da dama, sannan sai su nemi izini daga sashe cewa suna so su gana da dalubai, daluban nan suna da kungiyar nan ta masu nazari,kamar nan jami’ar Ahmadu Bello sunanta kungiyar Habaka Hausa, to shikenan sai su nemi wannan izinin, za a iya basu lokaci da ranar da za su zo sun tallata sa a taru a ce gashi-gashi su tallata ta, su nuna me ya sa suka zabi wannn ranar da kuma muhimmancin wannan ranar a dabbakata cewa ta zama ranar Hausa ta duniya, idan suka yi a Bayero suka zo nan jami’ar Ahmadu Bello Zariya, suka tafi Usmanu Dan Fodio suka dai kewaya har kwalejojin da ake nazari a Nijeriya kuma nazarin Hausan nan a matakin NCE har kudancin Nijeriya ana yi, to idan aka yi wannan to jami’a ta san da zamansu, kwalejoji sun san da zaman wannan ranar sannan manazarta da malamai sun sani dalubai sun sani, to a haka-a haka, ana ganin cewa za su tallata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: