‘Dalibai 880 Cikin 1,561 Suka Ci Jarrabawar Karshe Ta Karatun Lauya’

Karatun Lauya

Makarantar  lauyoyi ta Nijeriya ta bayyana cewa cikin dalibai guda 1,561 wadanda suka rubuta jarraba a watan Disamba, dalibai guda 880 suka samu nasarar cin jarrabawa. Shugaban makarantar, Farfesa Isa Ciroma shi ya bayyana haka a ranar Talata a garin Abuja wajen yaye sababbin lauyoyin. Ya bayyana cewa sababbin lauyoyin sun cika dukkan ka’idojin da karatun lauya yake bukata.

 

“Ina mai farin cikin tabbatar da cewa sun cika dukkan ka’idojin da dabi’u wajen samun horo. Haka kuma sun yi kokarin nuna da’ a da kyakkyawan dabi’u wajen samun kwarewa daga hannunmu.

 

“Kwamitin tattancewa na kungiyarmu sun dauki shaidar kowani dalibi da kyau kafin su tsinci kansu na zama lauyoyi,” in ji shi.

 

Ciroma ya kara da cewa makarantar ta fara gudanar da tsarin karatu na share fage ga daliban jami’ar karatu daga gida ta kasa (NOUN).

 

“An dai fara gudanar da wannan kos din ne tun daga ranar 28 ga watan Yuni a shalkwatar makarantar lauyoyi ta Nijeriya da ke Bwari cikin garin Abuja. Muna godiya ga dukkan mambobin kungiyarmu wadanda suka ba mu goyan baya,” in ji shi.

 

Shugaban kwamitin lauyoyi, Justice Olabode Rhodes-Bibour ya taya murna ga sababbin lauyoyin tare da kira a gare su da su ci gaba da bin dokokin aikinsu a ko wani lokaci.

 

“A matsayinka na lauya wanda ka kasance jami’in a kotu, bai kamata a yi wani aikin da zai saba wa doka wanda har zai iya shafar aikinka.

 

“Bin doka ya zama wajibi ga duk wani lauya. Aiki ne da zai iya shafar rayuwar mutane.

 

“Domin haka, ya zama wajibi ku dunga bin dokokin aikinku a kowani lokaci kuma a duk inda kuma tsinci kanku,” in ji shi.

 

Ya kara da cewa kwamitin horar da lauyoyi a ko da yaushe tana da dokokin da ta shiffida ga kowani dalibi da ke kokarin kwarewa ga aikin lauya. Rhodes-Bibour ya bayyana cewa kwamitin zai  gudanar da adalci ba tare da bayar da kofar yin cuta ba. Ya ce a tsakanin watan Junairu zuwa watan Yuni, kwamitin ya hukunta lauyoyi guda shida, sannan ya dakatar da wasu na tsawan shekaru biyu zuwa hudu, yayin da ya kori dauya guda daya a tsakanin wannan lokaci. Rhodes-Bibour ya shawarci daliban da su ci gaba da fadada ilimisu a wannan fannin na karatun lauya domin su fahimci dokin kasa da kasa.

Exit mobile version