Daliban ABU 6 Sun Lashe Gasar Fasahar Adana Bayanai Ta Huawei Ta Duniya

Huawei

Daga Sulaiman Ibrahim,

Dalibai uku na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, sun sami babbar kyauta ta duniya a cikin gasar fasahar kimiyya ta kamfanin Huawei na 2019-2020.

Farfesa Kabir Bala, Mataimakin Shugaban Jami’ar ne ya bayyana hakan a yayin bikin bayar da lambar yabo ta ICT ta shekarar 2019/2020 ta Huawei Nigeria da kuma kaddamar da bikin tayasu murna a ranar Laraba..

Bala ya ce gasar Huawei ta 2019/2020 ta na dauke da dalibai masu son cin gasar sun kai 150,000 daga kwalejoji da jami’o’i sama da 2,000 a kasashe sama da 82.

“Dalibai shida na ABU suka halarci gasar kuma uku daga cikinsu: Hamza Atabor, Emmanuel Abba da Hamza Beira, sun sami kyautar farko a Network Track Global.

“Mustapha Jimoh, Dahir Muhammad-Dahir da Abdullahi Khalifa Muhammad sun sami babbar kyauta a cikin kimiyyar AI da Cloud (gajimare), ” in ji shi.

Ya kara da cewa dangantaka tsakanin ABU da Huawei Technologies ta fara ne a watan Agusta 2018.

Mataimakin shugaban jami’ar ya kara da cewa, Huawei ta tuntubi jami’ar ne don hadin gwiwa a kan tsarin kamfanin Huawei  na basirar (HAINA) da sauran shirye-shiryen CSR.

“Muna farin ciki da sakamakon da muka samu yanzun; a karkashin shirin ABU-HAINA sama da mutun  1,000 sun Shiga tsarin sannan mun samu takaddun shaida daban daban 450, ” in ji shi.

Misis Melissa Chen, Darakta, Huawei Technologies Nigeria, ta ce sama da daliban Nijeriya 22,000 ne suka yi rajista a Huawei ICT Competition na 2019/2020.

Chen, wanda Mista Star Shi, Mataimakin Darakta, ta  wakilta, ta ce, wadanan daiban 1,000 sun fafata a wasan karshe na kasa a watan Disambar 2019.

Chen ta kara da cewa dalibai 15 daga ABU Zariya, da jami’ar Ibadan da Fatakwal sun wakilci Nijeriya a gasar karshe.

“Daliban sun samu kyakkyawan sakamako a fafatawar karshe  kuma an ba su dama sun wakilci makarantunsu da kasarsu Nijeriya a fafatawar karshe ta duniya,” in ji ta.

Mista Igwe Keneth, Huawei, Manajan Ci gaban Tsarin Yan Adam na ICT, ya ce kamfanin ya yi bikin daliban daga Najeriya wadanda suka samu kyakkyawan sakamako a Gasar Huawei ICT na 2020.

“Mun zo nan ne a yau don ba su lambar yabo da kuma yin biki tare da su sannan kuma mun kaddamar da Gasar ICT ta Huawei ta 2021-2022 don dalibai.

“A cikin gasar ta 2021-2022 akwai bangaren cloud track, bangaren sadarwar zamani da kuma bangaren kirkire-kirkire inda dalibai za su zo da sabbin dabaru tare da gabatar da shi yayin gasar, ” in ji Kenneth.

Manajan ya ce, an fara gasar ta ICT ta Huawei ne don bunkasa fasahar na’urar sadarwa ta zamani.

Ya kara da cewa gasar ta samar da tsarin da ya dace ga dalibai don samun ilimi da gogewa don gina baiwar haliita ta mutum ga tsarin ICT.

Exit mobile version