Sabo Ahmad" />

Daliban Hausa Na jami’ar Ahmadu Bello Sun Koka

Wani dalibi mai suna Zakariyya Sadik Jibril, daga Sahin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka, da ke nazarin harshen Hausa a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya koka, a madadin sauran dalibai masu nazarin harshen Hausa, kan yadda ake nuna bambanci tsakaninsu da sauran dalibai masu nazarin harshen Larabaci da Faranci wajen tura su wasu garuruwa da za su taimaka musu wajen kara gogewa a harshen da suke nazari. 

Zakariyya ya mika wannan kokken nasa ne a wajen taron da Sashin kula da tsare-tsaren karutu na jami’ar ya shirya don kaddamar da wakilan dalibai da za su kula da ingancin karatu.

A koken da ya gabatar, ya nuna yadda ake nuna bambanci tsakanin daliban Hausa da sauran dalibai masu nazarin harshen Hausa da masu nazarin sauran harsuna guda biyu da ke wannan Sashi, inda ake tura masu nazarin harshen Larabci Gamborin Gala domin da ke jihar Borno, domin su kara kwarewa a kan harshen Larabci, yayin da su kuma abokan karatunsu na Faransanci ake tura su Legas, domin su kara gogewa a wannan harshe da suke koyo, amma su kuwa daliban harshen Hausa babu inda ake tura su, duk da cewa, su ma za su iya zuwa Nijar domin samun kwarewa da ganin kayan tarihi.

Bayan wannan kuma, Zakariyya, ya bukaci hukumar jami’a ta farfado musu da dakin gwajin harsuna domin su samu damar ganin yadda gabobin furici ke aiki yayin da dan’adam ke furta kawoyin sauti, wanada hakan zai taimaka musu wajen kara fahimtar yadda furicin ke gudana.       

Wannan koke ya boyo bayan damar da aka bai wa daliban ne na su bayyana matsalolin da ke kawo musu tarnaki wajen karatunsu. 

A wannan taron dai za a iya cewa, allura ta tono garma, domin dalibai sun amayo da dukkan matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya wajen gudanar da karatun nasu.

Dalibai da dama daga sassa daban-daban ne suka bayyana matsalolinsu, kan abin da ya shafi muhalli da lafiya da jarrabawa da kuma matsaloli tasaninsu da malamansu.

Ta fuskar muhalli wasu daliban sun nuna yadda idan wani abu ya lalace musamman abin da ya shafi wutar lantarki ake cewa, sai sun hada kudi sannan a gyara musu. Haka kuma daliban sun koka kan yadda suke samun jinkiri yayin da suka je asibitin jami’ar don neman magani ko da kuwa sun je da matsananciyar damuwa ne. 

Tun da farko a nasa jawabin shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, wanda shugaban Sashin kula da tsare-tsaren karatun jami’ar Farfesa Muhammad Ishaku ya wakilta, ya nuna cewa, babban dalilin zakulo wadannan daliban da za su kula da ingancin karatu a jami’ar shi ne, a tabbatar da cewa, jami’ar Ahmadu Bello ta ci gaba da rike matsayinta na samar da kwarraun dalibai, sannan kuma daliban su gudanar da karatunsu cikin walwala yadda za su fahimci abin da ake koya musu.

Sannan kuma ya nuna cewa, dukkan malamin da yake yi wa aikinsa rikon sakainar kashi, wakilan daliban su sanar da hukumar makarantar, domin magance wannan matsala. Haka dai dalibai suka yi ta jero matsaloli daban-daban wadan shugaban ya tabbatar musu da cewa, za su dauki matakin magance su.

Exit mobile version