Daliban Jami’a 100 Sun Samu Horo Kan Fasahar Hasken Rana

Fasaha

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnatin Tarayya ta horar da dalibai 100 na Jami’ar Tarayya ta Aled Ekwueme, Ndufu-Alike kan sarrafa Ingancin makamashin hasken rana (Solar Photoboltaic Systems).

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an zakulo daliban ne daga fannin Kimiyya, Fasaha, Injiniya da Lissafi.

An horar da su ne a karkashin Shirin Ilimi na karfafawa na Gwamnatin Tarayya wanda Ma’aikatar Wutar Lantarki ke kula da shirin ta hanyar Hukumar Wutar Lantarki ta karkara (REA).

Da yake jawabi yayin gabatar da takardun shaida ga mahalarta taron a ranar Litinin, Jami’in Horarwa na Asteben Renewable Energy Academy, Mista Isaac Negedu, ya bayyana horon a matsayin wajibi kuma ci gaban da ake maraba dashi.

Gwamnatin Tarayya ta amsa makarantar horawa ta Asteben Renewable Energy don gudanar da shirin.

“Horon wani bangare ne na kwangilolin da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da makarantar da ta gina bangaren samar da wutar lantarki ta hasken rana a jami’ar,” in ji shi.

Ya ce wadanda aka horar sun samu horo a muhimman fannoni guda uku, wadanda suka hada da karatuttukan rubuce-rubuce, gudanar da abinda suka koya a bayyane da ziyartar wuraren da aka tsara wutar hasken rana.

Ya ce an shirya horon ne domin karfafawa daliban gwiwa su zama masu dogaro da kai, masu amsar aiki da daukar ma’aikata bayan kammala karatun.

Negedu ya ci gaba da cewa, horon wanda aka yi shi a rukuni-rukuni, zai samar wa da daliban rayuwa mai kyau nan gaba.

“Kasuwancin yana dorewa kuma yana samun riba,” in ji shi.

A wani jawabi, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sunday Elom, ya ce dumamar yanayi na fuskantar kalubale a duniya, wanda sauyin yanayi ke haifar da shi.

Ya ce ta hanyar makamashi mai sabuntawa (renewable energy), ana iya rage hadarin sauyin yanayi.

Elom, wanda ya samu wakilcin darakta a wajen taron, ya godewa Gwamnatin Tarayya bisa zabar jami’ar don cin gajiyar shirin.

Wani dalibi mai digiri 500 na injiniya, Michael Chukwu, wanda ya halarci horon, ya bayyana binciken makamashi a matsayin mafi mahimmancin aikin da ya dace dalibai su koya na SPS.

“Tare da ilimin, zaku iya tantance nau’in, inberter da batura da za a yi amfani da su wajen shigar da tsarin hasken rana.

“Ina gode wa mahukuntan jami’ar da suka ba mu dama.

Na yi alkawarin yin amfani da ilimin da aka bamu don inganta al’umma.” In ji shi.

Exit mobile version