Daliban Jami’a Su Yi Hattara Don Kar Su Bar Wa ‘Ya’yan Da Za Su Haifa Mummunan Tarihi – Neeshar Jay

Neeshar Jay

 

A kullu yaumin, burin wannan shafi shi ne kawo wa masu karatu hazikan dalibai a matakan karatu daban-daban domin su bayyana irin basirar da Alah ya yi musu a hanyar da suka hau ta neman ilimi. A kan hakan, a wannan makon ma shafin ya kawo muku bakuwar daliba sabuwa fil a leda inda muka tattauna da ita game da rayuwarta da ta shafi makaranta. Bakuwar tamu ta yi bayanai masu gamsarwa kan abubuwan da suka shafi tarihin rayuwarta, da makarantun da ta yi a baya da kuma wacce take ciki a halin yanzu. Ba ta tsaya a nan ba, har ila yau ta kuma yi tsokaci a kan yanayin rayuwar jami’a ta dalibai daban-daban, sannan ta dora da yi wa masu nuna halin rashin kirki a jami’a bulala domin su gyara halayyarsu. Duk wannan da ma sauran wasu muhimman bayanai za ku ji a cikin hirar, kawai ku karanta har zuwa karshe.

 

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi…

Sunana Aysha Murtala amma an fi sanina da Neeshar Jay.

 

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

Eh toh ni ‘yar asalin jihar Kebbi ce, gaba daya ni da family (iyayena) a can muke zama. Na yi Nazare a  Raudah da na kai aji daya na Firamare na koma Makarantar Yasima ita ma dai ina aji uku a Firamaren na fita na koma Makrantar Brilliance inda a can na gama na fara boarding school (makarantar kwana) a Zariya har Allah ya sa na kai aji shida, yanzu kuma Ina karatun nursing (nazarin jinyar marasa lafiya) na kusa kammalawa.

 

Da kyau! Bari mu koma kan abin da ya shafi karatunki, kafin kammala makarantar sakandare dinki shin wacce makaranta kike da burin shiga?

Gaskiya na yi burin shiga wata makaranta a Sudan Afhad Unibersity for women (Jami’ar Afhad ta Mata Zalla da ke Sudan), gaskiya ita na yi ta burin shiga.

 

Ko za ki iya fada wa masu karatu dalilin fasa zuwanki waccan makarantar da kike da burin shiga?

Toh Babana ne daga baya ya ce a’a na yi hakuri tunda ba wani dan’uwa da yake zama a cen kuma ga Mommy (Mama) ta ce ita ba za ta je ba ta fasa saboda aikin ta.

 

Yanzu kina wacce makarantar ke nan?

Kebbi state Unibersity of science and technology (Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi)

 

Da kyau! Wacce irin gwagwar maya kika sha wajen neman gurbin shiga makaranta, wato admission?

Gaskiya ban sha wahala ba kuma abunda na yi applying (nema) shi aka bani.

 

Masha Allah, ko za ki iya tuna sabbin abubuwan da kika fara cin karo da su tun daga farkon da kika fara cike form da rajista ta shiga babbar makaranta?

Gaskiya abunda na ci karo da shi ne kyauta da Abbana yayi min ta babbar waya da laptop tun da ya ji labarin na cike form zan shiga Unibersity (jami’a) shike nan komai na ce toh za a yi min tunda suna ganin makaranta zan je. Sannan gaskiya yanda na ga suna yi ba kamar makaramtar sakandare ba, komai sun dauke shi da muhimmanci sai na fara tunanin anya zan iya kuwa.

 

Ya batun zirga-zirga wajen cike-ciken takaddu da sauran su ya kasance kafin shigarki jami’a?

Gaskiya kam na sha wahala a wannan fannin dan sai na je a ce na koma bayan kwana biyu na dawo, haka dai na yi ta yawo karshe har na samu na yi screening (tantancewa) gaba daya muka tsaya jiran admission (gurbin shiga makaranta).

 

Bayan shigarki jami’a ko za ki iya tuna mutanen da kika fara cin karo da su?

A mata a kwai Safiyya, Fatima sai Fareeda.

Ya farkon shigarki aji ya kasance?

Na ji dadi sosai dan ranar ina ta zumudi dan haka tunda na yi sallar asuba ban kwanta ba, na shirya da misalin karfe 7:30am na safe Ina cikin aji, kuma mun yi lecture (lacca) mai dadi.

 

Ya darasin ranar ya kasance?

Ya yi dadi dan introduction (gabatarwa) kawai muka yi dan haka ya sa bamu gaji ba.

 

Ranar da kika fara zama a aji ya zaman naki ya kasance tun daga farkon shigar ku har zuwa lokacin tashi?

Gaskiya ni ban ji komai ba tun da muka shiga har muka fito, gaba daya ban ji wani canji ba.

Da kyua! Ko za ki iya tuna kusa da wadda kika fara zama a farkon shigarki aji?

A kusa da safiyya Muhammad Yauri.

 

Wanne darasi aka fara yi muku?

‘Physics 101’

 

Ya kika ji darasin a lokacin, shin ya ba ki wuya ko kuwa ya abun yake?

Gaskiya bai bani wuya ba dan na ji dadinsa sosai.

 

Bayan wadanda kika hadu da su a farkon zuwanki, da su wa kika fara kawance kuma mene ne musabbabin kawancen ku?

Toh da wata Amina sai Zaynab kuma abunda ya sa room (daki) din mu daya da su bayan Safiyya kuma suna da son karatu shi ya sa kullum muna tare.

 

Da kyau! Ya zirga-zirgar zuwa makarantar ya kasance?

A hostel (masaukin dalibai) nake zama.

 

In na fahimce ki ba kya shan wata wahala na zirga zirga Kenan?

Eh ba na sha, daga hostel (masaukin dalibai) sai hall (ajin karatu).

 

Gaskiya ne, me ya fara ba ki tsoro game da makarantar jami’a?

Yanda wasu ‘yan mata ke biye ma samari suna holewarsu.

 

Ya yana yin zamantakewar rayuwar jami’a take, kamar yana yin shigarsu da kuma mu’amular maza da mata na makarantar?

Toh gaskiya kowa da kalar shigarsa da yake yi, wasu suna saka hijab su yi shiga ta kamala wasu kuma za su saka gyale a takaice dai kowa da yanda yake yi. Wasu mu’amalar su da maza a kan karatu ne wasu akasin haka.

 

Toh ya batun da ake cewa wasu matan suna yin shiga ta mutunci daga gida yayin da suka baro gidansu sai su canja shigar wasu ma sukan saka hijab akai da zarar sun isa makarantar sai su cire me za ki ce a kan hakan?

Eh akwai wadanda iyayen su basa barinsu sun saka matsattsun kaya amma idan suka zo makaranta sai su canza saboda suna ganin kawayensu na yi suma sai abun ya bi ra’ayin su suma su saka.

 

Kin taba cin karo da kawaye masu irin haka?

Eh amma gaskiya ba na biye wa shirmensu.

 

Ya kike ji cikin zuciyarki a duk lokacin da kika ci karo da masu irin wannan hali?

Gaskiya ina tausayawa rayuwar su musamman wadanda a gidan su ba a san suna yi ba.

 

Wacce shawara za ki bawa masu irin halin?

Shawarata a nan ita ce su ji tsoron Allah su daina saboda suna cutar kansu da iyayensu ba su san kuma irin yaran da za su haifa nan gaba ba.

 

Gaskiya ne, wanne darasi ne ya fi baki wuya kuma me ya sa yake baki wuya?

‘Chemistry’ saboda wallahi tun a sakandare ba na sonshi.

 

Wanne darasi kika fi so kuma me ya sa?

‘Biology’ saboda Ina ganewa sosai kuma lecturer din ba shida tsanani.

 

Wacce daliba ce tafi burgeki a aji, kuma me ya sa take burgeki?

Hajara Badare saboda ba ta wasa da karatu.

 

A maza fa, wanne dalibi ne ya fi burgeki kuma me ya sa?

Saddik Bagudu saboda ba ruwanshi da kula ‘yan Mata, abun da ya kawo shi kawai yake yi.

 

Bangaren malamai fa, wanne malami ne ya fi burgeki kuma me ya sa?

Nafi son Malamin da ke koya mana Biology, saboda ba shida wulakanci kamar sauran.

 

Mene ne burinki na gaba game da karatunki?

Burina shi ne idan na gama na samu aiki a asibiti.

 

Da kyau! Zaki ji wasu mazan na cewa ba zasu auri macen da tayi jami’a ba, me za ki ce a kan hakan?

Gaskiya ba yi bane su suna kallon kamar duka matan aka taru aka zama daya toh gaskiya wannan ba shawara ba ce ka ce ba za ka auri ‘yar jami’a ba.

 

Mene ne ra’ayinki game da ci gaban karatun ‘ya mace?

Gaskiya ya kawo cigaba da yawa kin ga yanzu bai kamata a ce namiji ne zai karbar ma mace haihuwa ba kuma Alhamdulillah an samu cigaba yanzu kai ya waye muna da likitoci mata da suka yi karatu a kan fannin abun da ya shafi matsalolin lafiya na ‘ya mace. Gaskiya ra’ayina a nan shi ne iyaye da mazaje su dinga barin mata suna zuwa makaranta dan suna matukar taimaka ma al’umma gaba daya.

 

Ya za ki bambanta wa masu karatu tsakanin macen da ta yi karatun gaba da sakandare da kuma wadda ba ta yi ba?

A kwai banbanci sosai ma kuwa ita wacce ta tsaya iya sakandare ba ta da life edperience (hikima da basirar rayuwa) kamar na wacce ta yi jami’a kuma ko a gurin ilimi ba daya ba kuma ta fi sanin rayuwa a kan mai takardar shaidar karatun sakandare.

 

A naki hangen wanne amfani karatun ‘ya mace yake da shi ga al’umma?

Yana da amfani da yawa idan muka dakko bangaren aikin asibiti bai kamata a ce idan mace ba ta da lafiya wai namiji ne zai duba ta maybe (watakila) ma matar aure ce kuma musulma to kin ga kenan ba mu da kishin addininmu.

 

Idan aka ce yau ‘yarki ta kammala makarantar Sakandare shin za ki iya barinta ta ci gaba har jami’a?

Zan barta mana da gudu ma kuwa sai ta yi karatu ita ma.

 

Bari mu koma kan soyayya shin ko akwai wanda ya taba kwanta miki cikin makarantar har kuka fara soyayya da shi?

Akwai wani Hasheem da shi muka fara soyayya.

 

Ya soyayyar ta kasance?

Alhamdulillah gaskiya ta yi dadi sosai dan ni ma kaina na yi mamakin yanda na saki jikina. Toh a hanyar zuwa na hostel (masaukin dalibai) ne na  zubar da wasu papers (takarduna) ban sani ba toh a nan ne muka hadu da shi farko sai kuma ranar ina so na yi ‘parenting hand out’ dina bayan mun hadu a cafe (shagon dab’i) ya ce na je zai kawo min, toh sai ya karba lambata dan ba a barin maza na shiga hostel dinmu, haka dai muka cigaba da mutunci sai ranar yake gaya min shi fa sona yake da na ce mishi zan yi tunani kawata ta ce kawai na yarda, bayan sati na gaya mishi na yarda.

 

Har yanzu kuna tare kenan?

A’a tun a mataki na 200 muka rabu.

 

Mene ne burinki na gaba game da makarantarki?

Burina na gama lafiya na samu good result (kyakkyawan sakamako).

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga jami’a har ma da wadanda suke ciki?

Ina basu shawara da su zama na gari su fuskanci abun da ya kaisu wato karatu dan sune manyan gobe kuma suma za su haifa da kunya yaronka ya tashi ya ji an ce babanshi ko mamanshi sun nuna dabi’u marasa kyau a makaranta, kin ga wannan mummunan tarihi ne za su bar wa ‘ya’yansu.

 

Me za ki ce ga makaranta wannan shafin na DUNIYAR MAKARANTU?

Ina musu fatan alkairi a duk inda suke.

 

Me za ki ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a?

Ina mata fatan alkairi Allah kuma ya kara daukaka.

 

Amin, ko kina da wadanda za ki gaisar?

Eh ina gaida Rabi’at SBS da kuma al’ummar duniya gaba daya.

 

Muna godiya da bamu lokacin ki da kika yi ina yi miki fatan alkhairi.

Ni ma na gode.

 

Exit mobile version