Ahmed Muhammad Dan Asabe" />

Daliban ‘Kogi Poly’ Sun Yi Zanga-zanga Bisa Kashe Dalibi

Daliban ‘Kogi Poly’

Daliban kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kogi (Kogi Poly) a jiya Laraba sun gudanar da wata zanga-zanga biyo bayan mutuwar daya daga cikin daliban kwalejin wanda wani direban mota ya bige sa a daren ranar Talata kuma ya tsere.

Daliban wadanda su ke toshe babban hanya Lokoja zuwa Abuja, sun kuma hana ababen hawa wuce wa tare da kai musu hari da kuma lalata duk wata motar data ki tsaya wa.
Wakilin LEADERSHIP A Yau ya gano cewa, dalibin, wanda a yanzu ya ke matakin karshe na HND II, motar ta bige shi ne a yayin da ya ke kokarin tsallake titi da misalin karfe takwas na daren ranan Talatar da ta gabata.
Wata majiya ta ce, direban motar wanda ya danno a guje ya buge dalibin ne amma kuma ki tsaya wa.
Hakan kuma ya harzuka daliban kwalejin ta polytechnic inda su ka fantsama titi tare da toshe babban hanyar Lokoja zuwa Abuja sannan su ka rika kona tayoyi.
Hatta yan sanda da aka turo wajen zanga zangar daliban sun gagara shawo kan lamarin duk da cewa sun rika harbi da bindigogi a sama don tauna tsakuwa, aya taji tsoro da kuma watsa wa daliban hayaki mai sa hawaye.
Mai magana da yawun kwalejin, Uwargida Uredo Omale ta tabbatar da afkuwar lamarin ga wakilimmu, inda tace a yanzu jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.
Haka shi ma jami’in yada labarai na rundunar yan sandan jihar Kogi, Mista William Aya, ya tabbatar wa wakilin jaridar LEADERSHIP A Yau faruwa lamarin.
Ya ce, lamarin ya faru ne a daren ranan talata data gabata,inda bayan faruwar lamarin sai aka gaggauta kai dalibin asibiti amma kuma Allah yayi masa rasuwa a safiyar jiya Laraba.
Mista Aya ya ce, samun labarin mutuwar dalibin ne ya harzuka daliban wadanda su ka fantsama babban hanyar Lokoja zuwa Abuja don gudanar da zanga-zanga.
Ya nanata da cewa a yanzu kam rundunar ta shawo kan lamarin ganin cewa kwamishinan yan sandan jihar Kogi, CP Ayuba Edeh ya turo wasu jami’an tsaro na yan sanda zuwa inda lamarin ta faru domin kauce wa sake barke war zanga zanga wanda daliban ka iya yi.

Exit mobile version