Ifeanyi Dike dalibi dake zangon karatu na biyu a Jami’ar Fatakwal dake jihar Ribas ya arce ne daga Rundunar Jami’an Farin Kaya ta jihar (CID). inda aka kuma sake cafko shi a karamar hukumar Barkin Ladi dake cikin jihar Filato a satin da ya gabata.
Ana zargin sa ne da yi wa wata yar uwarsa ‘yar shekara takwas fyade san nan ya kasheta, yarinyar mai suna, Chikamso Mezuwuba, ta hanyar cire wasu muhimman sassan jikin ta,
Dubun Dike ta cika ne lokacin yana kan hanyar sa zuwa jefar da gawar Chikamso, inda ‘yan Sintiri kauyen Okporo cikin karamar hukumar Obio/Akpor dake jihar suka yi arba dashi suka kama shi.
Da aka gabatar dashi a gaban manema labarai a harabar Rundunar Dike ya ce, “bayan da na rubuta bayani na da yammar ranar ta farko da aka gabatar dani, Dan Sanda Johnbosco Okoroeze dake bincika ta, ya umarce ni in shiga cikin Sel sai nayi amfani da damar wutar lantarki da aka dauke a harabar Rundinar na silale.”
Dike yace, “bayan na gudu daga Fatakwal an kara kama ni ne a jihar Filato, lokacin da na kara aikata wani lafin na satar abinci, inda jamar yankin suka kama ni suka mika ni ga ofishin ‘Yan Sanda na yakin.”
“Ya ce, yin wa ce ta ishe ni ganin na shafe kwanuka a garin banci abinci ba, kuma ga raunuka a jiki na sai na yanke shawar in nemi abinci, inda naje satar abinci, sai jama’a suka kama ni suka mikawa ‘Yan Sanda”
A cewar Dike, “a ofishin na ‘Yan Sandan nayi ta kokarin in boye kai na, amma da naji na gaji da tambaye -tambayen su, sai na basu lambar wayar tafi da gidan ka ta yaya ta, suka buga mata, inda tace masu dama Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta Ribas suna kan farauta ta, bayan an tsare ni a ofishin na ‘Yan Sandan aka sake dawo dani Ribas.”