Dalilai 4 Da Suka Sabbaba Tasgaron Dinkin Sallah Ga Telolin Kano A Bana

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Teloli a Jihar Kano sun koka kan karancin dinkin sallah da jama’a ke kawo musu, biyo bayan matsin rayuwa da ake ciki.

Telolin sun bayanna dalilai hudu da ke kara ta’azzara rashin samun aikin, ciki kuwa har da karin kudin kayan dinki, rashin kudi a hannun jama’a, dawurwuran sayar da yadi, da kuma rashin samun albashi.

A cewar wani tela Abdussalam Kabir, da ke dinki a unguwar Rijiyar Zaki, kudaden da tela yake sayen kayan dinki sun yi tashin gwauron zabi.

“A gaskiya komai ya canza, saboda tsadar kayan dinkin, samun dinki ya ragu, wasu abubuwan da ake saya a da Naira 600 yanzu ya koma N800. Mai dinka kala 4 a da da wuya yanzu ya dinka kala daya” a cewarsa.

Shi ma wani tela Kabiru Abubakar, da ke Tudun Maliki ya ce, kudaden sayen kayan aiki a bana sun nunka.

“Kudin sayen kayayyakin dinki sun karu gaskiya, wasu sun ninka kudinsu a kan yadda aka sansu” kananan kamar zare wani dan Naiea 40 ya dawo Naira 50, kuma ingancin kayan ma duk sun ragu.
“Komai da komai yadda aka san shi ya ragu a inganci ga kuma kudin sa ya karu.” in ji shi.

Telolin sun ci gaba da cewa rashin kudi na hana abokan huldarsu kawo dinki. Wani Kabiru Muhammad, ya ce masu kawo dinki sun sauya daga yadda suka saba kawowa ba kamar a baya ba.
“Idan kwastoma a da na kawo kaya kala 3, yanzun ma zai iya kawo ukun amma za kaga darajar kanyan sun ragu.

“Alalmisali a ce bara sun kawo maka shadda mai tsada wanda duk yadi zai iya kai wa Naira 2,500 zuwa Naira 3,000 yanzu sai an rage kudin.

“Sai ka ga mutum ya je ya sayo yadi, irin su Lana ko Kashmir ko irin su dan Aba don ya samu rarar kudi, wannan ragowar canjin da aka samu zai iya biyan kudin dinkin da su”
Haka zalika, Abdulsalam Muhammad ya ce yara ma da iyayensu ke dinka musu kala 4 ko 3 yanzu da wuya a yi musu kala 2 saboda ba kudin.

“Kusan dai duk wanda ya kawo dinkin ‘ya’yansa ba sama da guda biyu-biyu,” a cewar sa.

Haka zalika Telolin sun bayyana cewa mafi akasari magidanta na shiga halin dawurwura da rashin takamaimai wajen zabar mai za su dinka da iyalansu.

Wasu na tunani biyu, tsakanin dinkin da wasu al’amuran na gida wanne ne ya fi amfani. “Mafi yawa ta abinci ake ba ta sutura ba, wani gani yake mai zai yi, shin dinkin ya kamata ya yi, ko abincin yara ya kamata ya saya, ko kudin makarantar yara zai biya.

“Irin wadannan matsololin da suke faruwa shi ne yake sa muke fuskanta karancin kawo dinki”
“Amma duk da hakan mutane na yin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun yi ma kansu da iyalansu sutura,” a cewar Kabiru tela.

Haka zalika telolin sun bayyana cewa rashin biyan albashi na sanya jama’a kasa kai musu dinki, tunda galibin al’umma ‘yan albashi ne.

Gaskiya wannan lokacin ana samun karancin kayan dinki musamman ma wasu ba a biya albashi ba, wani yana jiran sai an biya, inda zai iya kasancewa sai karshe-karshen azumi za a biya, kuma lokacin wani ma zai tunanin dinkin.
Shi ma Kabiru tela cewa ya yi “Wasu rashin albashi ne da wuri, wani za ka ga gwamnatin ta ba da albashin amma ta cire wani abu daga ciki, wani lokacin ma ba a biya albashin a kan lokaci ba ko dai wasu abubuwa makamancin haka”.

Exit mobile version