Ammar Muhammad" />

Dalilai Goma Da Ke Nuna Muhimmancin Kimiyyar Sadarwa Ga Rayuwar Al’umma Yau (2)

Na Shida; idan muka dawo bangaren ilimi, kimiyyar sadarwa na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa bangaren nan. Domin a halin yanzu dalibai sun ta shi daga dogaro da abin da ake koya musu kadai a makaranta ko nace a aji, sun koma zurfafa bincike dangane da abin da suke karanta, domin ganin sun fahimci darasin fiye da yadda aka koya musu. Wannan duk ya samu ne ta fuskancin kimiyyar sadarwa da aka samu a wannan zamani. Domin a halin yanzu abin da dalibi ke da bukata shi ne wayar salula kirar zamani ko kwamfuta, sannan yana da bukatar ‘network’ mai karfi wanda zai rika amfani da shi wajen shiga Intanet da shi domin samun bayanan da za su taimaka wa karatunsa. Wannan ya nuna yadda karatu ya tashi daga aji kadai ya koma hatta a cikin daki, ko gida.

A halin yanzu ma, akwai wadansu fitattun jami’o’i masu amfani da kimiyyar sadarwa wajen ilmantar da al’umma. A cikin su ma wadansu sun samar da darussa daban-daban da dalibai ke karatu akan su ta hanyar kimiyyar sadarwa wanda kuma a karshe ake ba su shaidar kammala karatun na su kamar yadda aka bai wa wadanda suke karatu a cikin makarantar. Kuma karatun yana bai wa kowa da kowa ko da ma mutum dan kasuwa ne, ko ma’aikaci, irin wannan karatu ta hanyar kimiyyar sadarwa yana bai wa mutum ya hada karatun da aikinsa ko sana’arsa.

Yanzu ma akwai jami’a guda da ake ce ma Budaddiyar Jami’ar Nijeriya wato NOUN a takaice da zaka yi digirinka na farko da na biyu ta fasahar nan.

Kuma ba ta nan kadai ake cin moriyar wannan fasahar ba, daliban za su iya amfani da shafukan sada zumunta wajen kulla alaka tsakanin su da sauran abokan karatunsu da Malamansu. Wannna yana daya daga cikin dalilan da ke nuna muhimmancin wannan bangaren.

Na Bakwai; sannan a bangaren lafiya ma, sadarwa yana bada gudummawa wajen ci gaban wannan bangare. Domin a yanzu daga dakin ka ma za ka iya binciken wuraren kiwon lafiya da za su duba lafiyarka ba tare da ka tashi ka tafi asibiti wannan binciken ba. Wanda bayan ka kammala binciken ka daga daki, sannan kai tsaye ka nufi inda za a duba lafiyarka ba tare da bata lokaci ba. Kuma har wala yau za ka iya binciken asibitoci daban-daban a fadin duniya domin ganin inda ya dace a duba lafiyarka. Duk wannan ya samu ne sakamakon kimiyyar sadarwa a yau. Sannan a kasashen ma da suka ci gaba, ana iya duba lafiyar mutum ta hanyar sadarwa ba tare da mutum ya gana da likita ba kai tsaye. Wannan yana daya daga cikin ci gaban da aka samu ta wannan fuskancin.

Sannan a halin yanzu ana amfani da sadarwa wajen tattara bayanan mara lafiya da abin da yake damunsa, sannan kuma a adana su ba tare da an rubuta su a takarda ba.  Wanda a yanzu cikin sauki idan ana neman bayanai akan ka, za a iya lalubo bayanan mara lafiyar domin ganin irin kulawar da aka taba ba shi da irin rashin lafiyar da ya yi.

Na Takwas; haka zalika a bangaren wasanni wanda ya hada da na kwallon kafa da na Kwando, da na iyo da na motsa jiki, da kuma wasannin barkwanci da wasannin fima-fimai iri-iri, sadarwa yana ba da gudummawa sosai. Domin ya saukaka yadda ake yin su. Misali; a yanzu ko ta fuskancin tantance kwallon da aka zura a raga a yayin gasar kwallon kafa, sadarwa shi yake ba da gudummawa wajen tantancewa. Sannan ko a bangaren wasannin barkwanci da na fima-fimai, sadarwa a yau yana ba su damar yada ayyukansu ga mutane cikin sauki. Kuma yana taimakawa musu sosai wajen kara haduwa da masoyansu da kulla alaka tsakaninsu harma da alakar kasuwanci da wadansu kamfanoni da ma’aikatu. Wannan yana daya daga cikin irin yadda suke ribantar wannan bangaren.

Na Tara; bangaren sadarwa na ba da gudummawa sosai a bangaren gudanar da kyakkyawan shugabanci nagari. Domin a yau shugabanni za su iya amfani da bangaren sadarwa wajen karbar korafi daban-daban daga wadanda suke yiwa shugabanci, domin fahimtar kurakuransu da abin da ya kamata su yiwa al’umma. Domin a yau al’umma na amfani da wannan bangare wajen bayyana korafinsu dangane da salon irin mulkin da ake yi musu. A don haka idan har shugabanni suka ribaci wannan hanya, tabbas za su gyara mafi yawan matsalolin da al’ummar ke fuskanta, kuma za a samu kyakkyawan wakilci da shugabanci na gari. Domin ba ya ga wannan ma, gwamnati za ta iya tattara ra’ayin ‘yan kasa daban-daban dangane da wani sabon shiri ko wani abu da take son za su kaddamar wa al’umma, yin hakan zai sa su samu shugabanci nagari. Domin da wannan sashen hatta ita kanta gwamnati za ta rika isar wa da jama’a abubuwan da take yi, da wanda za ta yi harma da wadansu bukatu na gwamnatin. Sannan za su rika sanin irin wahalhalu ko jindadin da ‘yan kasa ke ciki.

Na Goma; abu na karshe wanda daga shi zan tsaya ba don su ke nan ba, shi ne yadda wannan bangaren ke haifar da gasa a tsakanin kamfanunnukan da suke kirkirar ci gaba a bangaren sadarwa. Ba don komai ba sai don huldar kasuwancinsu ya bunkasa da kuma ganin sun kawo ci gaban da zai biya bukatun al’umma.

Kamfanunnuka irin su; Microsoft, IBM, Apple, Samsung da HP da sauran su a koyaushe suna cikin binciken domin ganin sun biya huldar kasuwancinsu da bunkasa tattalin arzikinsu tare da bukatun al’umma. Wadannan kamfanunnukan a halin yanzu a koyaushe cikin gasa suke domin ganin sun cimma manufofinsu wanda hakan ke taimkawa al’umma wajen ribantar wannan kimiyyar a yau.

A yanzu, kimiyyar sadarwa a yau ba bangaren rayuwarmu da bai taba ba, wanda yake tabbatar da batu na ke nan da na yi na yi na cewa; sadarwa na da muhimmanci a rayuwar mu a wannan zamanin. Amma za a cimma wannan gacin ne kawai idan muka ci gaba da ribantar bangaren sadarwar ta hanyoyin da suka dace.

Exit mobile version