Connect with us

KIWON LAFIYA

Dalilan Da Ke Haifar Da Katon Ciki

Published

on

Akwai alamu masu nuna cewar wata mukalar da aka rubuta akan katon ciki ko kuma babban kugu, anin ya sa mutane masu yawa sun san yadda jikinsu yake, bugu da kari kuma suna da masaniya yanzu, akan matsalar da zau iya shiga idan suna da babban cikin. An dai yi wasu tambayoyi masu yawa akan yadda za a iya rage shi girman cikin da kuma hanyoyin da za a bi, saboda aga cewar an samo shawo kan irin matsalolin da za a iya shiga. Don haka ne ma yasa taken mukalar wannan makon aka canza ta, daga abinda aka yi niyyar tattaunawa ko kuma tubutawa, shi yasa ma yanzun muke ganin wani sabon abu, babbar fatarmu ita ce abinda aka shiryawa masu karatu zai yi masu amfani, akwai dai alamu maganar gaskiya akan yadda ake samun karin nauyin jiki saboda kiba wadda za a iya lura da ita musamman ma a kugu da kuma ciki, abin yana daukar lokaci kafin a samu wani canji.
Mutane suna iya ganewa idan wasu na yin magana dangane da yadda kugunsu yake kara yin fadi, ko kuma lokacin da suka kalli kansu ta madubi, lokacin da kuma zasu gane cewar ashe girman kugunsu da kuma ciki, ya dauki wani sabon salo, da ke nuna tebar ciki. Shi wannan al’amari yana faraway ne sannu a hankali, ana iya dai farkawa ne daga barci tsakanin karfe shabiyun dare,da kuma karfe biyar na safe, wani lokaci ma abin bai iya kaiwa haka. Daga nan kuma sai ayi saurin yin wanka a kuma kama hanya zuwa ofis saboda aikin wannan rana, wani lokaci mu da kanmu zamu tuka motar ko kuma a tuka mu, ana kuma isa ofis ba wani cikakken lokaci na abincin daya kamata, don haka na ma iya cin snaks. Sau da yawa ana iya amfani da lemun kwalba na soda water da kuma biskit, ko kuma cake, biredi, ko kuma meat pie. Wani lokjaci ma kofin shayi ne nko kuma coffee, ko kuma biredi ko hamburg, wani lokaci ma wani abu ne daban wanda zainiya daure ma wasu kai. Koma dai menene wani abincin ya kunshi abin kara kuzari ne, wani kuma mai calorie ne za aci, a kuma bi shi da wasu abubuwan da suka kunshi sikari, ko kuma abin ya wuce hakanan. Duk lokacin da mutum ya dauka yana zaune kan kujerar shi mai kyau, yana karatu ko kuma rubutu, lo kuma yana halartar wasu tarurruka, lokacin su wadannan tarurrukan akan ci snacks sosai babu kama hannun yaro, wadanda kuma suka yi kama da irin wadanda yaci lokacin cin abincin safe ko kuma karin kumallo.
Wasu mutane suma mayar da ofisoshinsu su kasance kamar wani dakin dafa abinci ne, a gidansu. Shi yasa suke samar da nau’oin abinci daban daban,a ofishin su. Akwai shayi hakanan ma Akamu custard, oats, kai har ma teba. Wani hali ne wanda manya ma’aikata suka saba da shi na aiken mataimakansu su sawo masu abinci, wuraren da ake sayar da abinci kusa da ofis.
Ga wadanda basu da wadanda zasu aika suna zuwa ne da kansu wurin da ake sayar da abincin, ko kuma buka, kai duk ma wurin da zasu iya samun abincin su saya, bayan nan kuma sai su dawo zuwa ofisoshinsu, inda zasu ci gaba da zama da kuma iakin su, da kuma lokacin da zasu iya batawa wajen amfani da kafar sadarwa ta zamani, inda zasu yi amfani da komfutar ofis ta kan teburi. Idan kuma lokacin tafiya gida yayi, su zasu tuka kansu ko kuma a tuka su zuwa gida, inda zasu ci abinci mai yawa, sai kuma abinda zai iya biyo baya na kasancewa kan kujera suna kallon tala bijin na lokaci mai tsawo. Wannan halayyace ta mutane masu yawa wadda zata iya daukar awoyi masu yawa, kafin lokacin yin barci yayi, wasu ma ba zasu iya samun isasshen barci ba.
Abu mai yiyuwa ne bayan an ci abincin dare akwai wasu mutanen da duk da hakan zasu iya samun wani lokaci wanda zasu ci gaba da kallon akwatin talbijin, musamman ma wannan lokaci wanda ake buga gasar wasan kwallon kafa ta duniya wadda ake yi a kasar Rasha, akwai mutane da yawa wadanda zasu sa idanunsu babu ko kyaftawa, na lokaci mai tsawo, ba kuma wanda zai iya cewar a cikin lokacin ba zasu sha wani abu ba, na dangin lemun kwalba, ko kuma cakes da kuma sauran wasu dadadan abubuwa. Duk cikin wannan hali za a iya rike remote control a hannu, wannan kuma na nunawa ba wani lokacin da za a iya tashi, sai dai idan da akwai bukatar a shifa masai. Wannan yana nuna babban al’amari shi ne suna suna karawa kansu calories na kawai abinda ke nuna kiba ke nan, ana kara samun nauyi wajen kugu da kuma ciki, sai kuma wasu guraye a kasan ciki, su mata abin nasu a kugu ne da kum,a hannuwa, ko ina cikin jiki akwai kitse. Dalilin maisauki ne wannan ya nuna ne yadda mutane suka damu da su ci nau’oin abinci daban daban, amma kuma basu bukatar su rika motsa jikinsu.
Ba dole bane sai shi abincin ya kasance mai nauyi, muddin dai akwai caloreis cikin shi abincin , baya ga wadda ake da ita a jiki, wannan babbar matsala ce, idan ana maganar karuwar yawan nauyin jiki. Irin wannan nauyin ba za aiya rasa shi ba, ta hanyar yin wani ilinbo saboda a kasa ganin cewar ana da kiba, wannan wani abin dariya ne, babban abida ake so shi ne a rage kiba, ta yadda za a canza yadda ake tafiyar da rayuwa, abinda kuma shi ne zai iya nuna cewar dole duk wata calories din da zamu kona, yo kamata yayi ta zarce wadda zamu sake samu ta hanyoyi daban daban.
Amma kuma duk da hakan akwai wasu hanyoyin da za abi domin a samu shawo kan su matsalolin da ake fuskanta dangane da ita kibar ko kuma yawan karuwar nauyin jiki, da farko dai shi ne a bullo da wani tsari wanda zai iya samar da rage yawan calories, jamar dai yadda muke cin abinci. Ya kamata mu dan yi tattaki duk lokacin da muka ga da akwai bukatar yin hakan, ko dai abin ya kasance koda wane lokaci, ko kuma adan rika bada hutu. Da akwai bukatar arika yin shi dan tattakin saboda motsa jiki, wato daga takawa 8,000 zuwa 10,000 ko wacce rana idan har abin ana son ya kasance da muhimmanci wanda zai amfani jiki. Idan kuma halin jiki bai bada damar yin hakan ba, akwai wasu hanyoyin da za aiya kona su calories din da suka kushi kitse, ana iya yin kurme ko kuma iyo cikin ruwa, ko kuma a tuka Keke, ko kuma ayi wani wasa daga cikin wasanni. Akwai su wasnnin da suka hada da table tennis, lawn tennis, skuash, da kuma badminton, da cikin wasnnin da ake dasu masu yawa. Idan aka samu yin daya daga cikin wasnnin an samu dama ke nan ta kona calories, kamar dai saduwa da mace ke sa ana kona calories.
Idan mutum yana kan gini mai tsawo yana da kyau mutum ya dawo da lifta, amma kumaabu mafi kyau shi ne, ayi amfani da matakala, saboda ta yin hakan ma ana kona wasu calories masu yawa, wato kona uawan kitsen da ke cikin jiki. A tarurruka da ake bada alawa kada mutum yayi amfani dasu, maimakon hakan sai ayi amfani da kayayyakinn marmari. Idan kuma mutum yana bukatar yayi wasu abubuwan da suke da wahala, ba wai kana kara nauyi bane ba kawai, kana ma iya kara girma ne, kana ma iya kara samun kitsen da zai iya zama, ko kokuma kawo maka matsala, musamman ma a cikin hanta.

Advertisement

labarai