Dalilan Da Ke Sa Ake Dadewa Da Cuta Ba Ta Warke Ba

Cuta

Daga Idris Aliyu Daudawa

Tun kafin ko zuwan Turawa mulkin mallaka Nijeriya da ma nahiyar Afirka gaba daya, marasa lafiya ko kuma masu fama da cututtuka, an fara amfani ne da magungunan gargajiya wajen warkar da cututtuka. Sai dai sannu a hankali bayan zuwan ‘yan mulkin mallaka ne aka fara amfani da magungunan zamani wajen warkar da cututtuka.

Ko shakka babu, an samu cigaba tun daga lokacin da aka fara amfani da su, magungunan zamani wadanda aka kirkire su sanadiyar ilmin zamani, kamar su,  kwayoyin magani da allura da daukar hoto domin gano, inda cuta take, da kuma yin gwaji wanda shi ma ake gano wacce cuta ce take damun mara lafiyar.

Hakika ba karamar gudummawa, wadannan hanyoyin ka bayarwa ba, suke kuma cigaba da bayarwa, sai dai kuma wasu abubuwan  da suke kara  jawo koma-baya wajen ganinsu marasa lafiyar sun warke, wadanda sun hada da yadda wanda bai da lafiya da ya fara shan magunguna, misali a ce masa, magunguna nau’i biyar ne, ya sha su ko wanne daya- daya, ko wacce rana, har zuwa kwana biyar ko kuma mako daya ko kasa da haka.

Sai dai kuma, abin da ke faruwa shi ne, da ya fara samun sauki bayan fara shan maganin kwana daya ko biyu, da dai zarar ya ji ya samu sauki shi ke nan kuma sai ya bar shan maganin, sai kuma lokacin da ya sake jin alamun sake dawowar rashin lafiyar, ya kuma koma shan maganin.

Irin wannan hali ne yake ba da gudummawa wajen rashin samun warkewar cuta sanadiyar rashin bin ka’aidar da aka bayar tun daga asibiti sashen magani, wadanda su kuma suka bi umarnin da likita ya bada na magungunan da yake ganin idan aka ba mara lafiyar, ya kuma yi amfani da su kamar yadda ya dace zai samu sauki sosai ko kuma ya rabu da cutar gaba daya.

Haka abin yake ga yin allura, sai ka ga likita ya ba da umarni na mara lafiya a yi masa allura sau biyu a rana, har kwana uku, wani ma abin yana iya wuce hakan, wannan kuma ya danganta ne ga yadda cutar take.

Sai kuma shi abin da likitan ya ga ya fi dacewa ko matakin da ya ga idan ya dauka zai taimakawa maras lafiyar.

Abin bai tsaya kan shan magani ba, kamar yadda abin bai tsaya ga allura ba, domin kuwa idan aka zo maganar mara lafiyar kawo fitsari ko ba-haya ko yau ko za a ja jininsa, idan ya kawo daya ko biyu cikin an yi sa’a ba zai kawo sauran ba, a gwada domin gano irin cutar da take damunsa, wanda hakan zai sa cutar ta dade tana nukurkusarsa. Bayanin bai sauya ba, wajen daukar hoto a wani sashe na jikin mutum, nan ma idan an yi sa’ar ya je an dauki hoton wurin, wani bai sake komawa wajen karbar sakamakon hoton da aka yi, ballantana ma shi likitan ya san irin maganin da ya kamata ya rubuta masa da zai taimaka masa wajen samun sauki sosai da kuma warkewa.

Muddin dai su marasa lafiya wasu daga cikinsu za su cigaba da nuna irin wannan hali na ko in kula, hakan zai sa cuta ko cututtuka su dade suna tare da wadanda ke fama da su.

Da akwai bukatar gwamnati ta dauki nauyin wayar da su marasa lafiyyar muhimmancin bin umarnin likitoci wajen matakin da suka dauka, domin ganin sun samu waraka daga cututtukan da suke damunsu.

 

Exit mobile version