Khalid Idris Doya" />

Dalilan Da Suka Hanani Biyan Kudin Giratuti A Jihar Bauchi, Inji Gwamna M.A

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

 

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya fito fili ya bayyana dalilan da suka sabbaba har zuwa yau bai biya kudin kammala aiki na tsoffin ma’aikatan gwamnatin jihar ke bin gwamnatin ba; wato kudin giratuti.

Gwamna Muhammadu Abubakar ya bayyana cewar a sakamakon rashin amincewa da ya yi da lissafin aka gabatar masa kan tsabar biliyoyin giratuti da ake bin gwamnatin jihar ne ya sanya gwamnatin jihar mai ci ta dakatar da batun biyan har sai ta samu sahihin adadin kudin da ake binta na giratuti.

Gwamnan jihar wanda ke jawabi a jiya Talata a wajen bukin ranar ma’aikata wanda ya gudana a farfajiyar dandalin tunawa da Sa Abubakar Tafawa Balewa Stadium da ke Bauchi.

Gwamnan ya sha alwashin cewar a shirye yake ya fara rage kudaden giratuti da ake binsa, amma koda wasa ba zai amince da ba shi kidayar adadin kudin da ya wuce hanakali ba, yana mai shan alwashin cewar ko a yanzu aka bashi sahihin adadi zai fara rage kudin da ake binsa.

M.A Abubakar ya bayyana cewar ba fa zai sake ya yi wasa da damarsa wajen amincewa da kidayar da a ciki akwai surkulle ba, yana mai rokon wadanda abun ya shafa da su yi wa Allah su yi wa Annabi su gabatar masa da hakikanin adadin kudin domin gwamnati ta gama kimtsawa don fara biyan kudaden da ake binta.

Ta bakinsa, “A kan batun kudaden giratutu, a shekara ta 2015 an gabatar mini da cewar naira biliyan 15.5 ne kudin giratuti da ake bin gwamnatin jihar. Bayan da kudin Paris Club ya fito daga gwamnatin tarayya; na biya bashin albashin da ma’aikata ne bin gwamnatin jihar Bauchi; na so na rage kudin giratuti da ake binmu a jihar, amma kuma sai aka gabatar min da wai naira biliyan 26.3 ne ake bin gwamnati, wannan dalilin ya san a ce sai an binciko,” A cewar gwamnan.

Muhammad Abubakar ya ci gaba da cewa, “Ban san ta inda kudin ya karu haka sosai ba; a shekara ta 2015 naira biliyan 15.5 kawai daga wannan lokacin zuwa shekara ta 2017 sai kuma kidayar ya dawo biliyan 26.3, wannan ya wuce hankali,” A cewar shi.

Gwamna Abubakar ya bayyana cewar kasantuwar wadanda yake magana da su ma’aikata ne, sun san illar da ke cikin fitar da kidayar da babu sahihanci a cikinsa, don haka ne ya nemi wadanda abun ya rata a wuyayensu da su yi duk mai iyuwa wajen fitar da sahihin adadin kudin da ake bin gwamnatin domin a shirye yake ya fara ragewa “A shirye nake na fara rage kudin giratuti-A shirye na ken a fara ragewa, don haka ina rokon ku, ku fitar min da sahihin adadi domin a fara biyan kudin na,” A cewar shi.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan hakan, yana mai cewa ya kamata ne ya biya kudin, domin ko shi kansa yana son haka, ya bayyana cewar a kowani lokaci yana kwana da tashi da batun giratuti a ransa, “kudin giratuti na kara karuwa, domin mutane suna ci gaba da yin ritaya, yanzu ne lokacin da za a fara biyan kudin nan, don haka ina bukatar tallafinku domin a samu nasarar fara biyan nan. Amma ban san dalilin da kudin nan zai yi ta karuwa daga inda mu bamu san ta ina yake karuwa ba, dole ne a kawo mana sahihin lissafi,”.

M.A Abubakar ya kuma sake neman ma’aikatan a dukkanin ma’aitakai da su bai wa kwamitin da ya kafa domin binciken hakikanin adadinin domin samar wa gwamnati sashin lisassafi domin fara biyan masu hakki-hakkinsu.

Gwamnan ya bayyana cewar yanzu haka kwamitin na nan yana ci gaba da tantance hakikanin masu bin gwamnati kudin giratuti da kuma nawa ne suke bin gwamnatin yana mai shan alwashin fara biya da zarar ya samu hakikanin lissafin hakan.

Tun da fari ma, gwamnan jihar Bauchi ya bayyana cewar gwamnatinsa ba ta taba wasa da da biyan ma’aikata hakkinsu na albashi ba, ya bayyana cewar a kowace wata gwamnatinsa na sauke nauyin albashin ma’aikata da ke wuyansa, duk da matsatsin da gwamnatin ke fama da shi.

Tun a farko da yake tasa jawabin, shugaban kungiyar Kwadago na jihar Bauchi Hashimu Gital ya nuna farin cikinsa da zagayowar wannan ranar, sai kuma ya yaba wa gwamnan jihar a bisa kokarinsa a kowani lokaci na biyan ma’aikata albashinsu a kan lokaci.

Ya nemi gwamnan da ya kara himma kan hakan, sannan kuma ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban da su ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata domin kwalliyar aik take biyan kudin sabulu.

Gital ya bayyana cewar a kowace ranar 1 ga watan Mayu ne suke kaddamar da wannan ranar ta ma’aikata, yana mai cewa yau sama da shekaru 40 kenan ana gudanar da wannan gagarumar taron a fadin kasar nan.

Ababen da suka wakana a wajen taron sun hada da faretin murna da zagayowar wannan ranar, inda ma’aikatu daban-daban suka yi macin cikin kaya bai-daya suna nuna murnarsu da kuma alfahari da wannan ranar tasu ta ma’aikata.

Da yake ganawa da manema labaru kan wannan ranar, shugaban kungiyar Kwadago na jihar Bauchi Alhaji Hashimu Gital ya nuna amincewarsu kan binciken sahihin kudin da ake bi domin gwamnati da masu bin giratuti kowa ban kwari wani ba “Matsayinmu muna kira ne da a biya kudin giratuti,  koda yake ka ji gwamnan ma da kansa ya fada yana son biya. Sai dai abun da ya bashi tsoro kidayar da aka bashi a baya, da ya zo zai biya kuma sai kudin suka haura, wannan dalilin ne ya sanya ya nemi bincike domin a gano hakikanin adadin da ake biy, don haka muna bayan tattancewar da za a yi domin sa mu cika dukkanin abun da ake nema,” in ji shi.

Gital ya yi fatan Allah ya maimaita musu wannan ranar, yana mai kira ga ma’aikata da su ci gaba da zage damtse wajen gudanar da aikinsu a kowani lokaci domin ci gaban jihar ta Bauchi.

 

Exit mobile version