Dalilan Da Suka Sa Farashin Kayan Amfanin Gona Ya Fadi Warwas A Bana ­—Farfesa Sani

Gabatarwa.

FARFESA SANI YUSUF AHMAD shi ne mataimakin Daraktan Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Manoma Da Bayar Da Dabarun Noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya, a taunawarsu da Editanmu SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI, a ofishinsa da ke harabar Cibiyar,  ya bayyana muhimmancin zaben iri nagari wajen noma. Farfesan ya kuma bayyana, dalilan da suka sa farashin amfanin gona, ya fadi warwas a bana, wanda hakan zai  haifar illa ga tattalin arzikin kasar nan, da kokarin wadata kasa da abinci. Masu karatu ku biyo mu domin jin yadda tattaunar ta kasance:

Masu karatunmu za su jin tare da muke a halin yanzu?

Sunana Farfesa Sani Yusuf Ahmad mataimakin Darakta na Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Manoma Da Koyar Da Dabarun Noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya.

Kasancewarka kwararre a fannin noma kuma hamshakin manomi a aikace, me manomi ke bukata domin ya samu cin nasara wajen aiwatar da noman nasa?

Da farko dai ga dukkan manomin da yake bukatar cin riba wajen nomansa, dole ya tabbatar da cewa, ya samu ingantaccen iri. Samun ingantaccen iri shi ne, abu na farko wajen  samun nasarar noma, bayan an tanaji wuri mai kyau.

Ya ya kake ganin shirin gwamnati na bai wa manoma rance domin bunkasa harkar noma?

Wannan shiri abu ne mai kyau, sai dai inda gizo ke yin sakar shi ne, ba a aiwatar da shirin kamar yadda ya kamata domin ana ba manoman shirin a kunshe, ma’ana ba a fayyace musu cikakken yadda tsarin yake, yadda manoma za su yi wa abin kyakkyawar fahimta, na su karba ko su bari.

Akwai Hukumar NIRSAL da gwamnati ta kirkiro domin bayar da agaji ga manoman da wata annoba ta rutsa da su, ya ya kake ganin aikin wannan Hukuma, kana ganin aikin nata na fiya daidai ko ko akwai lauje cikin nadi?

Babba matsalar wannan Hukuma ita ce, ta tsaurara matakan da za a bi kafin manoma su amfana da ita, saboda haka ana iya cewa, manufar kafa hukumar na taimakawa manoma, bai samu nasara ba, domin manoman ba sa iya cin moryar da yakamata su ci daga hukumar.

Sannan abu na biyu kuma shi ne, an takaita aikin Hukumar. Ma’ana tunda an kafa ta ne domin ta ragewa manoma asara, yakamata a irin wannan lokaci da farashin amfanin gona ya yi warwas, ta fito ta sayi amfanin gonar a hannun manoma a kan farashin da ya dara na kasuwa, yadda manoman ba za su yi asara ba.

In ka dubi wasu kasashen duniya, idan aka samu irin wannan yanayin na faduwar farashi, irin wannan hukumar ce ke sayen amfani a hannun manoma da daraja, domin a karfafawa manoman wajen ci gaba da wannan sana’a tasu, amma ka a nan kasar ba haka abin yake ba.

Saboda haka, matukar wannan Hukuma za ta taimakawa manoma, sai ta sassauta ka’idojinta, kuma ta kara fadada ayyukanta.

A bana an samu faduwar farashin amfanin gona wanda hakan ta karya gwiwar manoma wajen fadada noman na su musamman ma na masara, me kake ganin ya haifar da wannan faduwar farashin?

Akwai abubuwa da yawa da za a iya cewa, sun taimaka wajen faduwar farashin amfanin gonar a bana, amma jigo daga cikinsu su ne, bayar da kofa da gwamnati ta yi na shigo da masara daga wata kasa zuwa wannan kasa.

Sannan kuma abu na biyu shi ne yadda ake amfani magununan kashe kwari masu karfin gaske wajen adana amfanin gonar, yin hakan na kashe kasuwar kayan amfanin gonarmu a wasu kasashen duniya, sakamakon tsoron da suke ji na yin amani da irin wannan abinci, gudun kada ya haifar musu da larurar rashin lafiya.

Haka kuma rashin sayen amfanin gonar da gwamnatin kasar nan ke yi, da wasu manyan kamafanonin sarrafa amfanin gona shi ma babban jigo ne wajen faduwar farashin. Misali kamar kamfanin yin abincin kaji na Olarm, mai makon ya sayi masarar da zai sarrafa daga wajen manoma, sai ya koma yana nomawa da kansa ko kuma ya sayo kasashen waje.

Shin kana ganin wannan zai shi harkar noma a Nijeriya?

Kwarai wannan zai kawo manufar gwamnati na wadata kasa da abinci da bunkasa tattalin arziki cikas, domin kuwa, bincike ya nuna cewa, manomasun rage yawan masarar da suke nomawa a bana, sun koma noma wasu amfanin gonar da suke hasahen cewa, nan gaba zai yi tsada. Babbar illar yin hakan shi ne, ana iya samun canji kuma, masarar da manoman suka gujewa ta yi tsada badi, domin tana iya yin karanci. Kuma dukkkan abin da ya yi karaci kuma bukatarsa ta karu akwai yiwuwar ta yi tsada.

Wace shawara kake ganin za ka ba manoman?

Babbar shawarata ga manoma ita ce, kada su karaya wajen ci gaba da noma masarar, akwai yiwuwar gwamnati ta dauki matakin dakile waccan hanya ta shigo da masarar da kasashen wajen, a wani kaulin ma ana ganin kamar tuna gwamnatin ta dauki matakin yin hakan, domin kuwa, an lura da cewa, irin wannan masarar da ake shigowa da ita daga kasashen wajen ba ta kai ingancin wadda muke nomawa a nan gida. Saboda haka, idan gwamnatin ta kile hanyar shigowa da masarar daga waje, ta ta mu za ta yi daraja.

Ga ita kuma gwamnati wace shawara kake da ita da za ka ba ta?

Babban abin da gwamnati za ta yi shi ne,ta tabbatar da cewa, dukkan shirye-shirye da suka da su  na taimakawa manoma su tabbatar da cewa, sun kai gare su. sannan kuma akwai sirin da ake tsaurara matakai kafin manomi ya mafana, wanda har takan kai ga ba kowane manomi zai iya cika wadannan ka’idojin ba. Saboda haka, gwamnati ta saukakawa manoma, yadda kuma za su ci moriyar wannan saukin.

Exit mobile version