Dalilan Da Suka Sa Jafanawa Ba Sa Tsoron Mutum-mutumi

Mutum-mutumi

A wani wurin ibada mai shekaru 400 na mabiya addinin Buddha, masu ziyara na iya yawo ta cikin lambunan shakatawa mai duwatsu, su zauna cikin kwanciyar hankali suna shan gahawa, kana suna daukar darussan addinin Buddha daga wani limami da ba a saba gani ba:

Wani mutum-mutumi da ake kira da suna Mindar.

Yana da wata irin fuska mai kwantar da hankali da kuma kamanni wanda ba za a iya rarrabewa ba, ba na tsoho ba ba kuma na yaro ba, ko kuma mace ko namiji. Baya ga fata ta mai kama da ta gaske da ta rufe daga kansa zuwa saman jikinsa, yana nuna rashin kammaluwarsa wanda ke bayyana wasu injina da bututai daga ciki.

Amma Mindar yana da nagarta sosai, yana magana a kan wasu rubutattun kalamai na addinin Buddha masu wahalar ganewa da ake kira Heart of Sutra.

Idan kana so ka gano inda za a samu wani limamin mutum-mutumi, kawai kana bukatar yin tunanin cewa a kasar Japan ne, a wani wurin ibada na Kodai-ji, mai matukar kyau a birnin Kyoto.

An dade da sanin Japan a matsayin kasar da ke kerawa tare da yin mu’amala da mutum-mutumi sosai fiye da komai.

Yayin da ake yawan zuguguta wannan suna da Japan din ta yi a kasashen waje – gidajen ‘yan kasar ta Japan da shaguna ko kamfanoni ba su cika ba da mutum-mutumin ba kamar yadda labarai a manyan shafukan jaridu ke nunawa ba – akwai wani abu daban game da hakan.

 

Abubuwan yau da kullum

Wasu masu sa ido na kasar Japan sun ce addinin gargajiyar kasar, Shinto, ya bayyana yadda yake kaunar mutum-mutumi.

Shinto wani yanayin amfani da tsirrai ne da ake dangantawa da ruhi ko, ba ga mutane kadai ba har ma ga dabbobi, da abubuwan dake kewaye da mutane kamar tsaunuka, har ma da abubuwa kamar fensira.

“Ko wane abu yana da rai,” a cikin kalaman Bungen Oi, limamin limamai na wurin ibadar mabiya addinin Buddha da ke yi wa mutum-mutumin karnuka jana’iza.

Kamar yadda wannan ra’ayi yan nuna, babu wani banbanci tsakanin mutane, da dabbobi, da kuma abubuwa, don haka ba wani abin al’ajabi ba ne don mutum-mutumi ya nuna halayya irin ta dan’Adam – yana kawai nuna irin na shi ruhin ne.

“Ga ‘yan kasar Japan, muna iya ganin abin bauta a cikin wani abu,” in ji Kohei Ogawa, jagoran wadanda suka kera Mindar.

Tsarin amfani da tsirrai wajen bauta na cin karo da falsafar al’adaun Yammacin duniya.

Mutanen Girka ta zamanin da suna da al’adar amfani da tsirrai a fannin yadda suke ganin rauhanai a wurare kama koramu, amma kuma suna tunanin ruhin bil’Adama da tunaninsu daga sama da sauran halittu da abubuwa da ke kewaye.

Addinan Musulunci, da na Kirista da kuma na Juda na saka mutane a babban matsayin na kasancewa halittar Ubangiji mafi girma da daraja.

An kuma gargadi Yahudawan zamanin baya kan bayar da muhimmanci ga abubuwa, don kada su zama masu bauta wa gumaka, wanda dokoki goma da Ubangiji ya saukar wa Annabi Musa suka haramta.

Addinin Musulunci ya haramta bautar gumaka da ma kera duk wani abu mai kama da dabba ko kuma mutum.

Kada ku yi wa halittun Ubangiji shisshigi

Kamar yadda al’adunsu yake, tunanin Yammacin duniya suna nuna, duk wani inji da zai rika yin abubuwa kamar na dan’Adam, ya saba wa tsarin iyakar halittu.

Wannan gargadi game da dabi’a na nuni da sanannen abu a tarihi game da fasaha, kamar Frankenstein, wanda ya samo akasarin sakonnin ciki na halayya ta gari daga littafin Bible, in ji Christopher Simon, wani farfesan kwatanta al’adu a Jami’ar Addinin Kirista a birnin Tokyo.

“Dakta Frankenstein ya kirkiri rayuwa a jikin wani dodo. Kamar wasu mutane da cin ‘ya’yan bishiyar ilimi a lambun Eden. Wannan shi ne ainihin aikata sabo; a sakamakon haka, aka hukunta mu,” in ji shi.

A karshen labarin marar dadi, bayan da Dakta Frankenstein da dodon nasa duka suka mutu: “Ku yi taka-tsan-tsan mutane. Kada ku ce za ku dauki matsayin Ubangiji.”

Wasan Jamhuriyyar Czech na shekarar 1920 RUR, wanda ya gabatar da kalmar ”robot” wato mutum-mutumin da aka yi wa taken addini: daya daga cikin ‘yan wasan ya kirkiri mutum-mutumin da ke tabbatar da cewa babu ubangiji, yayin da dayan kuma ya ce ya kamata a ce mutum-mutumina yana da ruhi, kana mutum-mutumi biyu da suka fara soyayya aka lakaba musu suna “Adam” da “Ebe” wato “Hauwa’u” da ”Adamu”.

A karshen labarin, mutum-mutumin sun hallaka kowa ban da daya.

 

Exit mobile version