Dalilan Da Suka Sa Ramos Ya Bar Real Madrid

Real Madrid

A daren ranar Talata kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar cewar kyaftin dinta Sergio Ramos zai bar kungiyar da zarar yarjejeniyarsa ta kare a karshen watan Yunin nan da muke ciki.

Ramos, mai shekara 35 a duniya, ya lashe kofuna da yawa a Real Madrid ciki har da gasar La Liga biyar da Champions Leagues guda hudu, tun bayan da ya koma kungiyar daga Sebilla a shekarar 2005.

Mai tsaron bayan ya buga wa Real Madrid wasanni 671 da cin kwallo 101, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen watan Yuni kuma tuni sun yi sallama da shugabannin kungiyar

Me  ya sa Ramos zai bar Real Madrid?

Ba wanda zai ce Sergio Ramos zai bar Real Madrid, ganin kokarin da ya yi wa kungiyar da rawar da ya taka, amma kwallon kafa babu tabbas kuma dai kyaftin din na tawagar Sifaniya ya samu sabani da shugaban kungiyar Fiorentino Perez da ta kai dole ya hakura da Real Madrid.

Cikin watan Janairu mahukuntan kungiyar sun zauna taro da Ramos kan tsawaita yarjejeniyarsa a Real Madrid wadda za ta kare a karshen watan Yunin nan sai dai sun kasa cimma matsaya a tsakaninsu da ta kai Ramos ya fara yanke kauna da Real Madrid tun kafin kammala kakar da ta wuce.

Ramos wanda ya hangi kokarin da ya yi wa Real Madrid yana hangen da rawar da zai taka shekara biyu nan gaba, sannan a saka shi cikin masu horarwa kaka biyu bayan nan.

Sai dai shugaban Real, bai yi wa Ramos alkawarin cika masa bukatunsa ba, kuma a lokacin da kungiyar ta ce za ta rage albashin ‘yan wasa – Ramos bai amince da hakan ba  tun daga nan dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu.

Daga nan Ramos ya ji cewar ba a kyauta masa ba, kuma ba a bashi kulawar da ta kamata ba, hakan ne ya kara samar da wagegiyar baraka tsakanin kyaftin din da Florentino Perez, wanda a kwanakin baya aka sake zabarsa a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Sai dai kuma taron da suka yi a watan Janairu kan tsawaita yarjejeniyar Ramos da ba su cimma matsaya ba, ita ce ta harzuka dan kwallon Sifaniyar saboda daga nan basu sake nemansa ba.

Ramos dai ya yi fama da jinya a kakar da aka kare, sannan ga shekaru a tare da shi, kuma sabon koci da aka dauka Carlo Ancelotti ba lalle ne ya dogara da Sergio Ramos ba mai shekara 35 duba da cewa bai halarci gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi a bana ba, bayan da tawagar kwallon kafa ta Sifaniya ba ta gayyaci mai tsaron bayan ba.

Exit mobile version