Dalilan Da Za Su Iya Sa A Dakatar Da Tsarin Almajirci A Kasar Nan!

A kwanakin baya ne, gwamnatin tarayyar ta tabo wani muhimmin labari mai sarkakiya, inda ta bayyana yuwuwar duba tsarin karatun allo da Almajirci, a kasar nan, ta dalilin matsalar tabarbarewar tsaro.

Furucin wanda ya fito daga bakin babban mai bai wa shugaban kasa shawara ta harkar tsaro (NSA), Babagana Mungono, a lokacin da yake zanta wa da manema labarai a fadar shugaban kasa, jim kadan da kammala taron kaddamar da kwamitin masu ruwa da tsaki a sha’anin tattalin arziki, wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Mungono ya bayyana cewa dakatar da tsarin Alamajircin da makamantun allo zai dauki dogon lokaci ana aiwatar dashi bisa ingantattun matakan tsaro a kasa.

Ya shaidar da cewa, wannan yunkurin yana da alaka da bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bika ga gwamnoni, kan su magance duk wata matsalar da za ta iya kawo cikas wajen aiwatar da wajibcin ilimin firamari da karamar sakandire ga yaran da shekarun su suka isa zuwa makaranta, kana da daura aniyar samar da karin wasu makarantu na daban domin almajirai.

Wannan yunkuri ya jawo zazzafar mahawara tare da cece-kucen dimbin yan Nijeriya; wasu na ala-san-barka tare da yaba wa wannan shiri na gwamnati, a gefe guda kuma wasu na suka tare da kalamai masu zafi a kan kudurin. Wanda bisa ga hakan ya jawo fadar shugaban kasa maida jawabi da cewa, rusa tsarin karatun Almajirci yana nan a matsayin zabi, wanda kuma wai gwamnatin Buhari ta na son ta dakatar dashi nan take ba; kamar yadda kafafen yada labarai ke kwarmata lamarin ba.

Har wa yau, sanarwar fadar shugaban kasa dangane da wannan lamarin, ta ofishin mai taimaka wa shugaban kasa ta sha’anin yada labarai, Garba Shehu inda ya bukaci masu caccakar wannan matakin wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana, na mayar da ilimi matakin farko ya zama dole ga kowane yaro a Nijeriya- kama daga firamari zuwa karamar sakandire, sa’ilin da yake jawabi a taron kaddamar da yan kwamitin masu ruwa da tsaki a sha’anin tattalin arziki, na kasa wanda ya gudana ranar 20 ga watan Yuni.

Haka kuma, fadar shugaban kasa ta sake nanata cewa, gwamnatin Buhari ta dauri aniyar samar da tsarin ilimi kyauta wanda zai zama wajibi ga yaran da shekarun su suka isa zuwa makaranta, shiri ne wanda zai dauki dogon lokaci kafin aiwatar dashi, wanda kuma zai kawo karshen yawan adadin yara da basu samu damar zuwa makaranta ba, yayin da idan hali ya samu- idan an ga yuwuwar dakatar da tsarin Almajirci, amma bayan tuntubar bangarorin da suka dace.

Wanda kuma idan za a iya tunawa, zauren majalisar dattijan da ya gabata, a watan da ya gabata, ta nuna damuwar ta dangane da yadda wannan tsari na makarantun tsangaya ke gudana a jihohin arewacin Nijeriya, lamarin da ya jawo koma baya ga karbuwar ilimin boko ga jama’a da dama da ke sha’awar tsarin.

Wanda bisa la’akari ga hakan, ya jawo wannan bukatar domin yin aiki da dokar nan da ta samar da tsarin ilimin bai-daya ta Unibersal Basic Education Act, ta shekarar 2004 wadda ta sanya wajibcin tsara makarantu don bai wa yaran da suka kai shekarun ilimin, daga shekara ta daya zuwa tara (9).

Yayin da bisa ga wannan manufar ne ya jawo zauren majalisar dattijan, ya bayar da umurni ga mahukuntan da hakkin aiwatar da tsari ya hau kan su, kan cewa su aiwatar da yadda dokokin sashe na 2 zuwa 5 suka kunsa, kan cewa su dakatar da duk wata makarantar da ba ta cikin wancan tsarin, wadda ke gudana a kan tituna, a daidai awanin karatu.

A bisa ka’ida, ya dace a fahimci cewa makarantu allo, tsari ne na ilimin Addinin Musulunci Wanda mafi yawa ake aiwatar dashi a arewacin Nijeriya. Haka kuma, ma’anar kalmar Almajiri ta samo asali ne daga harshen Larabci,  wadda take nufin “al-Muhajirun”, wanda a Hausa aka fassara ta ga duk mutumin da ya bar garin sa na asali da nufin neman ilimin Addinin Musulunci. Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, wannan tsarin ilimi a nan Nijeriya ya samo asali ne daga daular Kanem-Borno, wadda sarakunan ta suka himmatu wajen nema tare da karantar da Alkur’ani Mai Tsarki.

Wanda bayan sama da shekaru 700 a baya, ita ma daular musulunci a karkashin Sheikh Usuma Danfodiye wadda ta kafu a birnin Sakkwato, ta doru ne bisa koyarwar Alkur’ani Mai Tsarki. Wanda daga bisani, wadannan dauloli guda biyu; Sakkwato da Borno suka cimma matsaya wajen gudanar da tsarin makarantun tsangaya a tsakanin su. Wanda ta la’akari da gudumawar da wannan tsari na makarantun tsangaya ya samar, wanda shi ne ya yaye zakakuran manyan malaman addini da tarihi, musamman a tsohuwar daular Kanem Borno da takwarar ta, kana da rawar da suka taka wajen ci gaban baki dayan Afrika ta yamma.

Bisa wannan gabar, a nawa tunani dangane da wannan tsari na makarantun tsangaya, bai kai ayi masa cin moriyar ganga ba, balle har ace na yanzu ya daga masa karan gazawa, ko wani katabus da tsarin ilimin yanzu zai ce ya zarta shi. Sannan ba na ji wani zai daki kirji ya yi gigin ayyana makarantun tsangaya (Alamajirci) a matsayin wadanda suka kasa amfanar da al’umma. Wanda shekarun baya bayan nan ne lamarin makarantun tsangaya ya sauya daga manufar sa ta asali.

Yayin da abinda kullum idon mu ke  arba dashi, shi ne dandazon kananan yara almajirai, rike da roba suna yawo kwararo-kwararo suna baran abinci da kurdi. Wanda a bangare guda kuma, maimakon su kuma malaman su kula da yaran tare da karantar da su, sai suka fake da yaran wajen amfanar kawunan su. Lamarin da ya kai wasu kan yi badala dasu, wani zubin kuma su ci zarafin su.

Exit mobile version