Khalid Musa" />

Dalilan So

Muna iya fassara ma’anar dalili da sababi ko jagora. Dalilan so ke nan na iya kasancewa sababan so ko abinda ya jagoranci zuciya ga abkawa cikin soyayyar masoyi/masoyiya.
Shaihun Malami Ibnul-Kaimi-Aljauziy cikin littafinsa Raudhatul Muhibbiyn wa Nuzhatul Mushtakiyn ya gabatar da ababa uku cewar sune sababan soyayya. Abinda nake nufi da soyayya a nan ba ya nufin so, domin so daga janibi guda ne kadai yayinda soyayya na faruwa ne daga janinibi biyu, wato daga fuskar mai so da wanda ake so. Sababan da malamin ya gabatar sune:
i. Kyawun siffa
ii. Fadaka
iii. Dacewar ruhi ko gamon jini.
Duk yayinda wadannan siffofi suka cika suka karfafa labudda ne soyayya na karfafa har tai yauki. Hakanan nan soyayya na karfafa ne gwargwadon karfi da cikar wadancan siffofi da muka ambata, hakaza ta kan raunana gwargwadon rauninsu. Idan kyawun siffa ya cika, sannan a ka samu fadakar zuciya ga wannan siffa kyakkyawa kana dacewar ruhi ta biyo baya a nan ne a ke samun soyayya da’ima madauwamiya.
Sai dai kyawun siffar abin kauna ya danganta ga mutane. Wani ko wata kan iya zama nakisi a zahiri amma sai ya zama akasin haka a idanun masoyi, har ya zamanto ba ya ganin akwai mafi kyawun abin kaunarsa. Wata rana Azzatu ta shiga wajen Hajjaju, sai yace da ita, “ya ke Azzatu, wallahi ba ki kasance kamar yadda Kuthairu ke wassafa ki ba” sai Azzatu tace da shi “Ya kai wannan shugaba, ai [Kuthairu] bai kallona da irin idaniyar da da kake kallona. Ai babu mafi girma da kima a idanun masoyi kamar abin kaunarsa.” A bisa hakane Hakim bn Ma’amar bn Kunais Alhadharamiy ke cewa cikin wani baiti, [ma’ana]:
“Ban sani ba shin an kare ta da kyawu ne,
Bisa mataiku ko hankalina ne ke shudewa?”
A kan sami cikar siffar kyawu ga wani ko wata, amma idan babu fadakar zuciya ga wannan siffa sai son ma’abucin surar ya kasa ratsa zuciyar mai kallo. Da zai sami yayewar hijabin gafala ya shaidar da hakikanin kyawun siffar, babu makawa zuciyarsa na ribatuwa. Dalilin hakane ma shari’a ta dorawa mata rufe fuskokinsu[domin fuska ce ke nuna alamar kyau a karon farko] don kaucewa fitinintar da zuciyar mazaje. A bisa wannan hikimar ne ma a ka umarci mai neman aure da lalle ne ya ga matar da yake son aura. Idan a ka yi dace ya fadaka da kyawunta [imma kyawun zahiri ko na badini] ya kusanta ya so ta, so mai karfi da ka iya jayuwa zuwa ga kulluwar igiyar aure.
A cikin wadannan dalilai guda uku da malamin ya bijiro da su, dacewar ruhi ko gamon jini, itace siffa mafi karfin sababin samuwar soyayya tsakanin masoya. Rashin dacewar ruhi ko gamon jini sau da yawa kan kore samuwar alakar soyayya dungurum. Dabi’ar ruhi ce janyuwa ya zuwa ruhin da ya yi kama ko ya siffantu da shi, shi ya sa wani sha’iri ke cewa: “soyayyar kowanne mutum na zaikewa ne ga dacewar ruhinsa”.
Dacewar ruhi ko gamon jini ta kasu kaso biyu. Akwai dacewar ruhi tun daga asalin halitta, wanda shine hausawa ke kira gamon jini ko haduwar jini, sannan akwai kuma dacewar da ake samu saboda tarayya da kuka yi bisa wani ra’ayi ko sha’awa ko manufa. Soyayyar da ta ginu bisa wannan dalili na rushewa yayinda da ra’ayi, sha’awa ko manufa ta sauya sabanin son gamon jini wanda dalilinsa ba ya gushewa. Musabbabin gamon jini kamanceceniyar ruhi ce tun a asalin zubin halitta. Hakan ne ke sanyawa ku karkata ga juna tamkar maganadisu[mayen karfe] da karfe. Ma’abuta irin wannan so ba su da wata amsa ga tambayar ko menene dalilin son su ga ababan kaunarsu. Ba su san dalili ba, ba su san lokacin da son ya kama su cikin zuciyarsu ba har ya yi musu babban kamu. Suna kallon juna kallo mafifici, suna ganin kyawun surar juna fiye da kowacce irin halitta a doron kasa. Muna iya ganin misalin haka a baitin wani sha’iri a inda yake cewa:
“Ita ce sinadarin halittar kyawawa,
Ya ke maganadisun zuciyar mazaje”
Batun dacewar ruhi ya sa wasu cikin manazarta na ganin dalilin so bai takaita ga kyawun sura ba, hasalima dai kyawun sura bai taka wata rawa muhimmiya idan an aunata da tasirin gamon jini. Duk yayin da a ka sami kusancin halittar ruhi tsakanin wasu za ka samu shakuwar jini da soyayya mai karfi tsakaninsu kome rashin kyawun dayansu kuwa, domin dabi’ar ruhi ce, karkata zuwa ga kamanninsa. Muhammad bn Dawud Azzahiriy na cewa cikin wasu baitukansa:
“So bai kasance domin kyawun sura ba,
Taklifi ne an ka kallafa shi ga zuciya.”
Ya ci gaba da bayanin cewa, ko shakka babu so wani madubi ne da mutum kan hanga ya kalli halaye, da dabi’un halittarsa cikin surar wacce yake so. Shi ya sa wasu ke cewa ba abinda masoyi ke so illa dabi’u da kamanninsa, ma’ana, kansa dai kadai yake so ba abar kaunar ba.
Soyayyar da ta ginu bisa dacewar ruhi ko haduwar jini itace soyayya madauwamiya. Amma idan ta samu ne domin wani dalili mai gushewa kamar tarayya cikin buri, ra’ayi, sha’awa ko manufa tana shudewa tare da shudewar wannan sababi. Dukkan son da a ka haifar da shi bisa wani dalili mai wucewa ko yayewa, to wannan so ba zai karko ba, domin yana karewa tare da yankewar sababinsa. Amma idan wata siffar halitta , ko dabi’a ta zama tushen kaunar , to soyayyar da ta ginu bisa wannan sababi ita ce ke dorewa mutukar hali bai canza ba ko cutarwa mai so ga wacce yake so. Babu abinda ke iya raunana soyayyar gamon jini kamar cutarwar masoyi ga masoyi, wasu na ganin ma har takan iya tumbuke so daga zuciya dungurum. Wani sha’iri na cewa bisa wannan lamari kamar haka: {ma’ana}
“Ki yi hakuri dani za ki dauwami zuciya,
Kar ki zam mai caccacaka yayinda nake fushi,
Na tsinkayi so da cutarwa a zuciyar masoya,
Idan sun hadu bakasafai so kan zauna ba shi.”
Sai dai kuma wasu sun bambanta bisa wannan ra’ayi, suna ganin soyayyar gaske babu abinda ke gusar da ita. Rashin tausayi ko cutarwar abin kauna kan rage ta ne kadai. Wasu kuma na ganin ita kan ta cutarwar masoyi na daga cikin dadin soyayya. Abu Shaisu na cewa cikin baitinsa da ya zamewa wannan ra’ayi muhalli shahidi:
“Kin so magagabta sun zame min ababan kauna,
rabautuwarki da su shine rabauta ta da ke.
Zargin masu zargi ya zame min dadin dadada,
Ku zargen ko na ji ambatonta na dada tuntuni.
Wannan shine so na hakika mutukar so, domin karkatar zuciyarsa ga burin abar kaunarsa ko da wannan buri da take a kan sa mummuna ne. Ya yarda da ya wulakanta kan sa don kawai ya yi muwafika da bukatarta na ya wulakanta. Hakanan ya so makiyansa domin ta so su saboda musguna masa. Duk da dai kasancewar irin wannan so a na kyamatarsa, amma yana nuna mana hakikanin gaskiyars soyayya da abinda take wajabtawa zuciya.
Wasu manazarta kuma su ka ce, cutarwar masoyin ga abin kauna kan yaye so dungurum cikin zuciyar masoyi, saboda an gina zuciyar dan Adam bisa son duk mai kyautata ma ta hakanan kuma ta kyamaci mai musguna ma ta. Wa su kuma suka kama tafarkin daidaito tsakanin wandannan ra’ayoyi guda biyu. Masu wannan ra’ayi suna cewa ya yiwu zuciya ta so wani abin kauna sannan kuma lokaci guda ta ki wani abu tare da shi. Ko da cutarwar da masoyi kan yiwa abin kauna ya rinjayi soyayyarsa, hakan na iya rage tasirin son da abin kauna ke wa masoyi ne ba tare da cire son masoyinsa ba baki daya. Misalin haka ya baiyana cikin waken Abdullahi bn Dumaina inda yake cewa cikin baitukansa:
“Da za ki umarcen shiga wuta lalle ki san,
Zan zamo mai yarda da bi don ki kusatar da ni,
Zan mika kafa ina mai taku ciki,
Nufinki shiryarwa ko ko son ki batar da ni,
Idan zuciyata ta munana don kin cutar da ni,
Na ji dadin jin zuciyarki na zantawa da ni,
Kula da tasirin alakar ruhi ne ma ya sa wasu cikin maluma suka fassara so da ma’anar gaurayar ruhi da ruhi saboda dacewa da kamantuwar dake tsakaninsu” Sun buga misali da cewa idan an gauraya ruwa da ruwa ba za a iya maiyazewa ba, hakanan ma ruhin masoya kan gauraya da juna. Shi ya sa masoyi kan ji zafin abinda da ya sami masoyinsa maras dadi hakanan ma akasin sa. Kissoshin magabata sun nuna yadda a ka rinka samun kwanciyar rashin lafiyar wasu domin kwantawar masoyansu ba tare da sun san da rashin lafiyar ababan kaunar ba. An sami labarin cewa wani masoyi ya kwanta rashin lafiya kwanaki, har dai wata rana wasu su ka zo duba shi a lokacin ya sami sauki. A zantawar da su ka yi da shi ne yake tambayarsu daga ina suke, sai suka fada masa cewa ai sun je gidan wane ne dubiyar wane[wance]. Sai yace, ba shi [ta] da lafiya ne? sai su ka ce “E, amma ta sami sauki”. Sai ya ka da baki yace da su: Wallahi rashin lafiyar nan tawa na rasa dalilinta. Zatona da ma shine ko dai wani masoyina ne ke kwance ba shi da lafiya. A yau din nan jin na sami sauki na tashi da wani irin farin ciki da jin cewa mai yiwuwa Allah ya tashi kafadarsa [ta]. A nan ne ya dauki alkalami ya rubuta wadannan baituka gareta, cewa:
“Na kwanta zazzabi ban san da kwancinki ba,
Har sai da ‘yan dubiya su ka zo sun zantar da ni,
Ba domin zazzabin da ya zamo ya sameki ba,
Da wagga ciwo bai kasance zaikewa ga ni.

Habibiy.

Exit mobile version