Daga Musa Muhammad, Abuja
An kammala dukkan shirye-shirye don fara kashin farko na tallafin da ‘Gidauniyar Sardaunan Badarawa’ ta shirya don daukar nauyin auren mata zawarawa, musamman marasa karfi a duk fadin shiyyar Kaduna ta Tsakiya, wadanda ba za su iya biyan bukatun yin wani ingantaccen bikin aure ba, amma suna da burin zaman yin auren.
Da yake bayani ga manema labarai bisa ka’idojin da dole ne sai an cika su kafin Bazawara ta kasance mai cin gajiyar samun tallafin da za a gudanar, Shugaban gidauniyar, Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya ce an zabo amintacciyar mata wacce za ta kula da gudanar da harkokin bibiyar kowace mace a duk kananan Hukumomi bakwai, wadanda suka hada Shiyya ta Biyu, wanda ake kira da Shiyyar Kaduna ta Tsakiya.
kananan Hukumomin sun hada da, shiyyar Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Chikun, Igabi, Birnin-Gwari, Kajuru da Giwa.
A cewarsa, nauyin da matan masu kula da shiyyoyin za su dauka sun hada da yin bincike, tantancewa da zaban zawarawa na kwarai wadanda suka cancanta, wadanda za su ci gajiyar shirin. Kana ya nuna cewa za a ci gaba da aiwatar da shirin ne da nufin rage yawan mata marasa aure a cikin al’umma.
dan takarar Sanatan na Kaduna ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC ya koka kan yawan matan da aka sake su, wanda ya lura da cewa sun tsunduma cikin harkokin shan kwayoyi da kayan maye saboda bakin cikin da ke tattare da su a bisa mutuwar aurensu.
Ya kara da cewa, idan aka bar matsalar ta ci gaba da lalacewa, to zai yi mummunan tasiri ga tarbiyyar matasa wadanda ake musu lakabi da shugabannin gobe, wadanda dole ne su kasance masu kyawawan dabi’u.
Mazaunin garin Kadunan wanda ya kasance Shugaban rikon kwarya na Kaduna ta Arewa, ya bayyana cewa za a zabo zawarawa 100 daga kowace karamar Hukuma, wanda hakan ya sanya jimillar rukunin farkon suka zama 700, inda ya bayyana cewa an samu babban tsarin ne mai nagarta bayan an aiwatar da ayyukan gwajin tabbacin da za a iya samar musu da biyan bukatun su.
Ya kara da cewa a tsarin shirin da aka yi, sai da aka tabbatar da an samu wadatattun kayan da aka kebe domin yawan adadin mutanen da za a biya musu bukatun su da kudi na kyawawan kayan auren matan 700, sannan kuma aka samar musu da wani kunshi na kayan tallafi da zimmar karfafawa domin kowace mace ta amfana da shi bayan ta yi aure.
A cewarsa, katifa kawai da wasu kananan abubuwa na iya zama wani nakasu da zai hana yawancin mata zawarawan sake yin aure.
Usman Ibrahim, wanda ke rike da sarautar San Turakin Hausa daga Masarautar Katsina, ya kara da bayyana cewa, ba da wani lokaci mai tsawo ba shirin karfafa wa matasa da nufin samar da kiraye-kiraye ga dimbin samarin da ba su da aikin yi a mazabarsa shi ma zai fara shi.
“Ina tabbatar wa da ‘yan mazabata cewa zai kasance wani tsari ne wanda zai tabbatar da gaskiya da adalci, kuma na tabbatar wadanda suke da bukatarsa ne kawai za su ci gajiyar sa. Za a fitar da fom din da za a cike shi da bayanan wadanda za su ci gajiyar shirin bayan an yi cikakken bincike,” inji shi.
Ya kara da cewa, “wannan aikin zai dore ne har sai an cimma burin shirin don rage yawan zawarawa da suke a shiyyar Kaduna ta Tsakiya, ta hanyar baiwa mata damar dogaro da kai, yaki da matsalar karuwanci, shan miyagun kwayoyi da sauran abubuwan ayyukan ci gaban jama’a.”
“Al’ummar da ba ta yin komai ba don duba wahalhalun da marasa galihu da mata ke ciki, musamman zawarawa da marayu wadanda addu’o’insu ke da matukar muhimmanci ga ci gaban mutane, to zai yi wuya ta zauna cikin lumana da jituwa,” inji Sardaunan.
Sardauna Usman ya kara da cewa, “yana da muhimmanci mu kula da gaskiya da kuma tallafa wa mabukata a tsakanin mu, mu saurari kukan su, mu biya bukatun su, kuma mu yi musu kyauta da nuna kauna a gare su, domin Allah ma ya yi farin ciki da mu, kuma ya saukar mana da ni’imominsa akan duk abin da muke yi don amfanin al’umma. ”
A karshe ce Sarakunan gargajiya da shugabannin addinai duka za su shiga cikin shirin don inganta shirin.