Dalilin Al’ummar Barandau Na Hana Sabunta Katin APC

Daga Muhammad  Salisu Seeker,

Al’ummar garin Barandau dake mazabar Limawa a Karamar hukumar Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, sun yi kiran da a soke akwatunan zabensu da kuma yin kashedi ga dukkan wani dan siyasa na jam’iyya mai mulki ta APC da takwarorinsu na jam’iyyun hamayya da kada suka kara shiga musu gari da sunan yakin neman zabe, domin sun yafe cigaba da mu’amula da su jimlatan sakamakon rashin ayyukan cigaba ga yankin.

Hakan ya biyo bayan umarnin da jam’iyyar APC ta bayar na cewa, kowanne dan jam’iyyarta ya sabunta katinsa na shaidar zama dan jam’iyyar da yi wa sababbin mambobi rijista.

Sai dai al’ummar ta Barandau sun ki bin umarnin da jam’iyya mai mulki ta yi na sabunta kati tare da fitar da wani kashedi ga dukkan jam’iyyun siyasar da suke fadin jihar da cewa, kar wani dan siyasa ko na jam’iyya mai mulki ta APC ko takwararta ta PDP su kara shiga musu gari, don gudanar da kowanne irin harkokin siyasa.

Wannan dalilin da matakin da suka dauka ya kawo kiraye-kiraye daga wakilan al’ummar akan me ya yi zafi haka kuma su zo a zauna mana, amma sun ki kuma sun ce kada wanda ya zo musu gari matukar akan matakin da suka dauka ne na harkokin siyasa, walau Jam’iyya mai mulki ko abokiyar hamayyarta ta PDP.

Bayan korar waDanda aka tura garin, don sabunta wa jama’ar garin katin jam’iyyar, Wakilin LEADERSHIP A YAU ya tuntubi wasu daga cikin mutum garin da suka hada da shugaban akwatin garin na Jjam’iyya mai mulki da takwaransa na PDP da su ka yi wani kalar auren zobe kan ra’ayi iri guda akan dukkan ‘yan jam’iyuun nasu.

Safiyanu Isyaku Barandau, mai shekaru 52, kamar yadda ya bayyana mana, wanda shi ne  shugaban akwatin jam’iyya mai mulki ta APC, ya bayyana mana dalilansu na daukar wannan mataki kamar haka: “Gaskiya ba ma jin dadin yadda aka mai da mu marasa amfani a siyasar wannan mazaba da karamar hukuma da ma jihar nan gabadaya, kamar yadda ba irin gudunmawar da ba mu bada ba, amma mu an watsar da mu, ba mu da amfani sai lokacin da abu na siyasa ya taso ake tunawa da mu. Amma in dai abin da ya shafi cigaba ne ba ma ganin sa in kuma akwai wanda yai mana mu ka yi masa wannan butulcin ya fito ya fada.”

Ya ce, “ta fuskar bayar da gudunmawa kuwa ba za a fada mana ba, da na fito da sakamakon zaben da ya gabata da na nuna maka Kuma duk shugabannin sun sani ai sun zo lokacin yakin neman zaben su duk sun ga matsalolin da muke ciki,Kuma sukai mana alkawari suna yin nasara zasu aikata.

“Ba wanda ba mu je gurinsa ba, karshe ma wani Dan majalisa da muka je gunsa akai korar karnuka yai mana. Wannan dalilin yasa muma muka koma gefe muna jiran ranar da za a tuna da amfanin mu, kuma sai gashi an zo Wai masu katin Jam’iyya sun zo garin mu kowa ya fito, mu kuma baza muyi ba mun yafe har abada”. Alhassan Sani mai shekaru Arba’in da biyu, shi ne shugaban akwati na jam’iyyar mai hamayya na garin na Barandau, mun masa tambayoyi game da wannan zumunci na siyasa da suka kulla bata tare da kallon su abokan hamayya bane na daukar wannan mataki Kuma har ga ‘yan jam’iyyarsa da yanzu basu suke mulki ba.

“Dariya ya fara tare da cewa su da suke mulki ina mu ina siyansu, kawai zama mukai muka kalli garin mu da cigabansa fiye da duk wata siyasar wahalar da kai.

“Ba iya ‘yan jam’iyyarsa bane har nawa dalilin da yasa ma yai magana a matsayin wanda yake jagorantar Jam’iyya APC da kuma ni da nake jagoranta Jam’iyyar  PDP mai hamayya domin kafin suyi mu mukai mulki,kuma muke cin akwatin mu,amma ba ai mana ba, har suka kada mu. Suma lokacin su ya zo yanda akai ta wasa da hankalin mu a Baya haka ake musu. Wannan yasa muka gane bakin su daya wasa suke da tunanin mu,hakan yasa muka ajiye adawar siyasa muka kalli matsalolin da suka gadar mana da su babu yadda za mu yi.

“Ta wannan hanyar suna gajab-gajab suke shigowa muna nuna musu kodayaushe suna kauda kai, Kuma ba Wanda lokacin yakin neman zabe baya zuwa, Amma tunda suka ci ba idanun wanda muka gani, sai yanzu da aka zowa abokan hamyyar mu da sabunta Kati suka ce baza su yi ba, muma dama haka namu sukai mana, sai muka ajiye siyasa muka yadda garin mu dan shi muke siyasa amma kowa ya maida mu bamu san me muke ba muyi magana ace kauyawa ne kudi muke nema, to bama son sisin kowa ya rike Kuma kar ya haromu da shi ga matsalolin mu nan,in kuwa baza a iya ba to akwati dai ko ta PDP ko ta APC mun yafe a soke mu daga mazabar Limawa.”

Lami Idrith ita ce Wakiliyar Mata a garin na Barandau, an tambaye ya me ya sa mata ma sun goyi bayan hukunci da mazajen garin suka yanke, sai cewa ta yi, “akwai wadanda suka fi shan wahalar matsalar rashin hanyar nan da bata fi kilo mita biyu ba irin mata.

“Ka san mu da lalura ta haihuwa,idan mace Bata da lafiya ko tana da ciki ta hanyar nan za abi da ita ana gwajab-gwajab da ita zuwa asibiti, wata kafin aje sai dai ta ce ga garinku nan ta rasu,ya zamu yi . Don haka mu yanzu mun yanke hukunci suje su rike komai nasu, amma kar su shigo mana gari Wallahi.

“An sha mu mun warke ba abinda wani zai kawo mana yanzu in ba wadannan matsalolin namu ya kalla ba yai mana, kudi kan suje su rike abinsu Wallahi yanzu ko nawa zasu bamu bama so, in kuwa ba za su yi mana ba,muma mun daina zaben a soke akwatin mun yafe har abada.”

Exit mobile version