An yi hadaka tsakanin asusun da ke tallafa wa bunkasa aikin noma na kasa (NADF) da kuma Gwamnatin Jihar Jigawa, inda suka kaddamar da shiri na farko na bai wa manoma bashin noma.
A cikin sanawar da asusun ya fitar, shirin zai bayar da dama ga masu zaman kansu, musamman kananan manoma wajen ba su bashin kudin noma tare kuma da kara samar musu da wadataccen abinci.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
Babban Sakataren Asusun, Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa; shirin zai magance gibin da kananan manoma ke fuskanta wajen samun rance kudaden noma.
Shi kuwa, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Aikin Noma na Jihar Jigawa, wato JATA Dakta Saifullahi Umar, ya bayar da tabbacin cewa; jihar ta mayar da hankali wajen bunkasa fannin aikin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani tare da jawo kamfanoni masu zman kansu, ta hanyar yin hadaka.













