Abubakar Abba" />

Dalilin CBN Na Bai Wa Kamfanoni Shida Kawai Lasisin Shigo Da Madara

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa, ya bai wa wasu kamfanonin dake a cikin kasar nan su guda shidda lasisin shigo da madarar shanu daga wasu kasashen waje.

Kamar yadda Babban Bankin Nijeriya CBN ya zayyana Kamfanonin da ya basu izinin sune, Friesland Campina WAMCO Nigeria limited, Chi Nigeriya limited, TG Arla Dairy Products Nigeria limited, Promasidor Nigeria limited , Nestle Nigeria PLC da kuma Integrated Dairies Limited.

Babban bankin na Nijeriya ya sanar da hakan ne a ranar Talatar dsta gabata a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun Daraktan sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji.

Daraktan na sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji ya ci gaba da cewa, bai wa bawa kamfanonin lasisi yana bisa tsarin kudirin gwamnati na habaka samar da Madara a cikin kasa da kuma sauran wasu abubuwan da ake sarrafa su da Madara.

A cewar Daraktan na sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji babban bankin kasa (CBN), ya kuma sanar da cewa, umarnin da bankin ya bai wa kamfanonin su shida, ta fara aiki nan take.

Daraktan na sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji ya kara da cewa, babban bankun na Nijeriya CBN, ya sanar da sunayen kamfanonin shida ne kadai suke da lasisi daga gun gwamnatin tarayya don shigo da madarar ta shanu daga wasu kasashen waje.

Daraktan na sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji ya sanar da cewa, babban bankin na Nijeriya CBN, ya bai wa wani Kamfani fam na takardar ‘M’ na damar shigo da kaya daga kasashen waje.

Daraktan na sashen kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN Mista Ozoemena Nnaji ya kara da cewa, an bai wa kamfanin fam din ne bayan kamfanonin da babban bankin na Nijeriya CBN ya ya cika dukkan sharuddan da ya kama na shigo da kaya daga kasashen waje zuwa cikin kasar nan.

Sai dai, wasu masu fashin baki a fannin samar da madarar shanu a kasar nan, suna ganin mai makon a bai wa irin wadanan kamfanonin lasisin na shigo da madarar daga kasashen waje, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta samar da kyakyawan tsarin da zai inganta samar da madarar a kasar nan, musamman ganin cewar, fannin ya na samar da kudaden shiga ga kasa mai dimbin yawa.

Sun kara da cewa, ganin yafda Nijeriya ta yi fibe a duniya waken yawan dabbobi, musamman shanu, ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta fitar da tsare-tsare yadda za’a karawa masu kiwon shanu kwarin gwaiwa don su dinga samar da ingatacciyar madarar shanu da zata wadaci kasar nan da kuma wacce za’a dinga fitar da ita zuwa kasuwannin duniya don sayarwa.

Exit mobile version