Shekaru masu yawa da aka fara yin gyaran gashi, da yawan kitso, da sanya gashi da kuma kone gashi sun bar wata wacce ta ke son ta zama mai tallar kayan kawa ‘yar kasar Afirka ta kudu mai shekara 31 ta kasance da sanko.
Tayi bayanin cewar “A kullum idan na isa wurin da ake gyaran gashi na cire gashin da na sa a kai na, zan sa su kone gashi na da sinadarai kuma na sa wani sabon gashin a ranar – Na dade ban bar gashin kai na ya sha iska ba,” a cewar Bandile (wannan ba sunan ta bane na gaskiya ba).
Wata cuta ke damunta da ke kakkabe gashi wadda ake kira da sunaTraction Alopecia, kuma tana makarantar sakandare ne lokacin da ta fara gano cewar gashin ta na kakkabewa.
Amma mazauniyar Johannesburg din ba ita kadai ce ta ke fuskantar irin wannan al’amarin ba – yana shafar daya daga cikin kashi uku na matan Afirka a cewar wani bincike da aka wallafa a mujallar aikin likitanci “Clinical, Cosmetic and Inbestigational Dermatalogy”.
Wani binciken da cibiyar Boston Unibersity’s Slone Epidemiology Center ta yi a shekara uku da suka gabata ya nuna cewar kusan kashi 48 cikin 100 na mata 6,000 ‘yan asalin Afirka suna fuskantar kakkabewar gashi a tsakiyar kansu ko kuma a gefen kansu – cutar ta Traction Alopecia ce ke sanadiyar shi al’amarin na kakkabewar gashi.
Duk da yake su masu fama da irin wannan cutar basu cika bayyanawa ba, amma kuma wani shi ne yawan wadanda ke fuskantar matsalar yana karu.
“Idan aka ce mu cire gashin da muke sawa a kan mu, to takwas a daga cikin mata 10 za su samu matsala. Wani abu ne kawai da ba mu magana a kai, kuma ba za mu yi ba don muna jin kunya sosai,” a cewar Bandile.
‘Likitan ya gaya mani cewa na ja gashi na daga tushensa tun da na taba manne wani gashin da ba nawa ba a kaina. Abin da na yi amfani na manne gashin, ya bata tushen gashin nawa”.
Kuskure Game Da Gashin Halitta
Bandile ta dora shi alhakin matsalar kan tunanin da mutane ke da shi na cewa sa gashin da ba naka ba a kan ka, domin kitso yana kara tsawon gashin halittar mutum.
Wasu hasashen kuma sun ce matan Afirka suna kashe a akalla dala bilyan shida, wato fam bilyan hudu kan kitso da gashi a ko wacce shekara.
“Ko wacce mace ta fi daukar kanta da daraja idan ta sa gashin da ba nata ba ne ba. Rabinmu muna tunanin cewa idan kina da dogon gashi, to kin fi kyau da kuma karbuwa a idon jama’a,” inji ta.
“Ko wacce mace mai bakar fatar da na sani tana son a ce tana da dogon gashi. Suna yin kitso kaanana a kansu, wanda ke jan gashin,”
Wanan labarin Susan Magai ta san shi sosai. Tana da shagon gyaran gashi wanda yake babban birnin Tanzania, Dares Salaam.
“Yawancin mata sun saba amfani da mai wanda bashi da kyau domin sa gashi, ko kuma suna barin gashin ya wuce lokacin da ya kamata ya kasance a kan su,” a cewar ta.
“Muna yawan ba masu zuwa shagonmu cewa kada su wuce mako biyu da gashi a kansu, amma wasu sai su bar gashin ya kai wata uku, abin da ke janyo musu kakkabewar gashi.”
A shagon Ms Magai ana gudanar da wani tsari wanda a cewar ta yana taimakawa kan wajen barin gashi ya fito da kyau.
“Tsarin kamar dafa gashi ne. Muna amfani da man kwakwa wanda muke shafa wa a kan mutum. Sai mu rufe gashin mu dafa shi tare da amfani da wata na’ura klamar dai yadda ta bayyana”, ta kuma kara da cewa watarana sai an yi wata da watanni kafin tsarin ya fara aiki.
A cewar hukumar Institute of Trichologists da ke Birtaniya, wannan tsarin zai iya yin tasiri akan gashin ‘yan Afirka saboda yana kara mai a kan wanda ke hana karyewar gashi. Amma, hukumar tana gargadi akan cewa yin hakan kawai ba shi zai kara wa mutum gashi ba bayan kuma ya yi fama da kakkabewar gashi.
Fuskantar Rashin Gashi Bayan Haihuwa
Jumoke Koso-Thomas, wata likita ce wadda ke dai zama a Birtaniya wacce ke rubutu a wani shafin intanet na kiwon lafiyar mata bakaken fata, ta bayyana cewar yawan gyare-gyaren gashi shi ke janyo cutar Alopecia, wasu kuma daga kwayoyin halittarsu ne.
Alal misali, kakkabewar gashi zai iya zama wata alama ce ta wasu cututtuka ciki har da ma ciwon mashako da ciwon koda, in ji ta.
“Haihuwa, da shan maganin tsayar da haihuwa da kuma damuwa duk suna iya janyo kakkabewar gashi tsakanin mata,” a cewar Dokta Kosso, ta kuma kara da cewa kakkabewar gashi zai iya tafiya daga baya.
Boitumeo Monyaki, mai shekara 39, wata dalibar da ke nazari fannin kudi daga birnin Johannesburg ta rasa gashin ta gaba kaya ne shekara takwas da suka wuce – abinda take tunanin cewa haihuwarta ta farko ne ya janyo mata hakan.
Ms Monyaki ta bayyana cewar rasa gashinta ya shafi kwarin gwiwarta amma yanzu ta ko yi zama da tunanin cewa har abada watakila gashinta ba zai cika ba kamar yadda yake tun farko..
Tana son ta samo wa matan Afirka da suke fama da wanan matsalar taimako: “Har da masu shagon gyaran gashi ba su san maganin wannan matsalar ba.”
‘Kasancewar Mu ‘Yan Afirka Ne’
Dokta Koso-Thomas ta bayar da shawar bcewar da akwai bukatar kayayyakin abincin da suka kunshi duk wani nau’in na abinci da ake bukata, musamman wanda ya kunshi sinadarin bitamin C, bitamin B da kuma selenium, wanda ake samu a kayayyakin marmari, wadannan za su taimaka wajen gyaran gashi, wanda kuma daga karshe shi ma zai taimakawajen maganin cutar alopecia, sai kuma kaucewa duk wata matsalar da zata kawo rashin zubewar gashi.
Cin abinci mai Bitamins zai iya taimakawa fitowar gashi mai lafiya
Tana tunanin cewar mata da matasa ya kamata su canza yanayin yadda suke gyaran gashinsu.
“Ya kamata mu ci gaba da fada masu: ‘Ku yi kokarin kaucewa yin abubuwa masu yawa a kan gashinku. Kada ku sa sinadirai da yawa kuma kada ku rika kisto a kullun. Ku rika barin gashin yana dan hutawa kuma ku rika sauya irin kitson da kuke yi a lokuta daban daban.”
Bandile ta ce wannan shawara ce da zata iya samun karbuwa ganin yadda mata masu yawa yanzu suke kokarin gyara gashin da aka halicce su da shi.
“Su na son gashin halittarsu kuma sun fara rungumar asalinsu,” in ji ta, a inda ta bayyana cewar ta gaji da boyewa kullun a karkashin gashin wanda ba nata ba.
“Yanzu kawai ina son in je wurin aiki da gashin da aka halicce ni da shi ne.”