Abubakar Abba" />

Dalilin Da Ya Sa Ba A Iya Dakatar Da Shigo Da Madara Nijeriya Ba

Shigo Da Madara

Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona  na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Uwargida Chioma Achilam, ta ce an kirkiro da tsarin daftarin Masana’antun sarrafa madara na cikin kasar, wanda har yanzu ke kan aiki, don tabbatar da kara samar da madara a Nijeriya ba wai zai fara dakatar da shigo da madarar cikin kasar nan nan ta ke bane.
A cewar Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari Uwargida Chioma Achilam, manufar ta shafi shirin nan na baya-baya na hadewar kasa (BIP), inda masu ruwa da tsaki da yin kiwo za su zuba jari a Nijeriya tare da shigo da kayan aiki cikin kasar don samar da madara.
Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari ta kara da cewa, manufofin sun yi kama da Tsarin Raya Suga na kasa, wanda kuma ke amfani da BIP don bunkasa darajar sukari a Nijeriya don kawar da shigo da sukari.
A cewar Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, an dauki BIP din ne saboda Nijeriya ba ta da isassun klkarfin gida na iya dakatar da shigo da kayayyakin madara ba zato ba tsammani, amma ana iya cimma hakan cikin lokaci.
Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari ta bayyana manufofin Masana’antu na sarrafa madara da masu ruwa da tsaki don kayan aikin su kuma hakan zai daidaita kafin a tura kwafin ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya don amincewa.
Mataimakiyar Darakta a sashen kayan amfanin gona na Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari ta sabar da cewa, “Ba gaskiya bane cewa manufar ta karfafa shigo da madara daga waje, inda ta kara da cewa, manufofin na duban hadin kai na baya kuma hakan, zai bai wa mutanen mu karfin tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ga dubban yan kasar nan”.
A wata sabuwa kuwa Ministan ma’aikatar noma da raya karkara Sabo Nanono, ya jadadda aniyar gwamnatin tarayya na haramta shigo da madara cikin kasar nan.
Nanono ya ce, daga shekarar 2022 ko shakka babu za a daina shigo da madara domin ma’aikatarsa na shirye-shiryen samar da hanyoyin sarrafa ta a cikin gida, inda ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, Nijeriya ce kan gaba a wajen samar da shinkafa da rogo a duniya.
Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara cikin kasar daga shekarar 2022.
Nanono ya bayyana hakan ne a yayinda ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya bayanin cewa, ma’aikatar na shirye-shirye domin tabbatar da samar da kayayyaki don samar da madara.
Ya ce, “Muna shirye-shirye a wannan ma’aikata kuma ku zuba ido ku ga abunda na fadi, a shekaru biyu masu zuwa za mu haramta shigo da madara cikin kasar nan, inda ya ce muna da shanaye miliyan 25 a kasar nan da za su samar da madara lita miliyan biyar a kullun”.
A cewarsa, “Matsalar a yanzu shine kayayyakin amfani, wanda mun fara shirye-shiryen dasa hanyar sarrafa madara a fadin kasar, inda ya ce, ban ga dalilin da zai sa mu shigo da madara a shekaru biyu masu zuwa ba”.
Nanono ya kuma ce a yanzu Nijeriya ce ke samar da shinkafa da rogo mafi girma a duniya, inda ya kara da cewa, “Nijeriya ta habaka shirin samar da shinkafa domin karfafa harkar noman shinkafa a cikin gida sannan ta tsare hanyar shigo da yar waje.
Ministan ya cigaba da bayyana cewa, farashin kayayyaki da ya hau a yanzu saboda annobar Korona zai sauko a yan watanni masu zuwa.

Exit mobile version