Connect with us

KASASHEN WAJE

Dalilin Da Ya Sa Ba A Sanar Da Trump Batun Rasha Ba – White House  

Published

on

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta kare kanta kan dalilin da ya sa ba a gabatarwa da shugaba Donald Trump wani rahoto da ya nuna cewa wani rukunin dakarun Rasha da ke tattara bayanan sirri, na ba da tukwici ga mayakan Taliban domin su rika kashe sojojin Amurka da ke Afghanistan ba.

Sakatariyar yada labarai a fadar White House, Kayleigh McEnany ta fadawa manema labari hakan jiya Litinin a lokacin da aka tambayeta dalilin da ya sa ba a sanar da shugaba Trump ba, inda ta ce “ba a tabbatar da rahoton ba ne.”

Ta kuma kara da cewa, “an samu ra’ayoyi mabanbanta ne tsakanin hukumomin tattara bayanan sirrin kasar,” kan rahoton, dalilin kenan da ya sa ba fada mai ba.

Fadar White House ta gudanar da taro a jiya Litinin din ga wasu ‘yan majalisar wakilai 8 kan wannan batu yayin da ake samun kiraye-kiraye daga bangarorin jam’iyyun kasar biyu kan a fito a bayyana gaskiyar lamarin.

Ita dai shugabar Majalisar wakilai Nancy Pelosi na bukatar darektar hukumar leken asiri ta CIA Gina Haspel da darekta John Ratclife na hukumar tattara bayanan sirri na kasa, da su yi yi wa ‘yan majalisar wakilai 435 bayani kan wannan lamari.

Tuni dai Rasha da kungiyar ta Taliban suka musanta wannan rahoton wanda jaridar New York Times ta fara wallafawa a farkon makonnan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: