Connect with us

NOMA

Dalilin Da Ya Sa Cibiyar LCRI Horar Da Manoman Alkama  

Published

on

Cibiyar Gudanar da Bincike Aikin Noma ta Chadi  LCRI da aia doawa alhakkin sarrafa Alkama a Nijeriya ta fara horas da Manoman sababbin dabarun noman Alkama irin na zamani da aka samo daga kasar Masar.

Sabuwar dabarar ta noman Alkamar sun hada da, yin amfani da yin amfani da na’ura kuma anyi hakan ne da nufin samar da Alkamar mai dimbin yawa a kasar nan.

Ko’odinetan Shiyya na sashen ciyar da fasahar aikin noma ta Afirka (TAAT), Farfesa Ibrahim Umar Abubakar ne ya bayyana hakan a taron horas yadda ake noman Alkama na shekarar 2019 da yada za’a inganta noman ta tare da kaddamar da noman Alkama na kakar bana.

Cibiyar LCRI ce ta shiryawa Manoman na Alakama tare da hadaka da TAAT da shirin noman Alakama na Sasakawa dake Afir da Ma’aikatar aikin gona da kuma sauran hukumomin ayyukan aikin gona da aka gudanar a jihar Kano.

A cewar Ko’odinatan Shiyya na sashen ciyar da fasahar aikin noma ta Afirka (TAAT), Farfesa Ibrahim Umar Abubakar rungumar sababbin dabarun, zasu nunawa Manoman na Alkamar wasu gonakan da aka kebe da Manoman na Alakama don su gani a zahairi karkon da dabarun da aka samo daga kasar ta Massr suke dashi don nuna irin Albarkar amfanin ta Alkamar ako wacce kadada daya sabanin yin amfani da dabarun baya da aka sani, inda ya ce, dabarun na baya, basa samarwa da Maniman na Alkamar wani sakamako mai kyau.

Ko’odinatan Shiyya na sashen ciyar da fasahar aikin noma ta Afirka (TAAT), Farfesa Ibrahim Umar Abubakar ya ci gaba da cewa, wadannan sababbin dabarun, sun hada da yin amfani da inji tare da yin shuka a lokaci guda, inda hakan zai kuma bayar da kariya daga lalacewar da zata iya aukuwa  a gonakan na noman Alkamar saboda rashin ruwa mai yawa.

A cewar Koodinatan Shiyya na sashen ciyar da fasahar aikin noma ta Afirka (TAAT), Farfesa Ibrahim Umar Abubakar, “Muna fatan zuwan wadannan sababbin dabarun na noman Alkamar, zasu tsamo mu daga cikin matsalar da Manoman na Alkamar a jihar ta Kano suke a ciki na noman na Alkamar a wannan kakar ta bana,”

Shi kuwa Shugaban Kungiyar Manoman Alkamar ta kasa (WFAN) Alhaji Salim Muhammad ya sanar da cewa, Manoman na Alkamar sun jima suna tabka asara mai yawan gaske, inda ya kara da cewa, horaswar, a kan rungumar sabbkin dabarun na noman na Alkamar, babu wata makawa za ta taimaka wa manoman na alkamar yadda za su samu girbi  na alkamar a kan ko wacce kadada daya.

Shugaban Alhaji Salim Muhammad ya kuma shawarci mahukunta dssu a cikin gaggawa tabbatar da daukin da za a bai wa aanoman alkama ya riske su kan lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: