Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dalilin Da Ya Sa Dan Shekara 23 Ya So Ya Bindige Iyayensa

Published

on

Wasu iyaye mazauna a yankin Kiharu dake Murang a cikin kasar Kenya sun tsallake rijiya da baya sakamakon hallaka su da dan su yaso ya yi, amma bindigar taki tashi.

Lamarin ya auku ne a ranar Lahadin data wuce, inda dattawan magidantan masu suna Muthoni da Maina suna cikin gudanar da aiki a cikin gonar su, sai dan nasu ya danno cikin gonar dauke da bindiga kirar G3 ya kuma umarce su dasu gabatar da addu’ar su ta karshe.

A hirar ta da manema labarai, Muthoni ta ce, yaron dan kishiyar tane wanda kuma alummar kauyen sun san shi sosai.

A cewar ta, “ina cikin aiki a gona sai naji wata kara tana fitowa daga cikin dajin dake kusa da gonar, inda ina dubawa sai naga yaron mai suna Ephantus Muilwa ya kwamta a kasa rike da bindigar a hannun sa yana auna mu nida mahaifin sa.”

Ta ci gaba da cewa, a lokacin da yaron ya gane cewar mun riga mun ankare dashi, sai ya yi wani ihu ya ce, “ku fadi addu’ar ku ta karshe kafin in aika ku lahira.”

An ce yaron ya riga ya dana kunamar bindigar, inda ya auna mahaifin nasa amma sai bingigar ta cije taki tashi.

A cewar ta, can kuma sai bindigar ta yi kara, amma babu daya daga cikin mu da ya samu rauni bayan da iyayen suka ruga don neman mafaka.

Matar ta bayyana cewar, bayan kasa  samun nasarar yaron akan nufin sa, sai yaron ya saka bindigar a cikin buhu ya arce ya bar gonar akan babur din da yake a gefe yana jiran sa.

Ta sanar da cewar, wannan bashi karo na farko da yaron ya tayar da yamutsi ba.

A cewar ta, yaron yana zargin nice na sanya baban sa ya kori mahaifiyar sa ya kuma jina yana yin barazanar son kashe ni harda mahaifin sa.

Wani mai suna Godfrey Waweru, wanda lamarin ya auku a gaban sa ya ce,”ina cikin tafiya a cikin gona ta sai na ji harbin, inda bayan na samu inda na boye sai ha hangi yaron ya ranta a na kare daga cikin gona dauke da wani buhu a kafadar sa sannan sai ya dare kan babur ya kara gaba.

Mataimakin shugaban ‘yan sanda Cif Bernard Kagoto ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, ma’aura tan sun sanar dashi a rubuce.

A cewar sa,“naje wurin da lamarin ya auku tare da jami’ai na don gudanar da bincike.
Advertisement

labarai