Connect with us

NOMA

Dalilin Da Ya Sa Gidanuniyar AATF Ta Gabatar Da Sabon Irin Cowpea 

Published

on

Gidauniya Aikin Noman Fasaha a Nahiyar Afrika (AATF ta bayyana cewa, ta gabatar da shiri aikin noma don tabbatar da an samar da ingantaccen Irin cowpea ga manoman sa wani sabon samfarin Irin na cowpea na (PBR).

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a babban birin tarayyar Abuja.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya ci gaba da cewa, sabuwar fasahar zata taimaka matuka wajen kula da amfanin na cowpea da manomansa suka noma.

A cewar jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, manoman na cowpea, za su iya yin amfani da samfarin Irin na (PBR) irin yadda suke bukatar yin amfani dashi ba tare da samun wata tangarda ba.

A cewar Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, sabuwar fasahar, na bukatar a kula da ita yadda ya dace, inda hakan zai baiwa manoman na cowpea damar amfana yadda ya kamata.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, haka manufar kuma ita ce don a tabbatar da ana kula dashi yadda ya dace, tun daga farkon lokacin da aka gudanar da yin gwaji a kansa a dakin yin gwaje-gwaje zuwa masu kimiyya daga nan kuma zuwa gun kamfanonin da za su sayarwa wa da manoman na cowpea don kuma suyi amfani dashi a kan gonakansu.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, sabon Irin na cowpea, ba koma zai zamo wani nauyi ga manoman na cowpea ba, inda ya kara da cewa, sai dai ma ya kara masu ilimi da kuma taimaka masu kan yadda za su yi amfani dashi a cikin sauki.

Don a tabbatar da Irin na cowpea ba’a gurbata shi ba Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya bayyana cewa, hukumar zata yi kmfani da lambar wayar tafi da gidanka ta (MAS) da shirin ya tanada a matsayin dabarun gano Irin da aka gurbata shi.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya kara da cewa, hukumar zata samar da tsarin da yadda da manoman sunga Irin za su yi saurin gane shi don gudun kada a sayar masu da wanda bashi bane ba.

A cewar Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, muna tunanin wasu mutanen za su iya hada komai don sayarwa da manoma da sunan cewar samfarin Irin na PBR ne.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya sanar da cewa, don a tabbatar da manoman sun samu igantaccen Irin, hukumar zata yi amfani wayar tafi da gidanka ta hanyar yin amfani da lambar sirri yadda manoman za su samu Irin.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya bayyana cewa, din a samu dorewar shirin, hukumar ta AATF ta na yin iya matukar kokarinta kan hakan.

Ya kara da cewa, a don hakan ne hukumar take kan yi aiki kafada da kafada da hukumar gudanar da bincike a fannin aikin noman rani ta kasa da kuma hukumar (NAERLS) don a bai wa malaman noman rani horon da ya dace.

Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya sanar da cewa, hukumar ta kuma tattaunawa kashi-kashi da hukumar NAERLS, inda ya kara da cewa, nan da yan watanni masu zuwa, za’a fara horas da malaman aikin gona da ke a kasar nan musamman a kan irin ingancin da samfarin Irin na PBR cowpea.

A cewar Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, manoma za su kuma iya zuba samafrin Irin na PBR cowpea da kuma akan sauran amfanin gona da suka shuka a kasar.

A karshe Jami’in shirin da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya kuma yi nuni da cewa, idan hukumar ta AATF ta janye zuwa wani lokaci, ganin cewar an samar da sabon ingantaccen Irin na cowpea a kasar nan ne, Nijeriya zata dora kan inda hukumar ta tsaya, musamman ganin cewar fatan da ke ake yi shine ci gaba da dorewar shirin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: