Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa NIWA ta sanar da cewa, ta fara gudanar da aikin gyran hanyoyin ruwa da ke a jihar Legas, bisa yunkurin cire dukkan Fulawar da ke fitowa a cikin ruwan, su kuma haifar wa Jiragen Ruwan da ke wucewa kan ruwan tangarda.
Ofishin hukumar na yankin jihar Legas ne, ya fara aikin a ranar Juma’a, inda ta tura ma’aikata domin yin tsare-tsaren yin aikin, mussamman domin magance matsalar fulawar da ke a cikin ruwan da ke a yankinthe Ikorodu.
- Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka
- Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, tawagar ma’aikatan hukumar ta hukumar ta NIWA tuni, sun kai manyan kayan aiki, domin fara gudanar da aikin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta bai wa Jaridar LEADERSHIP, kwafi ta fara gwaji na aikin daura da yankunan Ebute Ikorodu da kuma Ikpakodo.
Sanarwar ta kara da cewa, aikin zai tabbatar da cewa, Jiragen ruwan da ke bin hanyoyin ruwan za su samu sauki wajen yin zirga-zirga ba tare da wata matsala ba.
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.














