Ibrahim Muhammad" />

Dalilin Da Ya Sa Man Girki Ke Tsada Yanzu – Mustapha Shu’aibu

Mustapha Shu'aibu

Sakamakon tsadar da man girki ke yi, musamman manja ya sa ake dora nauyin hakan kan masu hada-hadar saida man.Hakan ta sa wakilinmu ya tuntubi shugaban gamayyar kungiyar ‘yan kasuwar Galadima da ke Kano, Alhaji Mustapha Shu’aibu, kasancewar kasuwar ce cibiya ta hada-hadar man girki, inda ya bayyana cewa su kansu wannan ta’azzarar tana damunsu, abin da ya jawo tsadar man, shi ne karancinsa da aka samu a kasar nan.

Alhaji Mustapha Shu’aibu ya ce, a baya ba a cika samun hakan ba, saboda man daga gida ake samar da shi, tsardarsa bai taba kaiwa na wannan karon ba, wanda su ma hakan ya damasu.

Daga nan ya yi nuni da cewa, dama ana samun man ya yi karanci, amma saboda ana shigo da shi daga waje, hakan ta na taimaka wa na gida yana wadata.

Ya ce, man na gyada ko na manja su ma ana noma abin da ake sarrafawa ya zama mai ne, akwai lokacin da ake nomawa, idan lokacin kakan noman ya yi ana samu da sauki, kuma idan ya ja da baya, wanda ake kawowa daga wajen sai ya taimaka ya cike gurbi abin da ake bukata. ya ce, amma a halin da ake ciki yanzu an rufe dukkan hanyoyin da man yake shigowa daga waje, ya yi karanci duk abin da ya yi karanci, dole a sami yawan mabukatansa da kuma tsada, don yanzu mai da ake samar wa ba ya iya wadatar da yawan al’umma, domin man ya yi karanci ba kuma na waje, shi ya sa yake tsada.

Alhaji Mustapha ya ce kudin da suke iya zuwa su sayo jarkar man guda 10 a misali, yanzu ya koma sai dai ka sayo kasa da haka. Sannan da in ka je sayowa a cikin ‘yan kwanaki kake samowa ka dawo, amma yanzu jarka biyar za ka je nema, amma sai akai mako Uku ba a samu ba. Kuma hakan ya sa jarinsu yanayin baya saboda tsadar da kayan ya yi ba kowane dan kasuwane ke da halin da zai iya sayowa ba.

Alhaji Mustapha Shu’aibu ya ce suna daukar mataki a matsayinsu na ‘yan kasuwa na shiga lungu da sako da ake iya samo man, su samo shi ta yin kundunbala da tafiya cikin hatsari,suna kuma baiwa wasu kudi su shiga daji, inda ake samo man bayan kwanaki su fito da kayan, idan kuma aka sami matsala, wadanda aka baiwa kudi suka shiga neman man suka ki fitowa, ba ba za ka iya shiga ka nemosu ba, ba ka ma san hanyar ba, haka suke shiga irin wannan kasada da dukiyarsu, lungu da sako su nemo kayan da kansu iya kokarin da suke ke nan.

Ya ce, ita kuma Gwamnati ta bangarenta, kokarin da ya kamata ta yi, shi ne ta rika sa kwararru suna kididdige yawan man girkin da jama’a ke amfana da shi a kasar nan bisa la’akari da yawan al’umma, ta san yawan mai na girki da zai ishi jama’a, kamar yadda ake wa man fetur na gane lita kaza ne ake bukata kullum a kowace jaha.Ya kamata duk abin da za a yi amfani da shi a girki a rika kididdigewa ana sanin yawan abin da jama’a ke da bukata.

Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya jaddada cewa man girki da ake yi a cikin kasa ba ya wadatar da bukatun ‘yan kasa a halin yanzu, dole sai ana samowa daga waje, yanzu a halin da ake ciki man na kasa ya janye, ga kuma sabo bai kai ga zuwa ba, wannan ya sa farashin man ya nunka, domin a baya ana saida jarkar man N8,000 ya koma N20,000, ya nunka kudin da za ka sayi jarka biyu, a baya 16,000 yanzu ya nunka har da kari. Hakan ya taimaka wajen kawo musu nakasu a harkar kasuwa jari ya yi baya.

Ya ce kamata ya yi mutane su rika gode musu a wannan yanayi da suke daukar kudinsu suje su nemo kayan, komai tsada cikin kasada, duba da halin da ake ciki na tsaro da suke zuwa su dauko kayan don a wadatar da su ga bukatar jama’a. Ya ce, aa a ce su ma sun duba yanayin su ma sun tsaya ba su nemo kayan ba, shi ma ba za a samu ba.

 

Exit mobile version