“Dalilin Da Ya Sa Na Fi Jin Dadin Lalata Da Yara Maza”

Wani matashi da a ke zargi mai suna Friday Okeke, wanda a ka cafke, bisa laifin yin lalata da kananan yara guda biyu maza a Jihar Legas, ya bayyana wa ‘yan sanda cewa, ya bi jin dadin yin lalata da kananan yara maza biye da mata. A cewar Okeke, mata su na saka cuta musammam mara sa tsafta.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Legas, Bala Elkana, shi ya tabbatar da wannan lamari a jiya. Ya bayyana cewa, “a ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2019 da misalin karfe 11.30 na safe,‘yan sanda daga yankin Ebute-Ero su ka samu korafin lamarin daga iyayen yaran guda biyu, a kan Okeke mai shekaru 35, wanda ya ke zaune a kan titin Kose cikin garin Legas Island.   

“An samu korafi daga iyayen yaran guda biyu cewa, wanda a ke zargi ja yaran guda biyu masu shekaru 12 da kuma 9, zuwa shagonsa da ke kan titin Kose, inda ya yi luwadi da su. “An garzaya da yaran zuwa babbar asibitin Jihar Legas, domin yin jinya, yayin da tawagar ‘yan sanda daga yankin Ebute Ero, wanda Sina Olunlade ta ke jagoranta su ka cafke wanda a ke zargin.”

Ya cigaba da cewa, wanda a ke zargin ya bayyana wa ‘yan sanda cewa, “yara mata su na dauke da cuta, shi ya sa ya fi jin dadin yin lalata da maza.”

Elkana ya ce, wanda a ke zargin ya bayyana cewa, “mutane su na cewa, ana yin luwadi ne domin yin tsafi, amma kuma ni na dauke shi a matsayin abin dariya da kuma jin dadi. Na yi ladamar yadda na ke saka yara maza cikin wannan mummunar dabi’a, amma dai haka rayuwa da juya min.” Ya kara da cewa, Okeke ya bayyana cewa, akwai karin yara maza da za a shigar da su cikin kungiyarsa.

Exit mobile version