Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Amaryar Kano da aka yi zargin an sace, ta fito ta bayyana gaskiyar lamari, Amina Gwani Danzarga ta ce ta kagi garkuwa da kanta ne saboda ta daina son angon nata,
sai dai ta dora alhakin hakan a kan sharrin shaidan inda ta nemi afuwar iyayenta.
Amina Gwani Danzarga, amaryar da ta boye awanni 48 kafin bikin aurenta, ta bayyana dalilin da ya sa ta dauki matakin.Tun da farko ‘yan uwanta sun shaida wa jaridar manema labarai cewa, an yi garkuwa da Amina ne a kan hanyarta ta dawowa daga unguwar Dorayi inda ta je ta ajiye katin jarrabawarta. Amma daga baya sai ‘yan sanda suka ba da sanarwar cewa amaryar ce da kanta ta shirya hakan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa manema labarai cewa, budurwar ta buya ne saboda ba ta son a gudanar da bikin auren.
Amina ta amsa aikata laifin, inda ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda bata son saurayin nata. “Ba na son saurayin, shi ya sa na dauki wannan hukuncin… Duk da cewa ni ce na nuna shi ga mahaifana,” in ji ta.
Amina ta kara da cewa, kasancewar tana ganin girman iyayenta sosai, ba za ta iya sanar da su cewa ta sauya tunaninta game da mai neman ta ba. Sai dai kuma, ta ce, a yanzu tana son mai shirin zama ango nata fiye da da, kuma a shirye ta ke ta zauna da shi cikin lumana har tsawon rayuwarta. Ta kuma nemi afuwar iyayenta da mijin da za ta aura, inda ta bayyana cewa sharrin shaidan ne ya kai ta ga aikata hakan.
Kawun Amina, Gwani Rayyanuna, ya nuna kaduwa game da juyawar lamarin. “Har yanzu ina cikin kaduwa da abin da yarinyar ta aikata. Ita ce ta gabatar mana da shi kuma na yi bincike game da saurayin, kuma a matsayinmu na iyaye, mun yi dukkan tsare-tsaren da suka dace game da bikin auren ”.
“Ba ta sanar da mu komai game da canjin ra’ayi da ta yi ba, sai yanzu da muka ji wani labarin na daban daga wurinta,” in ji shi.
Da aka tambaye shi kan yadda mataki na gaba zai kasance, Gwani Rayyanuna ya ce dangi za su hadu su yanke shawara.
Lokacin da aka tuntube shi, mai shirin zama angon nata, Umar Hassan, ya ki cewa komai kan batun, yana mai cewa har yanzu bai hadu da ita ba.
A baya mun ji cewa kwana biyar bayan an yi garkuwa da ita, har yanzu ba a san inda wata amarya da za a yi a Kano, Amina Gwani Danzarga take ba.
Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta a yammacin ranar Juma’a.