Daga Rabiu Ali Indabawa,
Bayan kisan gilla da aka yi wa dan uwanta, Rokeeb Musa, a ranar Asabar, 26 ga Disamba, 2020, matar auren mai shekara 24 da ke zaune a Ede, Jihar Osun, Mariam Musa, ta bayyana yadda ta kashe shi da kuma dalilin da ya sa ta kashe shi. Mariam, ta ce ta sanya wa Rokeeb guba ne saboda mijinta ya fi kulawa da mahaifiyar yaron.
Da yake magana yayin a gaban sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Osun, Wale Olokode, ya gabatar da ita a ranar Laraba, wacce ake zargin, ta ce yaron dan shekara uku ya bar mahaifiyarsa ya zo dakinta a wannan ranar da ta aikata hakan, ta kara da cewa ta sanya maganin kashe kwari a ciki bakin wanda ta kashe din, sanadin da ya jawo dalilin mutuwarsa. Mariam, wacce ke dauke da cikin wata biyar, ta ce mahaifiyar marigayiyar ta kasance ba ta girmama ta saboda ita ce matar da mijinta da ya fi so.
Ta ce, “Hadama da kishi sun sa na kashe dan matar mijina na biyu. Tana da da namiji kuma bana jin dadin yadda nake ganin mijinmu yake nuna mata kulawa sosai fiye da ni. “ A baya (Ni da Mijina) mun kasance muna cin abinci daga kwano daya, amma yanzu yana wulakanta ni saboda ba ni da da namiji. Don haka, na sanya wa yaron guba ne saboda na yi kishi sosai, amma ban nufin kashe shi ba.